Sashe 13
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
min wake-wake sun yi sun gaji sun hakura, dama hausawa Sunce wai watan wataran din guda daya ne in naka ya mutu sai kuma na wani ya kama. Mu'amala ta da Mansur ta yi amntukar sama min natsuwa da kwanciyar hankali a tare da ni, har na samu karfin da na ji zuciyata ta daina faduwa don na hango Mubarak ko na ji wata magana game da shi, a wannan lokacin sai naji a shirye nake in har Mansur ya yi maganar aurena in amince don kuwa na yarda na sakankance da cewar shi din miji ne da zai kula da 1yalinshi ya samar musu farin ciki da natsuwa da suke bukatar samu. Ina zaune a dakina hutawa nakeyi saboda dawowa ta kenan daga asibiti don yau ma na raka babana ganin likita saboda gaya min da ya yi cewar ya yi kwanaki uku cur bai samu yin bacci ba da daddare, hutawar da nake yi tare da kara tuna kalmomin da likita ya yi game da jikin nashi sai naji yaro yana magana a tsakar gida wai anak iran Mero a waje. A zuciyata na ce Mansur kenan shi da yace in shiga gida in huta sai an jima zai zo me kunma ya tuna ya sashi fasa hakan? Na mike na fito na wuce baba Lantana tana fadni, o'o shi wacan ya ja jiki wannan Kuma ya maye gurbi ya samu an bashi wuri ya zama shi kadai. Ban kalleta ba na yi wucewata na fita, ban ganshi a zaure ba kamar yanda ya saba shigowa ciki don haka na leka kofar gidayasan na zo ina lekawa sai kawai mukayi ido hudu da Mubarak, ya sha kwalliya cikin kananan kaya ya yi kyau sai dai ban ji faduwar gaba a tare da ni ba, dadi ya kamani na kara gamsuwa da kaina. Yana ganin naja baya ya biyoni cikin zauren, sunkuyar da kaina nayi don in kaucewa idanuwan da ya tsareni da su, zuwa nayi in rokeki ki yi min wata alfarma Maryam. Na dan yi kokari na daga ido kadan na kalleshi saboda maganar tashi da yanayin da yayi maganara ciki, alfarmar me ni kuma zanyi maka? Na rokeki na kuma sake rokonki ki yi min wannan alfarmar ki fita hanyar Mansur bana so ina ganinki tare da shi. Cikin natsuwa hankalina kuma a kwance na buda bakina na ce mishi, gaskiya ba zan iya ba. Maganar tawa tayi matukar bashi mamaki saboda abinda na gani a tare da shi, cikin wani irin yanayi ya tambayeni, ba za ki iya ba? Shiu nayi ban bashi amnsa ba, ban kuma sake daga idona na kalleshi ba, saboda har yanzu ina jin nauyinshi a zuciyata. Me na yi miki Mero? Me nayi miki haka da kike nemaki sani bakin ciki? Ai ban cuceki ba, ban zalunceki ba, ban yi miki wani laifi ba, in kumakina gani nayi to gaya min shi in abki hakuri Mero, ai in rai ya baci hankali baya bata a kowane hali muke ciki ko muka samu kanmu, bai kamata ki rufe ido ki kasa ganin gaskiya tsakanina da ke ba. Juyawa nayi da nufin shiga gida in barshi a zauren, ban san yanda akayi ba sai kawai na yi kicibis da baba Lantana a kusa da bakin zauren watakit da shigowa zatayi taga abinda muke yi, tana ganin Mubarak ta shiga salati tana tafa hannu tare da fadin, yau ga abin da mamaki yau ga abin al'ajabi, yau ga wata musiba da ta addabeta ta addabi sauran jama'a, ashe ba iyayenka sun yi maka aure na rufin asiri don ka fita hanyar wannan yarinyar ku daina lalacewar da kuke yi ba, haba wannan wane irin al'amari ne shi? Aure baifi wata shida ba masifar ka ta sa kullum yarinya tana kan hanyar yin yaji ta tafi a dawo da ita, ta tafi a dawo da ita, to kar ka ji da wai zan wanke kafata inje har gidan iyayenka in kara yin kashedi tunda na san su ma ba son mu'amalarka da ita suke yi ba tunda ina da labarin komai sai da ka yarda da sharadir da uka sanya maka na fita hanyarta sannan ne suka bar ka ka dawo suka kuma yi maka aure na rufin asiri wanda a yanzu kake wulakantawa ko da yake ba haka kawai suka barka ba 'yarta ai babu abinda ba zata iya ba. Wuceta nayi na shiga dakina na yi kwanciyata a kan gadona sai na ganta itama ta dawo na tabbatar tafiya yayi ya barta. Wunin ranar nan bakin baba Lantana bai huta ba fadi suke haka kawai basu shirya yarinya ba sun kunsota sun kawo sun ajiye mishi ba dole su da ita su yi ta ganin abinda basa so ba, tunda ya riga ya saba da tsome-tsome ai zama da shi kuma sai an shirya, Maganar tayi matukar watsuwa ta yanda har Mansur ma yazo ya sameni hankalinshi a tashe, ranshi a bace, me ya saura ne tsakaninki da shi kuma? Na rasa yanda zan yi na rasa abinda zan gaya mishi saboda bacin ran da na gani a tare da shi, don haka na kama yi mishi kuka, kuka kuwa mai yawa irin wanda na kwana biyu ban yi ba. To menene kuma na kukan hakan? Ya soma yin maganar a yanayi na sanyin jiki alamar bacin ran da ya zo da shi din ya kau, to ni me nace miki da kike wannan kukan? Kinga share hawayen nan ki ji abinda zan gaya miki, to ai kuma na gane so kawai kikeyi raina ya baci shi yas akike ta kukan, in ba haka ko ma menene nace ki yi hakuri ki yi hakuri ina ce shi kenan zance ya kare. Kinga tunda abin nan ya zama haka ana nema a rinka kai kawon maganganu a tsakani to ina ganin gara kawai a kawo karshen al'amarin gaba daya in kina dakina da wani wanda ya isa ya zo yana Rananan maganganu ne a tsakani? Don hakan ni in kin yarda kawai a shirye nakwe in je in samu babana ya dawo ya sake yin amgana da baban nan gidan a daidaita a sanya lokacin auren mu kome kika gani. Lokaci mai tsawo na dauka ban ce mishi komai ba har ta kaima ya sake tambayata, ba ki ce komai ba Mero ko kuna da wani tunani ne? Na sunkuyar da kaina kasa kafin nace mishi, kai ne dai nake ganin kamar ya kamata ka kara tunani akan maganar tunda ka sani sarai an fadi maganganu da yawa a kaina har yanzu ma ba a daina ba tunda ga ma wanda aka je har gidanku aka fada kwanan nan in... Ban karasa zancen nawa ba ya yi maza ya katseni, yanzu ina amfanin wannan maganar da kikeyi in dai ba so kike sai d le kin sa raina ya baci ba? Shiru nayi bance mishi komai ba, kar ki sake kawo min irin wannan maganar bana so. A hankali cikin natsuwa na ce mishi, to kayi hakuri. Dadi ya kamashi saboda hakurin da na bashi, ya dan gyara tsayuwa kafin ya ci gaba da magana, shi baba yana dawowa zanje in same shi da maganar. Na ce Ubangiji ya dawo da shi laf ya, yayi maza ya ce amin Maryam. Kafin babansu Mansur ya dawo wata irin lafiyaiyar soyaiya mu ka shiga, ka'ida ne kullum sai ya zo ko da rana ko da daddare, wataran ya zo ya sake dawowa, in na ce mishi baka riga ka zo ka dazu ya ce ai wata magana ya tuna da ya manta dazu da ya zo din bai gaya mini ta ba. Rannan muna hira ni da shi tattaunawa muke yi irin ta fahimtarjuna, ra'ayinshi yake fada kan irin tsarin da yake ganin zan gudanar a gidanshi wanda hakan yake matukar taimakawa ma'aurata bayan an yi aure. Kin fa san 'yan uwane da ni masu yawa ina fata zaki yi hakurin zamada su. Na yi murmushi na ce, insha Allahu. Can cikin zuciyata kuwa tunani nake yi ni da nake rayuwa cikin kewar 'yan uwan miji zasu isheni har in kasa yin hakuri da su? To kuma ba zan barki yin aiki ba don kar ki ji ina cewa za ki koma makaranta don ki samu takardarki ki yi tunanin ko har da aiki cikin lissafin nawa. Na yi murmusih na ce nima ban damu da yin aiki ba amma cikin zuciyata ina sha'awar yin sana'a, da sauri ya ce wonderful tamkar ace kin shiga zuciyatakin gani ai ni mai sha'awar taimakon mace yin sana'a ne, Maryamu ina son ganin matata ta tsaya da kafafunta tana dogaro da kanta saboda karki samu damuwa akan wannan wacce irins ana'a kike son yi? Na ce a'a ban sani ba tukunna ni dai kawai cikin zuciyata ina son yi amma ban zabi wacce zanyi bal to ai kin gani ma shi kenan sai in duba in ga abinda zaifi dacewa da ke ina ganin ma kawai dinki za ki yi domin shi ya fi bani sha'awa ko kuwa? Na ce mishi to. Tun ranar da Mubarak ya zo gidanmu ya rokeni alfarmar fita hanyar Mansur na ce mishi ba zan iya ba ya dauki mataki in ya ganni bei kulani ko yana fara'a ya hangoni sai ya yi maza ya tsuke fuska, a zuciyata na ce nima gara irin haka, abu guda daya dai da na kasa fahimta ko dalilin yin shi shi ne wunin da Isiyaku yake yi kan dakalin kusa da gidanmu a zaune bana dai ko amsa gaisuwarshi balle-wani abu ya hadamu tunda kowa ya san dan gidan Mubarak don haka na kara kiyaye mu'amala da shi don Mansur ya kara samun kwanciyar hankali. Ni da Mansur muka zama bamu da wani fata ko buri sai na jiran dawowar babanshi daga tafiyar da ya yi. Mansur dak ullum yake ce min ai kawai kwana daya zan yi mishi in ya dawo da rana in barshi ya kwana ya wayi gari kafin inje mishi da maganar. Sai gashi baban Mansur ya dawo har ya kwana bakwai babu wani motsi ko yunkuri daga gidan nasu shi da kanshi ma sai nake ganin shi tamkar a sanyaye yake ban dai ce mishi komai ba tunda dama can ba