Sashe 4
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 7 min read
Jikina ya sake yin sanyi a nutse na ce." Ki gaya mini Salim din ya nemi wani abu nasa ya rasa ne, ko kuwa ita ma Momin ta nemi wani abu bata gani ba?"
Ta ce." A a babu d'aya Amina, ni kaina ina jin nauyin gaya miki wallahi, Amma ya zama dole ki sani domin ki nemi mafita Salim din ne yake gayawa maigidan wai Kamalu yana lalubensa a cikin dare har yana cire masa gajeran wando!"
Wani irin yamm! na ji tun daga tsakiyar kaina har zuwa kafafuna. Yawun bakina ya tsinke gabana yana fad'uwa na ce." Hauwa wace irin magana ce wannan don girman Allah!"
Ta dafa cinyata a hankali ta ce." Maigidan ya kira Salim domin jin 'karin haske dangane da maganar da ki ka gaya masa a waya tsakaninsa da Kamalu bud'ar bakin yaron sai ya ce masa Kamulu yana nemansa wai har yana cire masa gajeran wando."
Shiru kawai na yi kaina yana juyawa. Abubuwan da suka shud'e a shekarun baya suka dinga dawowa kaina. Yusi da Kamalu. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! maraici maraici maraici! an ce Yusi ya lalata yarinyar mutane, yau kuma an ce Kamalu zai yi luwadi.
Hannu nasa na tallafe ha'bata gabad'aya tunanina ya tsaya cak!
Ta dafa kafadata a sanyaye ta ce." Nasan dole ne ki kadu da jin wannan mummunan labari Amina, ki yi hakuri ban gaya miki da zummar na daga miki hankali ba, wallahi tallahi wannan shine dalilin da ya assasa mana rikici mai zafi saboda na gaya masa cewa wannan sharri ne kawai, kuma bai kamata ya yarda da maganar ba."
Na dube ta a hankali na ce." Kenan ya yarda da abinda Salim din ya gaya masa."
"Ya saurare shi dai a waya bayan sun gama shine yake gaya mini. Na ce to ya sanar dake kuma ya nemi Kamalu shima ya ji daga gare shi ya ce babu daya da zai yi a ciki. Jin haka sai kawai raina ya b'aci na fara nuna masa kuskuran abinda yake shirin aikatawa daga lokacin zamanmu ya rikice wai ban isa na nuna masa yadda zai yi ba. Tunda babu wanda na haifa a cikinsu na ja bakina na yi shiru shi ya san hukuncin da zai yanke."
Cikin alhini da zullumi mai radad'i na ce." Hauwa na gode sosai, ba ki munafurceni ba, kuma duk da ni na haifi Kamalu amma kai tsaye ba zan bada shada a kansa ba, ai d'an yau ne, kuma ba komai ne ya janyo wa yaran hakan ba sai maraici amma in sha Allahu zan d'auki mataki, na gode sosai Allah Ya kula miki da yaranki."
A nutse ta ce." Amin, ki yi hakuri don Allah kada ki sanya damuwa a ranki Amina."
Dariya na yi wadda babu nishadi na ce." Kamalu da Yusi za su bar gidan nan Hauwa koda kuwa hakan shine zai kawo k'arshen zamana daku."
Ta yi shiru tana kallona. Na ce." Wannan itace shawarar da na yanke rigima ce a kwance sai dai Allah ya magantata."
"Kin san Allah kina barin gidan nan zan bar bashi wallahi, ya zauna da ita da yaranta 'yan iska gabad'aya."
Murmushi na yi ina dubanta ita tafi ni ma d'aukar lamarin da zafi.
Tashi ta yi ta fita ranta a 'bace.
Na jingina bayana jikin gado ina sake tariyo maganganunmu. Ni ban san ma ya zan yi ba. Wayata na d'auka domin kiran anti Yagana. Bugun farko ta daga. Jin muryarta sai na raunana kwarai kukan da nake ta han'koron dannewa ya k'wace mini Ina yinsa na ce." Anti Yagana Ina cikin masifa." Furta wannan maganar ya yi daidai da lokacin da ya shigo d'akin ya zauna kan kujerar mudubi yana kallona.
Cikin kuka wiwi! Na cigaba da cewa ." Anti Yagana na yi rashin da har na mutu ba zan maye gurbinsa, na yi rashi anti Yagana ni da yarana muna cikin maraicin Yaya Aminu Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un"
Fadi take yi ki yi shiru ki gaya mini menene abinda yake faruwa Amina kar ki manta fa ke matar wani ce, yanzu babu abinda yake tsakininki da Yaya Aminu sai addu'a.
Cikin kuka na fitar hankali na ce." Anti Yagana ina cikin jarrabawar rayuwa duk inda yarana zasu ra'ba sai an ci zarafinsu, sai an tozartasu, sai an yi musu sharri, anti Yagana maraici akansu a ka fara ne?"
"Kin ga malama kada ki yi mana sabo don Allah, duk mutumin da Ubangiji ya cika jarabtarsa shine mumini kada saboda kin shiga rintsi ki nemi ki kafurcewa Allah."
Shiru na yi Ina jan hanci ina cigaba da sauraranta.
Na ce." Na ji anti Yagana, na ji duk abinda ki ka ce mini, amma idan kin samu labarin mutuwata to don Allah Ina neman alfarma kada wani ya zo ya yi miki dadin baki ya ce ki bashi Kamalu da Yusi zai ri'ke, don Allah ko wanene kada ki bashi mutanan yanzu basu da amana mugwayene azzalumai."
Tashi ya yi, ya nufo ni ya zo zai kwace wayar na mike tsaye da tsalle duk da nauyin jikina da wayar a kunnena na kai masa wani naushi a kirji da k'arfi ya yi baya tare da rike kirjinsa. Cikin raina na ce gwara na kashe ka kafin ka kashe ni.
"Ki gaya mini abinda yake faruwa." Wannan maganar na ji tana fad'a. Na jingina jikin bango(garu) ina numfarfashi sakamakon filinkin din da na yi. Na ce." Yaron nan Salim da na gaya miki suna rikici da Kamalu shine ya ce wai Kamalu yana nemansa da daddare har yana cire masa wan.....Ban kàrasa ba ya buge wayar daga hannuna ta fad'i kasan wajan.
Ya sunkuya ya d'auka tare da kasheta gabad'aya ya sanya cikin aljihunsa.
Daf da ni ya tsaya muka zubawa juna ido. Wani irin kallo yake yi mini wanda na kasa fahimtar ko na menene. Ni kuma wanda nake yi masa na tsantsar tsana ne da takaici.
"Wanene ya gaya miki wannan banzar maganar Amina?"
Kai tsaye na ce." Hauwa ce, ai ita ba munafuka ba ce, kuma uwa ce ta san ciwon haihuwa, idan har kai ba kasan ciwonta ba."
Ya gyada kansa da mamaki mai yawa a tare dashi ya ce." Ni ki ke zagi a fakaice Amina."
Na ce." Idan hakane zagi na zaga."
Murmushi ya yi na takaici ya cigaba da cewa." Ita Hauwa ai kafin mu tawo nan sai da na gargadeta akan kada ta kuskura ta gaya miki maganar nan saboda gudun tashin fitina amma saboda ta shirya shirya mini rikici a gida shine ta sanya kafa ta shure umarnina lallai ranta zai b'aci wallahi."
Na ce." Ai ba ta yi lefi ba gaskiya ta fad'a domin shine zama na amana. Kuma wallahi a yanzu Hauwa ta fiye mini kai sau dubu tunda ka nuna mini zahirinka na gani, ni duk wanda baya k'aunar yarana ni ma bana kaunarsa." Na fad'i maganar cikin 'karaji da ihu!
Ya zo zai ri'ke mini hannu na fizge tare da matsawa cikin babbar murya na ce.'' Kada ka ta'ba ni, domin kuwa babu abinda za ka gaya mini na yarda, ka nuna mini iyakata, na rantse da girman Allah da Annabi sai yaran nan sun bar hannunka tunda ka gaza ri'ke su tsakani da Allah ko da hakan zai yi sanadiyar rabuwarmu a shirye nake."
Kallona kawai yake yi har na dire maganata ya ce." Ki fahimce ni Amina, ban za'bi bangare daya na ajiye daya ba. Ni kaina lamarin ya sanya ni a rud'ani ba kad'an ba. Shirun kuma da na yi ba ina nufin na goyi da bayan maganar Salim ba. Ina bincike ne da kuma hanyar da zan kawo gyara. Akwai nauyi mutuka da gaske na tunkareki da maganar nan. Akwai kunya na titsiye yaron nan Kamalu ina neman hujja akan maganar Salim. Kada ki zarge ni bayan ba ki san menene a zuciyata ba.
"Na gaya maka wallahil-azim ba zan yarda da kanzon kurge ba. A wannan ga'bar ko ni ko kai, Kamalu da Yusi fa basu rasa madogara ba. Sannan Ubansu ba makwadaici ba ne, ba mazinaci ba ne, sannan ba b'arawo ba ne. Banga dalilin da zai sanya a dinga jingina musu manya manyan sharri ba. Ban nemi ka rike mini yara ba. Haka zalika ma ban nemi matarka ta ri'ke mini yarana ba. A ba ni kayana mana dole ne, zan iya rikesu, mu rayu cikin nutsuwa da kwanciyar hankali."