Sashe 9
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read
Kwarai da gaske na yi kokarin danne abinda nake ji a zuciyata game da al'amuran dake faruwa. Na zauna muka gaisa a tsanake fuskarta babu wannan murmushi da yake sake k'awata haibarta ta yi fiyau da ita dama abinka da mara jiki tabbacin da gaske ne bata da lafiya domin ga yanayin lalura da rashin kwarjin jiki nan a tattare da ita.
Ta ce." Amina na shigo nan ne saboda ke domin mu tattauna abubuwan dake faruwa da yaranmu, Allah Ya ga zuciyata ban shigo cikin rayuwarku da wata niyya ta cutarwa ba. Yana da kyau a matsayinki na uwa mai hankali ki yi nazari mai kyau Amina idan hankali ya 'bata fa nutsuwa da dattako ake sanyawa domin nemansa bai kamata ace kin d'auki munanan shawarwarin da ba za su zama silar gyar........Hauwa ta katse ta cikin fusata." Ai dama ban ce ki shigo domin ni ba, ko kuma kin ji na ce miki kin shigo ne da mummunar niyya. Hajajju ki dube ni da kyau ki ga ni, a waye nake babu wata kinaya da za ki yi mana, kafin ki san Amina da yaranta ni na zauna da ita. Idan har mijinki ya gaya miki cewa da hannuna wurin matakin da Kamalu ya d'auka bai yi miki k'arya ba, ga ni a zaune ai ina jiran hukunci tunda ku kun iya take gaskiya da gangan."
Cikin rashin sukuni na ce." Hauwa menene don Allah, duk cikinmu nan babu yaro karami tunda har ta shigo domin mu tattauna magana dan samun daidaito bai kamata wasu maganganu mara dad'i su biyo baya ba."
"Kina jin irin jirwayen da take yi mini ai, ai mu 'yan iska ne marasa 'yanci tunda mijinta haka ya nuna mata ba mu da sirri komai muka yi a tambade ita nata sirri koyaushe cikin danda'be shi yake baya so kowa ya ji. Bazan jure d'aukar cin kashi daga 'bangaranta ba wallahi."
A nutse ta ce." Ba halina ba ne raina mutum Hauwa, kuma kamar yadda ki ke hasashe hakane maigidan ya gaya mini komai ke ce ki ke ko'karin ganin lallai sai an yi 'batacciya domin kuwa abinda muke ta bunnewa dalilin gudun rikici mai muni ke ki ka gayawa mahafiyar yaron nan, kuma ki ka cire nauyi da kunya ki ka dubi tsabar idon yaron nan Kamalu ki ka gaya masa to kin fad'a kin ji dadi Kuma in sha Allahu abinda ki ke fata ba zai faru ba da izinin Allah."
Hauwa ta mike tsaye tana huci ta ce." Kin yarda yaronki mahassadi ne, kuma sharri ya yi wa Kamalu ko ba ki yarda ba, ai ita karya fure take bata 'ya'ya wallahi ni dai Hauwa Maryam ba ki isa ki siye ni da kudi da abin duniya ba. Wannan gingimeman sharri da d'anki ya alak'anta marayan Allah saboda rashin adalci da son zuciyarku sai ku ja baki ku yi shiru babu wani mataki da ku ka d'auka. Kenan wannan ya nuna kun sake bawa yaron lasisin ci gaba da aikata abinda yake yi dalili kun nuna masa akan daidai yake, na fad'a din idan ta yi miki zafi ki kaini 'kara ko kisa tsinken tsire ki tsire ni!"
Tsaye na tashi da sauri na tare ta tare da mayar da ita kan kujera sai huci take yi tabbacin a fusace take kuma a shirye take da duk abinda zai faru.
Hayaniya ta fito da Baba Tabawa daga kicin tana fad'in." Mai yake faruwa ne don Allah ku yi aiki da hankali da girman shekarunku kada hayaniyarku ta d'auki hankalin yaranku k'ananu har su fahimci abinda yake faruwa, kun san dai yaro da ri'ke abu a zuciyarsa.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 105
Cikin numfasawa Hauwa ta koma ta zauna tana huci! ita kuma Momi ta yi 'kasa da kanta k'walla cike a kwarmin idonta. Alamu sun nuna cewa ba ta iya fad'a na cacar baki ba koda fad'ansu ya yi tsayi da Hauwa ita za ta kaita kasa.
Har cikin zuciyata ban ji dad'in abinda ta yi mata ba duk da cewa duka su biyun ban san menene a cikin zuciyoyinsu ba don haka ba daidai ba ne abinda ta yi tsinka na k'asa da kai ma tozarci ne ballantana wanda yake sama da kai ashekaru. Ni da ita duka haihuwa ce ta janyo mana domin kuwa da yara ba su had'a ba ina ganin babu wani dalili da zai sanya na yi sa'insa da ita akan namijin da ba shi da wani tabbas. Tun farko itama Hauwan da ta d'auki shawarata abinda yake yi akan Momin ba zai dameta ba tunda ta san tafi amfanarshi fiye da ita ko a wurin tarayya ta aure ne. Kuma ita ce uwar mai sunan mahaifinsa Ibrahim Khalil, uwa uba kuma 'yar uwarsa ta jini. Hauwa ba ta fi ni kishi ba wallahi kawai na fita ha'kuri da juriya ne dalilin gwagwarmayar da na yi a rayuwa ita ba ta yi irinta ba.
BabaTabawa ta koma kicin jikinta duk a sanyaye bayan cikin hikima irin ta manya ta yi mana nasiha aka ci sa'a kuma Hauwa bata k'alubalanceta ba.
Falon ya yi shiru bayan gushewar baba Tabawa daga wurin babu wanda ya sake magana. Ita Momi din tunda ta sunkuyar da kanta kasa ba ta sake d'agowa ba tabbatacin ta ji ciwon irin tijarar da Hauwa ta yi mata.
'Dagowar da za ta yi kuwa sai ya yi daidai da kwaranyowar ruwan hawaye a dakalin fuskarta. Ba ta yi yun'kurin gogewa ba sai ta kalleni ta fara magana cikin karaya da zullumi." Amina ni na haifi Salim amma wallahi ba na goyon bayansa akan irin abubuwan da yake aikatawa na rashin kyautatawa. Kuma na nuna masa takaici da 'bacin raina na kuma gargade shi akan kada ya kuskura abu mafi muni ya sake faruwa irin haka. Ina kwance cikin ciwo jiya na samu labarin doki-in-doka da ya shiga tsakaninsu. Wannan shine abinda ya fi tayar mini da hankali na ce kina ina har hakan ta faru. Ban haifi Kamalu da Yusi ba, amma yau zan gaya miki wani abu da nake ji game da yaran a zuciyata wallahi ina sonsu fiye da yadda ki ke tsammani. Yadda nake jin yaranku gabad'aya a raina haka nake jin wanda na haifa. Ina rokonki da Allah da annabi kada ki yanke kyakykyawar ala'kar dake tsakaninmu. Kada ki yi yun'kurin datse k'akkarfan zumuncin da yake tsakanin Adamu da Yusuf domin kuwa d'azu Adam ya je mini cikin damuwa cewa kin tura yaran kano, ki yi hakuri yara su dawo mu cigaba da rayuwa cikin aminci na yi miki alkawari wani abu makamancin wannan ba zai sake faruwa ba. Kuma in sha Allahu Salim zai shigo ya baki ha'kuri komai ya shige da izinin Allah."
Ta gama maganar tana sanya hannu domin share hawayen da yake ta tsiyaya a fuskarta. A nutse na ce." Ki yi hakuri ki daina kuka akan wannan lamari Momi wallahi ban k'ullaceki ba, kuma ni har abada akan yara ba zan yi rigima dake ba, amma ina so ki sani ce wa muddin Kamalu da Salim na tare a Inuwa daya to sa'bani ba zai daina giftawa a tsakaninsu ba. Abinda ba na fatan ya sake faruwa. Ba wai ba ki isa ba ne, kin fi karfin komai a wurina domin ban mance alheri ba, ki yi hakuri yara dai har abada sun bar nan in sha Allahu suna can hannun dangin Babansu sai dai su zo da ziyara. kuma ban isa na yanke zumuci da ala'ka ba tunda ai ba ni na had'a ba."
Ta yi shiru tana gyad'a kanta kafin daga bisani ta yi wani murmushi da babu nishadi ta ce." Shikkenan ba zan karya miki rantsuwarki ba tunda har kin rantse amma ya za a yi da kayansu akwai takardun Yusi na makaranta shi ma Kamalu akwai wanda na sanya aka yi masa domin na gama shiri tsaf za su tafi saudiya domin cigaba da d'ora karatunsu a can makarantar da Salim ya kammala."
A nutse na ce." Babu damuwa duk abinda ya danganci nasu ne za ki iya aiko mini dashi sai nasa a mota a kai musu in sha Allahu rabbi, na gode sosai Allah Ya saka miki da alheri."
A sanyaye ta amsa da "Amin." Kafin ta yun'kura da kyar ta tashi tana gyara madaidaicin hijab din da yake wuyanta ta ce." Zan shiga gida, Allah Ya ba mu alheri."
Ni kadai na amsa mata. Hauwa uffan ba ta ce mana ba har muka 'kare maganarmu.
Gabad'aya muka bi ta da kallo tana tafiya a hankali da rashi kuzari.
Sai bayan da ta fita ne Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Sai ta d'an ban tausayi wallahi."
Na dubeta a hankali na ce." Hauwa zan gaya miki gaskiya abinda ki ka yi wa matar nan ba daidai ba ne, don Allah ko don gaba kada ki sake kwatantawa ko so kike ki kàrasa gawar da ba ta ki ba. Kina kallon fa a yanayin da take ciki amma sai tsalle ki ke kina han'karo kamar za ki kai mata duka. Takaici abinda ki ka yi mata ne fa ya sanyata kuka. Ki duba shekaru da kuma d'awainiyar da take yi da yara don Allah."
Dan murmushi ta yi sai kuma ta ja tsaki a karon da babu adadi ta ce." Ta yi kukan jini ma, ni ina ruwana, sau nawa a sanadinta ana sanya ni kuka, munafukar banza kawai duk abinda take yi wallahi da niyya take yi ai sanin zuciyar mutum sai Allah."
Na gyad'a kai Ina sake ce wa." Magana dai ta mutu Hauwa don Allah ni dai kada hakan ta sake faruwa kin ji."