Sashe 43
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 4 min read
Wataranar asabar da daddare bayan na kammala abinda nake yi a d'akina na shirya tsaf na nufi wurin maigidan haka kawai nake jin shau'ki a cikin raina. Ashe farincikin da zan yi ya na gaba. Na same shi yana ta cike wasu takardu bai dago ba ya amsa mini sallamata na zauna daf dashi Ina duba takardar da take gabanshi. Sunayen mutane ne a jere ban kawo komai ba sai da ya kammala tukkuna ya dube ni yana kashe ido ya furta." Tawan ya ake ciki ne?"
Ni ma na kanne idon ina fad'in." Ya labari?"
Sai ya sa dariya yana fad'in." Yana wajenki ai!"
Ban ce komai ba sai kallonsa nake yi.
Ya d'an sauke ajiyar zuciya kafin ya furta." Kina da wanda za ki kai umara ne?"
Na daga kaina da saurin gaske."
Sai ya ce." Fadi sunansu na shigar yanzu wanda Allah Ya sa yana da rabo."
Na ce." Gwaggo." Ya rubuta Yana fad'in." Daya kenan."
"Baba Tabawa, Baba Sule Ummansu Hadiza Anti Yagana Sahura Ummansu Saminu Hadiza Hamusu."
Na yi shiru ina ta kallonsa yana rubutawa. Ina dariya na ce." Kana so ka ga haukana ko?"
Ya girgiza kansa a nutse ya furta." Duk wanda ki ka kira sunansa da izinin Allah zai je d'akin Allah Amina." Na gyad'a kaina a hankali na ce." Dada ta tsufa da yawa Baban Saude kuma ka kai shi aikin hajji shekara biyu kenan." Ya ce." Ai aikin Hajji daban umara daban a sa sunansa ko?''
Na daga kaina ina kallonsa. Ya rubuta ya dago yana fad'in sai wa kuma."
Na ce." Suke kenan?" Na Fadi hakane kawai ba don sun kare ba, akwai da yawa daga 'yan uwan Mamanmu da kuma bangaran Babanmu. Nasan kuma dole zai tambayi Hauwa duk da yake kusan babu wanda bai je umara ta bangaran mahaifiyarsa ba.
Ya ajiye biron hannunsa Yana fad'in." Amma Hadiza ba ta na prison ba ne Amina?"
Na sauke ajiyar zuciya Ina kallonsa na ce." Ashe ban gaya maka ba ta fito wata uku da suka wuce ta shiga cikin ayarin wad'anda governor ya yi musu afuwa. Tana gida yanzu haka."
Ya gyad'a kansa yana fad'in." To, alhamdulillahi amma kun kaita asibiti ko?"
Na ce." An kai ta lafiyarta lau sai dai ta rame kaf kamaninta ma duk ya canza."
Cikin alhini da jimantawa ya ce." Sai a hankali zata dawo daidai sai ku cigaba da bata shawara ta dage da azkar istigifari da neman afuwa wurin Allah, abu na gaba kuma shine idan ta samu miji ta yi aure shine mutunci."
Na ce." In sha Allahu, mun gode sosai Allah Ya saka da alheri."
Murmushin ya yi kafin ya rike hannuna yana fad'in." Menene abin godiya Hajiya."
Ban ce komai ba illa rausayar da kaina da na yi. Ya janyo ni na fad'a jikinsa ya sanya hannu ya rumgumeni sosai a kirjinsa yasa bakinsa a kunnena yana fad'in." Mu yi soyayya ko?"
Lumshe idona na yi a hankali yayin da na ji yarrr a ilahirin jikina gabad'aya. Ya dan hura mini iskar bakinsa a kunnena cikin wani irin sauti ya furta." I love you kaddarata. Na yi alfahari dake jiya na yi alfahari dake yau na kuma yi alfahari dake gobe. Allah Ya inganta mana rayuwa. Ya albarkaci abinda muka haifa.
Hannuwana duka biyun na sanya na matse shi sosai ina fad'in." Amin Ya Allah, Ubangiji Allah Ya sa mu mutu rana d'aya."
Sai ya fashe da dariya yana ko'karin dago fuskata ina nokewa domin ni har ga Allah a lokacin da zuciya daya na fadi maganar domin sai nake rayawa a raina idan ya rigani mutuwa ya zan yi? idan babu shi a doran duniya babu ni abinda zuciya take raya mini kenan!"
😃 To ni ma da nake bibiyar labarin naku na ce Allah ya amshi adduarki Amina. Idan Kun mutu rana d'aya Ubangiji sai ya jibanci al'amuran yaranku domin shine mai rayawa da kashewa.
ALHAMDULILLAHI.
ALHAMDULILLAHI.
ALHAMDULILLAHI.
Cikin ikon Allah anan na kawo k'arshen wannan littafi mai suna GUDUN AURE ina ro'kon Allah Ya yafe mini zunubi na, abinda na rubuta daidai Kuma ina dai rokansa ya ba mu ladan tare daku masu karatu. Na gode na gode na gode. Ubangiji Allah Ya sada mu da alheri, Allah Ya had'a mu cikin aminci daku a cikin wani littafin nawa da izinin mai duka..🙏