Sashe 25
Halin Rayuwa Part 3 Complete Hausa Novel · about 2 min read
kaucewa zanyi in baku wuri banda musu banda jayaiya banda gardama, dif sai kawai naga wutar fitila ta mutu duhu mai tsanani ya baiyana, na yi matukar tsorata irin tsoratar da ba zai yiwu in kwatanta ta ba. A firgice kwarai na shiga furta kalmar Innalillahi wa inna ilaihi raji'un, shiiiii sautin da ke ta karuwa a cikin dakin kenan sai kuma tsananin sanyin da ya fara lcadani, na shiga cikin wani irin yanayi mai tsamanin firgitarwa baranma dai da na ji wani abu ya sauka a jikina wanda ya yi min kama da hannun mutam, rauhanin ma yana da hannu ne irin na mutane? Tambayar da ta zo cikin zuciyata kenan, ban daina furta kalmomin da nake firtawan ba sai ma karawa nayi zuwa can naji abin nan da ya tabani mai kamar hannu ya cafko kullin da na yiwa zanina a ta bayana yana kokarin kwanceshi, kici-kici da kokawa mai tsanani ya kaure tsakanina da rauhani saboda ganin da nayi rauhani yana Rokarin gradamin karfi, ya yi min illar da bazan laminta ba, ganin da nayi kamar rauhanin zai yi galaba kaina yasa na sa hannu da kafa na kuma bude baki na kurma ihu da iyakacin karfina ina bana so bana so aikin a kyaleni, ban sani ba ko maganar da yaji nayin ne ya sashi bude bakinshi shima ya yi min magana da irin nashi zancen. Gyaaraaahhhh ki budeec kafahfuh mu sah miki albarrkah. Mu sake bin Maryamu cikin littafi na hudu don mu ji karshen labarin na ta tare suka fito. Fatan alheri gareku dukkanku na gode Ubangiji ya saka muku da alheri ya kuma kara zumunci a tsakaninmu. SummaryInformation DocumentSummaryInformation WpsCustomData TECNO LD7 WPS Office Normal Times New Roman Times New Roman Calibri Calibri !%),.:;>?]} $([{ e7fabbc4ebe948d29cdc4cfc65cedd55