Sashe 17
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 11 min read
Washe gari kiran wayar Baban Saude ne ya tashe ni da yake jiya na jima ban yi bacci ba idona ya soye da tsabar tunani tare da neman mafita. Wannan shine dalilin da ya sanya da baccin ya kwashe ni bai ajiyeni a kusa ba domin ni kaina tunda nasan ba ni da tsarki sakin jikina na yi sosai motsin kirki ba na so na yi.
Hannu na kyarma na daga wayar lokaci guda idona ya yi tarmazai wani irin yanayi na shiga ba fargaba kiran wayar Baban Saude a irin wannan lokacin yana da ala'ka da abubuwa da yawa. Walau mutuwa ko wata mas'alar domin kuwa nasan a cikinta muke
Muryarsa radau ya amshi gaisuwata ya Dora da fad'in gani nan kan hanya domin kuwa daf nake da shigowa garin abuja.
Na ce." Baban Saude ziyara za ka kawo mana kenan, ka gaya mini abinda ka ke so ka ci yanzu da kaina ma zan shiga kicin din na yi maka.
Ya ce." Ai ba abincin gidanki na zo ci ba Amina, ni ko da me ki ka sauke ni a wajena daidai ne."
A hankali na ce." To shikkenan Baban Saude Allah Ya sauke ka lafiya."
Ya amsa da Amin a takaice kafin ya kashe waya.
Na jima cikin nazari da tunanin dalilin zuwan Baban Saude a wannan safiya haka sai kace wanda ya kwana a hanya. Ashe ni da mutumin nan ba mu isa mu kashe matsala mu binne ta ba har sai ya dangatata da iyayena.
Gaza ha'kuri na yi na daga waya na kira shi. Matarsa ce ta daga har tana kiran sunana. Da sauri na daidaita yanayina muka gaisa a tsanake kafin ta ce." Yallabai din bacci yake yi ko a tashe shi ne?"
Na ce. "A'a kada ki tashe bari idan ya tashi sai ki gaya masa na kira."
Na ji tana fad'in." Yawwa gashi nan ma ya tashi can sama sama na ji maganarsa ban fahimci mai yake cewa ba na ji tana ce wa dashi Maman Yusuf ce." Na ji shi sosai yana fad'in.'' Amina." Ta ba shi amsa da e, ita ce ya ce ta bashi wayar.
Na ji dad'i da bai nuna mata a cikin rikici muke ba. Maganarsa na ji ta daki kunnena."
"Ya aka yi?"
Zuciyata ta yi wani zullo kamar za ta faso kirjina ta fito. Kalmar ''Ya aka ayi din nan tana yi mini ciwo kwarai da aniya, bayan yasan a cikin yin muke ni da shi.
Na daure na furta." Yanzu don girman Allah Baba menene amfanin kiran Baban Saude da ka yi ashe ni da kai ba mu isa mu warware matsalarmu ba, mai ya sa har yanzu ka kasa yarda da ni."
"Ya za a yi na yarda dake Amina? ba ki d'auki hanyar ba domin kuwa duk yadda na so ganin cewa da ni dake mun zama abu daya kin ki ba ni goyon baya, 'kiri-'kiri ki ke nuna mini gadara da ikon akan yaran da ki ka haifa da namijin da ki ka fi so a duniyar nan. Na ha'kura na kyaleki duk da cewar nasan har yanzu zuciyarki na kewar wannan mutumin da ya riga ya gushe a doran duniya bayan da igiyoyin aurena a wuyanki. Yanzu kina gwada fifiko da soyayya akan yaransa. Ni na yi ha'kilo na raba dare wataran ma da rana idan abin ya ciyo ni, na yi ta ko'karin ganin na samar da k'wayayyaina a mahaifarki kina zubarwa saboda ni din kare na bai kai tsaiko ba. Mai yasa zan yarda dake kuwa Amina. Na tabbatar da cewa Hassana da Usaina ma Ubangiji Allah ne ya nuna miki ikonsa a kansu ke kam ai tunda suka diro duniya ba ki isa ki shafe babinsu ba. Za su rayu ko da babu soyayyarki."
Kaina ne ya dinga juyawa maganganunsa na ta amsa mini kunnuwana. Na rasa wadda zan d'auka a ciki na yi nazari. Wane irin zargi ne wannan da mugun bala'in kishi. Yaya Aminu ma da ba kowan kowa ba a duniyar nan musaki mai lalura har shi za a dinga yi wa wannan mugun kishi na bala'i. Zuciyata ta ce da ni wannan shi ake kira da "Kishin kushewa."
Ban ankara ba kawai na ji kittt! ya kashe wayarsa. Na ajiye tawa a saman cinyata kana na tallafe ha'bata tare da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da gaske shi din ya kira Baban Saude saboda yana zargin na sake zubar masa da ciki. Hawaye ne ya silalo saman kuncina, ni kam mutumin nan Ina ganin ni kadai ya tsana a cikinmu, gabad'aya ya ki bari na na huta a rayuwata.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 110
Cikin kasala na yi wanka ina ta nazarin hanyar da zan 'bullo da ita domin ko'karin ganin na kare kaina tunda ban san irin maganganun da ya tsarawa Baban Sauden ba, kuma ban san shi din da me yake tafe ba.
Ban yi wata kwalliyar kirki ba saboda babu nutsuwar yin hakan a tare da ni. Na gama shafa mai ina duba lallen jiya ya sake fitowa sosai ya bi fatar 'kafafu da hannuna ya kwanta abin ban sha'awa.
Zuciyata babu sukuni na fita falo muka gaisa da Baba Tabawa lokacin tara da minti takwas na safe ta kammala shirya abin kari tsaf har ta yi wanka. Na tambayeta Hauwa ta ce mini ba ta fito ba tukkuna.
D'akinta na nufa sai na sameta nad'e a cikin bargo tana bacci. Ban yi yun'kurin tashinta ba saboda nasan illar hakan na janyo kofar a hankali. Na dawo falon na zauna ina kallon Baba Tabawa daka can wurin daning tana gyarawa na ce." Baba mai aka yi ne yau."
Sai da ta d'ago ta dube ni kafin a tsanake ta ce." Kunun gyada ne sai kosai da fanke, sai na yi wa Hauwa Indomee kuma kamar yadda ta buk'ata."
Na ce " To kawai tsiyayo mini kunun da k'osan amma ba mai yawa ba.
Ta amsa da kulawa. Na janye idona daga wurin da take zuciyata na can tunani na tsinkayi maganarta ina d'aga kaina na ganta a tsaye ta miko mini madaidaicin kofin da ta tsiyayo mini kunun kosai kuma ta ajiye mini shi a saman hannun kujerar da nake zaune .
Ban ce komai ba na sanya hannu na kar'ba sai ta zauna gefana jikinta a sanyaye.
"Na gama alamar akwai abinda yake damunki hajiya tun fitowarki na lura da hakan, ina yi muku addu'a tare da fatan Allah Ya iyakance muku wannan rikicin."
Haka kawai sai maganarta ta karya mini zuciya na ji hawaye sun cika idanuwana. Tunda nake shiga matsaltsalu na rayuwa da rikicin duniya ban ta'ba jin kewar mahaifiyata ba sai wannan karon da nake ganin karfi da dabarata sun yi rauni. Komai ya cakude mini na rasa yadda zan yi da rayuwata. A irin wannan yanayin ne ya kamata a ce na je kafadarta na d'ora kaina a kai, na yi kuka ta share mini hawaye ta kuma fahimce ni ba tare da ta kyare ni ba..
Hawaye suka tsinke mini dalili na kasa jimirin jure hana su gudana. Ina ganin kamar kukan ma zai sanya ni na ji sasaauci a cikin zuciyata. Duk da ban rayu da uwata na tsayin lokaci mai yawa ban shaku da ita ba, amma ina shiga tsananin tashin hankali da kewa a duk lokacin da na tuna cewa ba tare raye na tuna irin wahala da gwagwarmayar rayuwar da na fuskata gani a cikinta sau'ki sai daga Allahu rabbi.
Anti Yagana uwa ce a makwafin Mamanmu amma bai zama tilas ta fahimce ni ba kamar yadda uwa take mayar da damuwa da kukan d'anta nata. Uwa ta kan kar'bi wahala da fad'i tashi akan dai duk rayuwar abinda ta haifa. Idan tawa tana raye a 'kalla ni ma zan ji sasaauci ta wani gefen zan je na gaya mata damuwata ta fahimci ni kuma ta ba ni shawarwari.
Cikin nashihun da Baba Tabawa take yi mini babu wadda na fahimta gabad'aya rauni ya yi mini 'kawanya na ma gagara tsayar da hawayen dake karakaina a dakalin fuskata. Daga karshe ta shi na yi ma na nufi daki rigif haka na fadi saman gado na fashe da kuka mai gunji ina kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Baba Tabawa hankalinta ya tashi ainun! domin biyo bayana ta yi da abin karin tana cigaba da rarrashina. Ganin halin da nake ciki ya sanya ta ajiye duk abinda yake hannunta ta tararrayoni jikina itama murya na rawa take fad'in." Amina komai ya yi tsanani maganinsa Allah don Allah kada ki karya mini zuciya da wannan kukan na ki, kowane bawa yana tattare da jarabawa, sai dai ta wannan ta fi wannan haka lamarin yake, amma ni a ganina matsalarku karama ce wadda za ku hadu ku maganceta ba tare da kowa ya ji ba, ban san ba ko bayan wadda na sani akwai wata matsalar da take damunki, don Allah ki yi shiru ki yi mini bayani ko Ina da shawarar da zan iya ba ki."
Rungumeta na yi sosai ina kuka na ce." Baba Tabawa na sare zuciyata ta yi rauni ta yi sanyin da ba za ta iya jimirin jure matsaltsalun da ta jure a can baya ba. Ni marainiya yarana ma marayu Baba Tabawa ga damuwa iri daban-daban wanda nake tare da shi shine mussababbi Baba Tabawa mutumin nan ya tsane ni, wallahi ya hana zuciyata ta huta, bala'in yau daban dana gobe, na gaji! na gaji da auransa ya zame mini karfen kafa a rayuwata."
Ta dinga girgiza kanta tana jimantawa kafin na ji saukar hannunta a kumatuna tana share mini hawaye take ce wa." Ki daina ce wa kin ga ji da ibadar Allah Amina, ba ki sani ba ko wannan itace hanyar shiga aljannarki. Ni kam sai nake ganin kamar kukan dad'i kuke yi, domin kuwa a kaso dari Ubangiji ya yi ba ku kashi tamanin, idan har an samu wani tasgaro da kalubale a cikin kashi darin nan a shawarce godiyar Allah ce za ta biyo baya. Kuna rayuwa ne anan a lullube amma Amina duniyar nan a rikice take wallahi talauci da k'akanakayi ya yi wa al'umma yawa. Matan aure zina zawarawa zina 'yan mata k'ananun yaranmu zina duk domin su ci abinci. A yanzu duk wata mata da Allah ya rufa mata asiri ta samu miji mai kula da iyali da d'aukar nauyin ci da sha da kula da lafiya, to wallahi tallahi ta yi hakuri ta zauna domin idan ta fito rayuwar da za ta fuskanta bayan auran gagarima ce. Amina mace yanzu ko tana da kudi tana kasuwanci muddin ba ta da miji abin zargi ce a wurin mutane koda kuwa tsarkakkiya ce, yanzu nan za ki ji wasu daga cikin marasa fahimta marasa hankali suna kiranta da sunan karuwa. Wannan rayuwar kin yi ta a baya Amina a lokacin duniya ta dan kwance gari bai lalace irin haka ba. Ki yi hakuri ki jure kalubalen gidan auranki in sha Allahu watarana sai labari."
Sosai maganganun Baba Tabawa suka sanyayyar mini da jiki. Duk abinda ta fad'a babu k'arya. Na yi gwagwarmaya na san komai. Amma ni a irin fargabar da nake ci a yanzu sai nake ganin gwara mini zaman babu laluran miji hankalina zai fi kwanciya shin mai ake nema a cikin aure ne haihuwa to na samu. Ina da dukiyar da zan iya ri'ke kaina da yarana marayu. Allah da kansa ya ce a rabu idan abin ya ci tura, ai gabad'aya lamarin aure da maslaha ya zo domin kuwa abu ne na mutum biyu tare da yarjejeniya kafin tabbatuwarsa.
Fuskata na goge a lokacin na ji idanuwana sun tasa sosai, ba komai ne dalili ba sai irin kukan da na yi wanda na shafe tsayin shekaru rabona da yin irinsa.
Wayata dake saman madubi ta fara kara alamun shigowar kira. Da kanta da sauri ta tafi ta je ta d'auko mini ta ba ni na kar'ba ina dubawa A kunnena kawai na sa wayar kafin ba bud'e baki da kyar cikin alamun cushewar murya da dashewa na ce." Na'am.''
Muryarsa babu amo ya furta." Baban Saude ya sauka tun d'azu yanzu haka muna tare da shi sashena da nake saukar ba ki."
Shiru na yi ban ce masa komai ba. Na ji yana fad'in." Ko ba kya ji ne?"
A takaice na ce." Ina ji ya za a yi yanzu to?"
"Ke muke jira?"
Ban bashi amsa ba na kashe wayata jin yadda zuciyata take wani irin harbawa, ina ganin sai mutumin nan ya kaini kasa tukkuna hankalinsa zai kwanta.
Baba Tabawa ta kwashe kayan karin kummalon tana fad'in." Sai dai a had'o miki wani don wannan ya yi sanyi.
Cike da sarkewar murya da numfashi na ce." Ki bari na dawo tukkuna na yi ba'ko daga Maiduguri d'an uwan mamana ne ya zo."
A sanyaye ta furta." Amma lafiya dai ko?"
Ne ce." Baba Tabawa akan maganar 'barin cikin da na yi ne, shine ya kira shi ya gaya masa don yana zargin zubarwa na yi da gangan.
Sai ta shiga girgiza kanta gabad'aya yanayinta ya nuna alamun damuwa da fargaba ta ce." Haka kawai kuma sai ki zubar da ciki Amina, ai kuna da ilimin addini daidai gwargwado wad'anda ma suke yin sakarcinsu a waje su samu ciki ba su zubar ba sai na sunnah, amma ban ji dadin wannan zargin ba.