Sashe 30
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 6 min read
Kai na jima ban shiga tashin hankali da nadamar rayuwa ba sai a rasuwar baiwar Allah nan. Tunda gawar ta iso gabad'aya estate din namu ya cika da motoci jama'a daga kowace kusurwa abokanan maigidan dama wasu daga ciki abokan tsohon mijinta ne. Cikin gidanta cike da 'yan uwanta da zuriarsu tare da abokanan arziki da yaranta masu yi mata hidima da shagunanta. Ana ta koke koke masu dauriyar daga ciki kad'ane. Babbar yarinyata Nusaiba sumanta biyu har yanzu ba ta gane wanda yake kanta ba. Nabila kuma tana ta iskokai a wani d'aki da 'yan uwansu sun kulle-kulle kofa don kada ta fito daga inda muke a zaune muna jin ihunta. Cikin masu yi wa Momi wankan gawa har da Baba Tabawa lallai na yaba kwarai da aniya wurin jajuecewarta da dauriyarta koda yake yadda take ba ni labari a gaban idonta mahaifiyarta ta rasu kuma itace ta wanke ta. Wannan ya kara tabbatar mini da cewa Baba Tabawa tana daya daga cikin salihan matan da Ubangiji ya ce lallai yana jin kunyarsu a gidan duniya da lahira dalilin rashin haihuwa.
Ban tashi tabbatar da cewa d'an adam ba a bakin komai yake ba sai da aka gama had'a Momi tsaf cikin likkafani a mike cikin makara ana ta lallabata sunanta gabad'aya ya shafe daga jiya zuwa yau din wasu na kiran ta da gawa wasu na kiranta da marigayiya. Yaranta da mijinta tare da yan uwanta sun kewaye makarar yayin da masu aikinta mata da muke tare da su a gidan suke gefe sun cure kansu wuri d'aya sai sharbar kuka suke yi.
Hajja da Gwaggo suka nufi bakin makarar. Na yi na yi na ja kafata domin bin bayansu na kasa domin wata irin juwa da Hajijiya nake ji idona na ganinsu garagara, hawaye masu d'umi suka silalo kumatuna wanda ya yi daidai da lokacin da na yi hu'bbasa wurin sarrafa kafafuna amma suka doje ban san yadda aka yi ba kawai na ji a kasa na zube a lokacin ne kuma naga kamar gilmawar wani abu daga sannan ban sake gane komai ba sai dana farka tukkuna na tabbatar da cewar suma na yi lokacin har an kaita makwancinta an dawo. Anti Yagana sun iso tare da Inna Uwani. Ban yi mamakin ganin yanayinsu ba domin akwai d'imuwa da tashin hankali na rasuwar da aka kwantsama. Ko baka da ji'bi da mumini fad'in Annabi ne mutuwarsa dole ta nasheka balle wannan matar da alherinta ya rinjayi lefinta mijinta kuma tun kafin ta mutu ya yafe mata jama'ar da suka sallaceta sun zarta wanda Annabi ya fad'a tabbacin samun rahama daga Allah buwayi.
Hajja ta shigo d'akin da muke tana fad'in." To alhamdulillahi tunda ta tashi da ji da ganinta da kuma lafiya mun gode Allah Yagana taimaka mata sai mu koma can gidan nasu mu yi namu zaman domin nan din zaman zai zame mana fitina.
Gwaggo da fitowarta daga bandaki kenan daure da alwala ta ce." Ni ma shawarar da na yanke kenan hakan zai fi alheri."
Anti Yagana ta dube ni a d'an sanyaye kafin ta ce." Sannu ba dai kya jin komai a jikinki ko?"
Kaina na gyada mata a nutse na ce." Ashe kun zo?"
Ta ce." Mun zo mun tarar da gidan a kacame ana ta hayaniya ke kuma gaki a sheme sai da likitanku ta zo ta dubaki fa dogon suma ki ka yi."
Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce." Anti Yagana mai ya faru ne?"
Tabe bakinta ta yi ba ce mini komai ba. Na daga kaina na kalli Hajja dake tsaye jikin bango rumgume da hannunta a kirji nan take na karanci damuwa da b'acin rai a saman fuskata.
Ban sake wata magana ba na tashi zaune hijabi na da yake gefe anti Yagana ta miko mini na zura a jikina tana taimaka mini na yun'kura na tashi ta ri'ke ni. Na ce." Ki cika ni zan iya tafiya da kafafuna. Inna Uwani ta ce." Da dai kin bari ta rike ki jikin naki ai har yanzu bai gama daidaita ba.
Hajja da Gwaggo suka yi gaba.
Wani irin kallo dangin marigayiyar suke mini na tsana da kyama. Anti Yagana ta juyar da kanta ba ta ce komai ba. Ni ma ban ce musu komai ba na ji daya daga cikinsu fad'in." Kun kaita kasa kun ji dad'i, sai ku jirayi hakki domin wallahi ba mu yafe muku ba, duk abinda za ki nuna a banza a wofi Maryam dai karshenta ya yi kyau ku kam in sha Allahu mutuwar wulakanci za ku yi."
Maganganunta ne suka dinga yi mini amsa kuwawa! a kunne gabana ya dinga bugawa da karfi da karfi. Wannan babban kalubalen ban shirya tararsa ba a yanzu domin ba ni da hujjar da zan kare kaina Allah shine shahidi.
Muka fita tun daga haraba cike da jama'a har zuwa waje mutane cike cikin manya manyan rumfunan da aka kafa.
Kafafuna suka dinga hardewa gabad'aya sai na tsargu domin maganganun da matar nan ta yi sun sake dakusar da duk wani karsashi da kwarin gwiwata. Shin wane irin kallo jama'a suke yi mini a yanzu dana fito cikinsu. Cikin dubara na janyo saman hijabina na rufe fuskata dashi dama rike nake a hannun anti Yagana. Ina jin sanda Hajja ta tsaya suna gaisawa da ire-iren abokanan Yallabai din na ce da anti Yagana ta yi sauri mu wuce domin ba ni da wani kumaji da nutsuwar da zan iya tsayuwa a gaban jama'a domin kar'bar ta'azziya. Muka yi gaba muka bar su ita da Gwaggo suna gaisawa.
Kuryar d'akina anti Yagana ta dangane da ni na zauna kan gado kamar wata sabuwar amarya na yaye hijabin da ya katange fuskata. Muka had'a Ido nan take na rushe da kuka na ri'ke hannunta katamau! Jikina na kyarma na furta." Anti Yagana Momi ta mutu sanadiyar lalure-laluren da suka yi mata hijabi, ina tsoron kada 'yan uwanta da jama'a su jinginta rasuwarta da ni da Hauwa, ai kin ji abinda daya daga cikin 'yan uwanta take fad'a ko?"
[12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: *117*
" 'Karamin tsaki ta yi kafin ta ce."Amina duk wanda zai alak'anta rasuwar matar nan daku to dama can ba masoyinta ba ne. Su kansu 'yan uwan nata da suke ko'karin tashin husuma ba kaunarta suke yi ba tunda har suke jingina rasuwarta da wani abu daban. Kishi halak ne kuma duk gidan da aka had'a mace fiye da biyu ana samun irin wad'annan matsaltsalun. A ganina wannan ba wani abun damuwa ba ne, rigima ce suke nema kuma in sha Allah rabbi har a share makoki ba za mu tanka musu ba. Ni gidan ma ba zan sake shiga ba tunda na lura duk yawansu babu mai dattako a cikinsu. Rashi Kam ba su kadai suka yi ba mutane da yawa ne domin Hajiya Maryam bango ce majingina kuma uwar marayu har ma da masu uban. Don haka iyakacin k'aunar da za su nuna mata su bita da addu'a tare da rungumar abinda ta bari shine kawai sakamakon da za su yi mata bayan rayuwarta. Don haka ki samu nutsuwa ki kuma daina tunanin kina da hannu lokacinta ne kawai ya yi kuma babu wanda ya isa ya tsalle rana da sa'in komawarsa ga Allah."
Maganganun anti Yagana sun d'an sanya ni mini nutsuwa kad'an amma har yanzu zuciyata ba ta daina yin tsalle akan abinda na ji yana fitowa daga bakin 'yar uwar marigayiyar ba.
Wajen daya da wani Abu Babanmu suka iso tare da baba Sule da Ummansu Hadiza kamar yadda ya fad'a. Baban Saude ne har yanzu bai shigo inda nake ba, anti Yagana kuma ta gaya mini tare suke da Babansu Fadila har da Baba Madu wanda ya kasance babban yayansu Mamanmu, mahaifin Babandi.