Sashe 42
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 6 min read
Rayuwa kenan ko da na gayawa Hauwa makasudin zuwansa kano. Ta yi mamaki amma irin na farinciki ko kad'an ban ga alamun kyashi ko hassada a cikin kwayar idonta ba. Idan ma ta ji wani abu a ranta a zahiri ta daure bata nuna mini ba.
Kamar yadda ya yi alkawari kuwa a ranar ya dawo bai kwana ba yana gaya mini Anti Yagana tana gaisheni da sauran 'yan uwan Babanmu domin duk sun halarci taron har Yaya Talatu Yayarsu Yaya Aminu dake aure a kamaru itama ta zo. Duka suka bada sakon gaisuwarsu. Na ce ina amsawa. Lallai taron ya tattara manyan malamai attajirai da alarammomi daban-daban. Hoton nan da aka yi a wurin ya dinga nuna mini a wayarsa Kamaluna cikin manya masu daraja da tsantsar ilimi. Lallai babu abinda ya gagari Ubangiji babu shakka har na koma ga Ubangijin talikai ba zan ta'ba daina godiya gare shi ba. Ga kuma wani farincikin da na kasa boye shi a cikin raina ganin har da Salim da Adamu wurin taron kuma suna cike da walwala tare da farinciki akwai wani hoto da ya d'auki hankalina duk a cikin hotonan da aka yi a wurin taron bayan wanda aka yi musu su biyar na farko Kamalun sai Saminu Turmuzi Yusi da Adam, gabad'aya yaran suna cikin manyan kaya sun zama samari masu nutsuwar da babu rawar kai a cikinta. Turmuzi ya nutsu sosai haka zalika ma Saminu da ya zama k'ato dama can yana da jikin girma a gidanmu. Na cigaba da godiya ga Allah Ina sake duba hoton da ya yi masifar kyau ya kuma d'auke mini hankali kwarai da gaske
shine wanda aka yi musu su biyu Salim din da Kamalu suna ri'ke da hannun juna suna dariya a take a lokacin na d'ora shi a saman profile dina na kuma sanya shi a fuskar wayata.
Sai hawayen da nake ta dannewa suka zo kumatuna tuna irin artabun da aka yi a baya na tuna babban burin Momi kenan tabbatuwar zumuncin yaran da wannan ta rasu a cikin ranta. Sai kawai na gagara kasa kàrasa kallon hoton nan na mik'a masa wayarsa tare da sanya duka tafikan hannayena na rufe fuskata ina kuka wanda fitarsa yake yi mini wahalar gaske..
Ya tallafo ni sosai a jikinsa yana d'an tatta'ba wuyana a lokacin shima bakinsa mutuwa ya yi don bai iya yin rarrashin ta hanyar kalamai ba sai ta sigar da ya tabbatar da cewar zan lallasu. Sosai naga zahirin k'auna da kulawa mai wahalar samu a daran.
MURFI.
Tabbas komai ya yi farko yana da k'arshe kamar yadda Ubangiji Allah Ya hallici rayuwa da mutuwa. Ya kuma hallici kuruciya da tsufa. Ya hallici talauci da arziki. Ya hallici namiji da mace ya hallici dabbobi da tsirai. Ba shakka a shekarun da na yi tun daga haihuwata zuwa yau na fuskanci kalubale na rayuwa ma bambamta na kuma kar'ba hannu bibbiyu. Idan har Ubangiji ya wanzar da kai a wannan duniyar tasa ya zama dole ka bi dukkinin dokokinsa kuma kayi biyayya ga umarninsa. Ni 'yar adam ce kuma ajiza. Nasan ina tattare da kuskure wanda yake kan kowane bawa har da annabawan Allah ba su tsallake ba. Cikin irin jarabawar da Allah ya yi mana ni da maigidana wanda a yanzu muka samu kyakykyawar fahimta shine haihuwar yara mata biyu masu d'auke da lalurar sikila tun bayan twin's wanda sune cikkaku mutane masu ingantaciyar lafiya a cikin yarana dashi. Allah Ya azurta ni da mai sunan Hajja Halimatu muna kiranta da Suhaila tana d'auke da lalurar. Allah Ya sake azurta ni da mai suna Saratu wadda ta ci tudu biyu sunan Mamana da kuma yayarsa Hajiya saratu Muna kiranta da Islam. Wad'annan yara guda biyu sai suka tsaye mana a rai ni da mahaifinsu wanda har soyayya da tausayin da yake nunawa a kansu ta d'an so ta shafi zamantakewarmu da Hauwa duk da tana iyakacin bakin k'okarinta wurin daurewa amma a wasu lukutan takan nuna rashin jin dadinta akan irin abubuwan da yake aikatawa akan yaran. Ba na ganin lefinta wani sa'in domin kuwa zuciya ba ta da kashi ita da take da lafiyayyun yaran hud'u maza uku daya mace daya. Khalil Minal Sultan Aslam mai sunan mahaifinta kenan sai
Mahamud ba su samu kwatankwancin wannan soyayyar ba cikinsu gwara Minal ita tin dama 'yar gidansa ce tuntuni. Tana jurewa sosai kuma tana ta ya ni kula da yaran a duk lokacin da ciwon ya motsa musu yadda nake shiga damuwa itama haka take shiga mu dinga zurga-zurga asibiti tare har sai da Babansu ya samar musu da likita na mussaman domin kulawa da su a duk lokacin da abin ya motsa. Suna rayuwa irin yadda 'yan uwansu suke yi cikin jin dadi da kulawa kuma suna zuwa makaranta sai dai wasu al'amuran masu tsauri suna gagararsu ba don komai ba sai don yanayin lafiyarsu. Amma karshen kulawa da so ubansu yana yi musu abinda na gama fahimta tsabar tausayi ne na iyaye. A duk sanda wata daga ciki ta kama ciwo tare suke yi domin yakan fi ni shiga damuwa da tashin hankali. Ba komai ake yi wa ba ran nan guda daya shi ake tattali da kashewa dukiya. Akwai wata rana da ciwon ya motsawa Sulaita ta dinga suma ya gigice kwarai da gaske shi da kansa ya jinyace ta a asibiti tsayin sati biyu ta samu lafiya. Na riga na gama fahimtarsa mutuwa kawai yake tsoro kuma ko da ciwo ko babu za a tafi. Shiyasa idan ciwon ya motsa baaya garin ba na gaya masa domin zai daga hankalinsa har ya gagara yin wasu al'amuran na rayuwarsa. Da yake ma muna kula da su sosai da bin dokoki ba kasafai abin yake motsawa ba sai a shafe wattani har shekara ma wata daga ciki bata kwanta ba.
'yan uwansu duka suna son su tare da taya mu kula da su. Don dole muka ha'kura da haihuwa saboda shawarwarin da ake ba mu. Ni da shi muke yin dabaru wurin kwanciyar aure wanda har yanzu akan hakan muke saboda ya yi rantsuwa babu rabuwa kamar yadda wasu daga cikin likitocin ke bashi shawara ya kuma ce babu maganar juya mahaifa ko shan maganin hana d'aukar ciki. Sai dai mu yi dabaru idan har rabo ya rantse an samu karuwa zai kar'ba Allah ne mai ji'bantar al'amura.
Bai sake shawa'ar k'ara wani auran ba tun bayan turka-turkar da aka sha da Nabila ta gaji ta ha'kura sai bayan da Salim ya koma legos da zama tukkuna muka fahimci dama ba da niyyar kula da su ta tare musu a gida ba da niyyar ta auri maigidanmu ne. Ta cigaba da business dinta sai ta fi wata biyu a Dubai bata dawo ba. Karshe maigidan ya dawo da Adam gidanmu ya damka mana amanarsa. Dama kuma can shi ba shi da matsala kusan duka ya fi su nutsuwa da sanin ya kamata. Dole tasa itama Nusaiba ta ajiye komai ta nemi shiri damu. Cikinmu babu wanda ya kyamaceta ni hakan ma dadi ya yi mini sosai domin babban burina mahaifiyarsu ta kasance cikin farinciki a kabarinta ni ma na samu irin ladan da ta samu na ri'kon maraya.