← Book details Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 25

Sashe 16

Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

da nayi cewar ni da Asabe bama ko ga maciji. Waiyo-waiyo dama dai kawai in mutum in huta da wannan wahalar. Zumbur nayi na tashi na zauna saboda jin maganar ta ta, me ya satieki haka Asabe? A tsorace na yi mata tambayar. Bata tanka min ba, waiyo-waiyo, abinda kawai take te faman fadi kenan. Na sauko gareta ina kokarin riketa don in tsaida murkususun da take yi a kasa cikin yanayi na tausayawa ina isowa gar ta na gane lamarin ba karami bane, ya kuma wuce duk yanda ake zato don haka nace mata bari in kira miki baba Lantana don tazo ta ga halin da kike ciki in yaaso a kaiki asibiti. Tayi maza ta ce min u'u barta kawai kar ki kira min ita ke dai kawai ki taikameni ki kaini cikin kankon bola ki barni a wurin in ma mutuwar zanyi in mutu a can. Tausayin Asabe ya yi matukar kamani, haba Asabe daina fadin irin wadannan kalaman kankon bola a cikin tsohon daren nan ko mahaukaci ai ba zai dunfari wurin ba, na shiga share mata gumi da majina da hawayen dake ta dalala. Ki yafemin abubuwan da na yi tayi miki Mero satar kayanki da ua rinka yi ina sayarwa da kudinki da sharrin da na... Kai haba Asabe bar irin wadannan maganganu ai zanman tare ne. Ana cikin haka naga Asabe tayi rigingine ta bankade komai babu sauran kunya a tare da ita, tsoro ya sake kamani jikina ya dauki rawa cikin muryar kuka nace mata Asabe, don naga alamar bata cikin haiyacinta, kan in kai kkarshen bayani na hango wani abu yana shirinf itowa da gudu na nufi kofa na 6alleta cikin rawar jiki da karkarwa na buga kofar da take ta baba Lantana da babana, tana jin bugun kofar da nayi sai na ji ta soma cewa, yauwa ai ga ranar da nake jiran zuwan nata nan ta zo ranar da asiri zai tonu, ranar da zaka gane shirunda kake kame bakinka kana yi a kan komai ba dabara bace, ai tun dazu nake gaya makaa wannan zirga-zirgar da akeyi ana ziryar bayan gida da kyar ne in ba nakuda ake yi ba, ni na dade ina fatan ganin an haifar maka shege a gidan nan, ba dai kwadayin abin duniya ya sa ka zuba mata ido tana yin abinda taga dama ba? Yaro ya ki aurenta ya kai gida amma a waje ya maida ita matarshi? To muje ka karbi haihuwar da hannunka don kar ka ce sharri aka yi mata ba a jikinta ya fito ba don haka nuje a yi kornai a kan idonka, kaga ta inda yalke fita muje mu je. Ina jin hakan nasan fitowar zasu yi tare don haka na tsaya a inda ana bude kofar babana zai ganni. Abin kunya ina jin gadonshi kukeyi malam tunda ba haka ai nayi ta gudun makashi baka yarda da shawarat bane yasa baka koreshi ba sai da ya sameka saboda bai damcka ba, muje nace muje kana ji ana ta gurnanin nakuda ka ki kayi kuzari sai wani jan kafa kake yi kamar kazar da kwai ya fashe mata a ciki. A na bude kofar mukayi ido hudu da babana, muje m ana kayi wani kerere ka tsaya min a hanya kaki ka bani wuri in fita, abinda haba Lantana ke fadi kenan daga bayanshi saboda kasa motsin da ya yi a dalilin ganin da ya yi min a bisa da na tabbatar kuma shi ne da ni ya gani a cikin wani hali na abidna take gaya mishi watakila da ya yi faduwar da bai sake tashi ba don a haka ma tsinkewar da yayi ta kai duk inda ta kai. Kurdawa tayi ta bayanshi ta fito saboda ta kasa hakurin ya matsa ya bata wuri, tana ganina a tsaye tayi maza ta ja ta tsaya ta yi turus cikin tsananin kaduwa nan take tsoro ya baiyana a idonta, a'a to wake zirga-zirgar da gurnanin nakudar da ke fitowa. Ban ce mata kala ba balle kuma babana da ya zama tamkar mutum mutumi, to wane irin abu ne kuma haka mai nakuda tana tsaye kememe, da gani dai nasan kece kike wannan zirga-zirgar da gurnanin nakudar inma... Kan ta karasa maganganun nata masu kama da sanbatu sai kawai mika jiyo kukan jariri daga cikin dakin namu. Ina kallon yanda jiri ya debi baba Lantana ya yi wuji-wuji da ita kafin ya fyadata da kasa, tayi faduwar yan bori vato da mazaunanta, tsoro ya kamani saboda ganin irin faduwar da tayin, sai kawai na ga ta zabura da iyakacin karfinta ta yanka da gudu ta nufi cikin dakin namu. Wato da ma shari ne abin? Watp ni za a kawowa iya shege? Dama da hadin baki ne tsak ninki da m atsiyacin likitan da yace min kaba ce da ke? Ni za ki kawowa tsiya? Ni za ki jawa magana? To ai kuwa yanzu za ki gane wautar ki don kuwa kasheki zanyi murus har lahira. Tana fadin hakan mulka jiwo-ibun Asabe da sauri Sallau ya fito ya fada cikin dakin; ba zaiki kasheta anan ba baba ba zaki yi mana kisan kai a gida ki jawo mana wata fitina ba, tunda dai har kin kaita gun lik ya ce miki kaba ce ai kin san da komai, lokacin baya ta kawo miki gasassun kaji kina ci kowa ai yana girban sakamakon abinda yake aikatawa ne. Da karfi Sallau ya jawo baba Lantana ya fito da ita waje, tana-kicin kwancewa daga gareshi tana kurma ihu da iyakacin karfinta, ka sakeni kawai in hadata ita da shegen dan natain murkushesu kowa ya huta. Wannan dai duk kina kokarin jawowa kanki wani abin magana ne kawai in har kika bari makwabta suka jiyoki suka gane abinda kike ciki da ma ki yi maza kin san abinda kike ciki da ita da dan nata kafin gari ya waye magana ta watsu. Daga cikin gidan baba Baidu muka jiwo muryar baba Sumaye tana cewa, kar makwabta su ji na nawa tunda ni naji? Ai ko ladan cikins hegen da tayi ta rokarwa ya'yan jama'a sai na baza wannan labarin, barde a gonar wani sunkuru ya rufe naka, ddonki kam ya' yan jama'a ammakin kasa sawa naki balle ki gano abinda suke ciki, wai likita ya ce miki kaba ke gareta? Ta kwashe da dariya kafin ta ce, saboda ya gane ke din mahaukaciyar uwa ce shi ya sa ya yi miki hakan, kar kumaki ji da wai ba nan unguwar ba ko a wani wuri na ji 1abarin an tsinci mataccen jinjiri zan kai rahotonki don nasan halinki kin kuma furta zaki kashe uwa da da kat su jawo miki abin kunya, sai kace in da ana kashewa da ke kin kawo yanzu, ai yanda kika sa su Jkuka da bakin oiki lokacin da kikayi naki haka kema za sa ki ki yi abinda,kukayi ne ai za a yi muku, shi kuma malam Habu Ubangiji ya yaye mishi abinda ya sameshi, yauwa duk inda naji an tsinci mataccen jinjiri nasan kece zan fada na kangon bola ma da aka gani kwanaki wa ya sani ko ke kika kaishi? Fitinannun mutane masu jawa mutane annoba iri-iri. Baba Sumaye tana rufe baki baba Lantana ta yi zumbur ta maike da sauri ta sake shigewa cikin dakin namu inda Asabe da dan jaririnta suke tamkar dai ace dama kasake tayi tana sauraron bayanin nata ban san yanda akayi ba sai ganinta muka yi ta fito tana rungume da dan jariri Asabe tana biye da ita cikin katon lullubi sun sa kai sun fita sun bar gidan, ganin sun bar gidan ya sa ni nufin shiga dakin namu wai in kwanta. Abinda na gani a tsakar dakin ya sani kwallara ihun da na dawo da baya cikin sauri Sallau ya fito ya leka cikin dakin ya tayani ganina binda na gani, ya koma ya dauko leda ya sanya shi a ciki ya kuma. sa omo da izal da tsintsiyar zabori ya wanke dakin tas zuwa tsakar gida dama bayan gidan baki daya maimakon karni da kazantar jini ya koma tsabta da kanshin kayaiyakin da ya yi amfani da su. Na shiga dakin nayi salla na hau gado na kwanta cikin jimamin abinda ya faru, akan idona Asabe ta haihu ta haifi da babu aure ba shiri nake yi da ita da uwarta ba amma na tausaya mata tare da dan nata, ina cikin hakan na jiyo muryar baba Lantana tana cewa ba dai dani kuke yi ba ai za mu sa kafar wando daya ni da ku, munafukan banza munafukan wofi matsiyatan mutanen da basu san mutunci ba duk zaluncin ubanku. Na yi kasake ina sauraron zage-zagen nata cikin zuciyata na ce, oh oh wannan mata da jarumtaka take ko ita da su wa take yi oho. Ina jinta ta shigadakin da Sallau yake bamuji komai ba illa iyaka dai na jiumuryarshi yana ce mata to nan take kuma ya yi waje, nima na fito don in nemawa babana abin karyawa da kuma maganinshi, lokacin ne na gane daga tafiyarshi masallaci don sallar asuba bai sake dawowa gidan ba. Ina daki a kwance ina sauraron shigowar babana don ba dabi'arshi bacewucewa kasuwa daga masallaci na ji muryar Salau alamar ya dawo daga aiken da ta yi mishi na ji shi a fusace yana ce mata, kin ganta ko mnama kin ganta ko baba kinga halin Asaben ko? A gabanki bakinta ta ce min Agogo ne Gabana ya yi mummunan faduwa cikir raina na ce Agogo kuma? Ban kai karshen maganar zucin nawa ba naji Sallau shima yana karasa nashi bayanin to an je anzo da Agogo ya zo ya zare m ata ido yana tambayarta' shi kadai ne su sauran me yasa bata amabci sunansu ha sai shi? Mainakon taja ta tsaya a kan shi kadai ne sai kawai ta tsorata ta ce wai Alhaji Nalami ne. Kiis ya rage in rikito kasa daga kan dan gadon nawa saboda firgitar da nayi, nayi maza nasa hannu biyu na dafe kirjina saboda harbawar da ya kama yi, nayi maza na sake tambayar kaina, Ahlaji Nalami kuma? Wannan abin mamaki da ban tsorod a yawa suke, Nalami da Agogo su Asabe take tuihuma da yi mata ciki,
Chapter 16 · 0% Book details