Sashe 3
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
ta kan zo ne da tabarmarta ta shimfida a hanyar da ta san itace tas higowar mutane tana ganin an zo sai ta tari masu zuwan tayi musu jagora zuwa inda babana ke kwance in suka gaisheshi suka ba da abin da zasu bayar tayi amza ia karbe ta saka a cikin yar fos dinta ta koma kan tabarmarta ta zauna ba kuma zata sake tasowa ba sai wasu bakin sun zo daga ni har yaya Dija babu wanda ya daga ido ya kalleta balle ya ce mata kanzil. Kwana tara baba ya yi kafin aka sallameshi a hakan ma matsawar shi ce ta sa aka yi ta saboda yawan maganar da yake yi bai son zaman asibiti bai taba zuwa asibiti don kanshi ba sai dai don ya zo duba mara lafiya, yaya Ibrahim ne ya yi duk wata dawainiya har da biyan kudin sallamar muka dawo gida. Likita ya sallame mu ne bisa dokoki na a kiyaye. bacin ranshi a kula da abincinshi banda gishiri banda barkono banda farin magaji banda kanwa banda yawan cin man gyada. Tun likita yana bayanin baba Lantana ta somna fadin, hu un wannan banda bandan ai ya yi yawa. Yaya Dija ta kalleni cikin natsuwa bayan munje gidamnu da baba tace min debi kayan da zaki diba mu tafi nace mata a'a je ki kawai ni zan zauna a gida, da sauri ta sake k llona za ki zauna fa kika ce? Nace e, amma ai kuma kin san gidan ba zai zaunu miki ba a yanzu a yanda take fusacen nan ina nan ma kina jin irin maganganun da take furtawa balle kuma ace na tafi na barki ke kadai. A hankali na daga ido na kalleta kafin na tambayeta, to in muka tafi dukanmu muka bar baba a yanda yake din nan wa zai yi mana jinyarshi? Wa zai bashi magani? Wa zai kula da abincinshi balle ya tsaya yaga an tsare dokokin da aka sa mishi? Tace to kuma haka ne ta bude jakarta ta fito da kudi ta bani tare da fadin, to rike wannan a hannunki kafin inje gida in ga abinda zan iya hadawa nace mata to. Na koma zaman gida tare da baba Lantana da ya'yanta biyu ga kuma babana a kwance yana jinya tunda ko fita runfarshi baya iyawa balea yi maganar kasuwarsu, dan garama dai Sallau don shi kam yayi mana mutunci kwanakin asibitin baba duka tare da shi muke kwana. Duk lokacin da na zo shiga dakin baba Lantana don yiwa babana wani abu ko bashi magani sai tace wai bata yarda ba ina shiga ne ina ganar mata sirrinta shi ba zai sha da kanshi ba sai an bashi kamar wani dan yaro? An wani tasashi a gaba ana shagwabashi ita bata son gulma da iya yi. Babana kuwa shan maganin yake yi a kan dole sai na yi ta rarrashi ina bashi hakuri kafin ya yarda ya sha. Ganin da nayi takurar ta kai inda ta kai ya sa na shiga dakin da Sallau ke ciki yana kwance kan katifarshi na ce mishi, Sallau kawar da katifarka ka .koma can gefe zan yiwa baba shinfida anan don a samu saukin mu'anala, cikin sauri ya ce min to, nan da nan kuma ya mike ya soma yin abinda nace mishin har ya tayani na shiga dakina na dauko katifar da nake kwanciya a kai nad awo mishi da ita nan na shinfida mishi ita naje na samu babana na ce mishi tashi baba mu koma dakin Sallau don zai fi mana saukin zama ya ce min to. Na dawo da baya ina jiran fitowar tashi Sallau ya leko daga cikin dakin yana tambaya ta Mero wannan ai katifar gadoski ce nace mishi eh, ya ce to ki maida ita mana kawai sai ya yi amfani da wannan ni zan rinka yin shimfidar tabarma ina kwanciya, har zance mishi a'a ya barta kawai sai baba Lantana ta taso da saurinta to ai ba tasu bace wannan din da kake neman gwaninta a kanta tawa ce da kudina na sayeta don haka ban yarda ba, ta sake kallonshi cikin wani irin yanayi da takaici yafi komai baiyana a idonta kana tsoronta ne saboda wancan dan iskan ko? Dama ka wartsake kayi hidimarka shima yanzu ta kanshi yake yi sakara matsoraci bani katifata ka rinkak wanciyar tabarmar da ka zabarwa kanka. Na kalleta cikin natsuwa na ce mata, to ki fito min da wacce take kan gadonki ai wannan tamu ce tunda ta gadon innarmu ce. Ta zabura kamar zata ki famin mari saboda hakan dana gaya mata ban san yanda akayi ba ta fasa ta kuma bar katifar ta tayi nima naja tawa na mayar kan gadona. Dawowar da babana yayi dakin sallau sai ya bani damar dana rinka kula da shi dama duk wani ala' marinshi ko wane lokaci ina tare da shi komai naga ya dace in yi mishi bana jiran sai ya ce a yi mishi, wanka, wanki, komai a kan lokaci. Duk wannan abinda yake faruwa baba Lantana bata cas bata as kan abinda ya shafi rashin lafiyar mijinta taja ta tsaya kan wai raina mata mukayi ya sa na zo na kasa na tsare a kanshi don haka itama ta cire hannunta kan lamarin shi tunda shi dama abinda ya'yanshi suke so yake bi baya kuma gudun abin kunya na aikata babban laifi bai ce min komai ba ya tasani a gaba yana kallona masu ya'ya mza ma sun hukunta 'ya'yansu amma ni ya yi kamar bai san abinda na yi ba. Yanda dama can babu mai ce ma ta komai in tana maganganunta haka yanzu ma a wannan lokacin ko wani wadataccen girki batayi sai ta ce wai ba a fita an kawo mata ba me zata girka? Don haka kullum gidan a bushe yake babu abinci ni dai ina tsare da cikin babana ba na yarda ya ji yunwa ba na ma zaton ya san baba Lantana bata girki in dai ba ya lura ya gane abinda kalamanta 11a tsakar gida suke nufi ban e. Wurin Isiyaku da ya zo gaida babana da jiki na samu labarin wai ashe Alhaji Muhammadu baban Mubarak korarshi yayi daga gidan saboda samuna da akayi a dakinshi da kuma cin mutuncin da baba Lantana ta je musu da shi cikin gidan tun yana tsare a wurin 'yan sandan wai ya aike mishi cewar in ya fito ya nufi inda ya nufa amma ba gidanshi ba, ya kuma turo har abokan baban sun zo sun b ashi hakuri yaki ya hakura ya tsaya kan bai son sake ganin shi a yanzu. Gabana ya yi mummunan faduwa saboda jin irin hukuncin da baban Mubarak ya zartar a kanshi bayan kuma na san matsayin da yake da shi a wurin iyayena nashi na yi matukar kaduwa, tausayinshi kuma ya kamani har na rinka ganin tamkar ni naja mshi tunda ai ni naje wurinshi ba shi ya kirani ba, cikin zuciyata na ce to abinda baba Lantana ta je kenan tana fadin masu ya'ya maza ma sun hukuntasu amma nawa yana kallona saboda abin kunyar da na aikata bai dameshi ba sai wani lallangabewa yakeyi ina tarairayarshi wai shi nan ga mai 'ya. A wannan lokacin ba zan iya zama in kwatanta halin da nake ciki ba na kunci, takura da kuma bakin ciki a halin dan a samu kaina a ciki, na gane ashe ba auren Alhaji Nalami kadai bane karshen bakin cikin rayuwa ko da yake dai ni a wurina ina ganin tamkar shi ne ya yi min sanadi na shiga duk wani hali da nake ciki, ban kara sanin irin cikin wani hali na shiga wata gagarumar fitina ba sai da na ji Asabe tana rera wata irin waka da na sha jinta a bakin yara ban atba kulawa na gane abinda suke fadi ba sai ko yau da na ji ta a wurin Asaben sh ne na gane ashe wai ni aka yiwa wakar. A wancan lokacin da ko yawan kula, samari budurwa take yi yan mata yan uwanta suke rera mata wakar, mace mai wasa da maza karya nayi mamakin kaina matuka na kuma ga sakarcina da tun asali ban gane da ni ake yi ba wai sai da na ji wakar a bakin Asabe, masu gatama masu ya'ya samari basu tsallake wannan wulakancin ba balleni da bani da kowa in banda babana sannan tun can asali damab a wani farin jini ne da ni ba a tsakanin yan mata da samarin unguwar iyaka dai tsoron Mubarak ya tserar da ni daga duk wani wulakanci ko iya shege da za a yi nufin yi min to yanzu kuwa babu shi kowa kuma ya san ta kanshi yake yi don kuwa wannan hukunci da babanshi zai yi ba sannan a yanzu bama maganar wasa da maza bace mas ala ta an kamo ni ne a dakin saurayi na kai mishi kaina baba Lantana kuma ta sake rattaba bayani a gaban kowa a cikin daren da babu siri a cikinshi cewar ba ranar na fara 'zuwajne kwana a wurinshi ba. Na yi kuka rannan irin wanda na tababtar ban atba yi ba a rayuwata nayi bakin ciki.na rasa inda zan tsoma raina in ji dadi na rinka jin tamkar ina ma dai imsda jlkon bude kasa in 6uya a cikinta saboda tsaranin kunya. Duk inda tozarta ta kai duk inda wulakanci ya kai duk inda muzantawa ta kai kalmomin da suke cikin wakar sun kai harma sun wuce gashi saboda wulakanci da raini sai aka yi anfani da sunana ta yanda kowa zai gane da ni ake yi amma shi Mubarak babu nashi sunan a cikinta, na samu kaina cikin wani yanayi da na rinka ganin tamkar babu wanda ya taba shiga cikin wannan yanayin sai ni kadai. Da kyar na ke iya fita waje sai in dolen ta kama dole ina nufin in zan saiwa babana wani abin in ta kama hakanma sai na yi ta leke naga mutane sun dan dauke sannan ne zan ruga da gudu inje shagon kusa da gidanmu in sayo in dawo saboda yara suna ganina suke fara rera wakar wasu suna anshi cikin tafi sannu a hankalima dana lura sai na gane ba waka