← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 43

Sashe 15

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 10 min read

Bayan mun gama maganar sai na kashe wayar na nufi kicin domin anan nake jin motsin Baba Tabawa na sameta tana ta buga sakawara a turmi. Na ce." Sannu da aiki Baba." Ta juyo da sauri tana amsawa. Na ce." Baba ko dai a samo miki wadda za ku dinga aikin nan tare, dukan sakawara na mai k'wari ne."
Tana dariya ta ce." Ni ma da kwarina ai, kuma aikin duka duka guda nawa yake. Yara ba anan suke cin abinci ba, ku biyu ne fa sai ni ta uku sai Masa'udu sai masu gadi biyu shikkenan fa, to sai kuma mai gayya mai aiki idan ya shigo gidan shi ma kuma sa'i da lokaci ne.
"Na ce." Hakane amma duk da haka za a cigita wadda za ta taimaka miki koda da wanke wanke da shara ne ke kuma sai ki ji da girkin ko.''
Ta gyada kanta tana fad'in." To hakan ya yi babu lefi, yau na ce bari na yi sakawara an kwana biyu ba a yi ba. Na ce." Hakane kin ga ma tana daya daga cikin abinda maigidan yake so bayan towon da kike masa." Tana bud'e leda ta ce." Ina kuwa fatan Allah Ya sa ya shigo gidan yau." Na amsa da amin a takaice kafin bar kicin din jin alamun motsi a falon.
Khalil ne tare da Usaina sai wata matashiyar budurwa da bata haura shekaru ashirin da biyar ba.
Rige-rigen gaishe ni suka fara yi har da tsugunawa "Mama ina yini." In ji Khalil na amsa ina dariya tare da nazartarsu yaran suna cike da walwalarsu da annushuwa gasu nan cikin suttura mai amince. Itama ta tsuguna "Mama ina yini." Usaina kenan. Dariya ta kama ni na ce." Ina yini Usai ina Hassana da Minal" Ta tashi tsaye tana ce wa." Suna can gida." Khalil ya ce. Momi ce ta ce wai ga mai lallan da take yi mata."

Na ce." Aikuwa ka ce mata mun gode sosai." Suka juya za su fita sai na ce." Kai Khalil dawo ku shiga ku gaida Mamanka mana." Ya ce." To. D'akinta suka nufa tare da Usaina tana bin sa zugwi-zugwi a baya. Na sauke ajiyar zuciya bayan shigewarsu na juyo kan mai lallan cikin nutsuwa ta gaishe ni na amsa ina fad'in." Wane iri za a yi mana ja ne ko baki?"
Tana fito da kayan aikinta daga cikin wata 'yar jaka ta ce." Duk biyun Ina yi wanda kuke so za a yi."
Na ce." To a yi mini duka ja da bakin. Amma dai ba na son dogon zama. Ta ce." In sha Allah daga nan zuwa magriba komai ya kammala."
Khalil ne ya zo ya gifta ni yana goge fuska. Da sauri na ce." Kai menene ." Bai ce mini komai ba ya wuce yana dafe idonsa. Kawai na ji fashewar kukan Usaina cikin gwarancinta tana ce wa." Mama ta dake shi a fuska."
Da wani irin yanayi na ce ." Mai ka yi mata?"
"Ba komai." Ya fad'a da sauri ya kama hanyar fita kamar ma a tsorace yake Usainar ta bi bayansa itama da sauri.
D'akin na shiga na ji motsinta a bandaki tana ta kakarin amai. Can na bita sai da ta gama tukkuna ta wanko fuskarta ta fito koda ta gan ni a tsaye a bakin kofa ba ta ce mini komai ba ta nemi gefan gado ta zauna. Laulayin ne ya dawo mata sabo da kuma hatsaniyar nan da muke ciki gabad'aya duk yanayinta ya canza ga wani uban haske da ta yi fau sai wasu k'ananun kuraje da suka feso mata a fuska.
Na ce." Wai ba ki da lafiya dama Hauwa."
Tabe bakinta ta yi kafin ta girgiza kai ta ce." Amai ne ya takura mini wallahi cikin 'yan kwanakin nan, amma in banda shi babu abinda ya dame ni."
Na gyad'a kaina a sanyaye na ce." Allah Ya bada lafiya." A takaice ta amsa da Amin.
Na ce." Khalil ya fito yana kuka Hauwa ba kya neman zaman lafiya ko, kin fi kowa sanin abinda mutumin nan ya tsana a rayuwarsa a daki yaran nan mussaman shi Khalil din daga gaisuwa kuma sai duka fisabillahi , ai ba shi ya yi miki ba."
"So na ke a yi ta take ai, shiyasa na dake shi. Ni ma ai iyayene suka haife ni. Ya dake ni a fuska kwanaki yanzu kuma yana dukan zuciyata da iyakacin karfinsa. Bai isa dai ya canzawa towo suna ba."
Shiru na yi Ina nazarin maganarta kafin na ce." Duk wannan bai ta so ba, za ki dasawa yaron nan k'iyayyarki da jin tsoronki a cikin ransa. zai kara yin nesa dake tunda tsakaninku duka ne da kyara da hantara, don girman Allah ki daina."
Hannu ta daga mini sai kuma hawaye suka k'wace mata ta ce." Kin san irin rad'adin da nake ji a zuciyata kuwa Amina ? wai Yaya Tajo shine yake fifita wata bare wadda ba su had'a dangantakar komai ba akaina. Na haihu dashi Bata haihu dashi ba. Jinina ne shakiki. Ita kuwa a duniya suka had'u, amma ya tozarta rayuwata a kanta. Wallahi har na mutu ba zan yafewa matar nan da alhalinta ba."
"Kai! Innalillahi! don darajar Allah Hauwa maganar nan ta mutu haka na rantse da Allah ta ishe ni. Ki gyara tsakaninki da shi kawai ki daina duba wata dangantaka namiji ne za ki ga abinda ya fi haka fa."
Shiru ta yi ba ta ce komai ba, na ce." Ga mai lalle ta zo za ta yi mana, ki fito falo."
Ta dube "Kin ga na yi kama da wadda za ta yi wani lalle yanzu?"
Na ce." Kwarai kuwa, ai ke ya kamata ma ki yi kitso da lalle domin jan hankalin mijinki ku daidaita har ya janye abinda ya ratsa tsakaninku."
Ta ja tsaki tare da gyara kwanciyarta tana fad'in." Kada Allah Ya sa ya janye wallahi babu abinda zan yi, ai ke ce matar gida."
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 109
Na gyad'a kaina ba tare da na sake yin wata magana ba na juya na fita daga d'akin gabad'aya zuciya sam babu dadi.
Yarinyar ta iya lalle sosai tana da zane ganin kamar ta d'auki mai wahala da jinkiri ya sanya na ce ta takaita domin ba ni son zama shine dalilin ma da ya sanya ban fiye yin k'unshin ba.
Baba Tabawa ta kammala aikinta ta fito ta zauna a falon muna hira jefi-jefi har yarinyar ta kammala tsaf ta had'a kan kayanta. Na ce." Ai kina da acct ko?"
Ta ce." E, ina dashi amma momi ta ce da ni kada na kar'bi komai."
Cike da mamaki na ce." Saboda me?" Tana murmushi ta furta." Da farko antina ce take mata lalle sai ta yi aure ni ma dama tana koya mini shine na kar'bi sana'ar duk karshen wata nake shigowa cikin estate din nan naku akwai wad'anda nake yi wa bayan momi din. Mun saba k'warai da ita ta yi wa antina komai haka zalika ta samawa babban yayanmu gurbi a daya daga cikin shagunanta dake garin nan, gashi nan har ya yi aure shekara daya kenan matarshi ta haifi mace ya sanya mata sunan momi din wato Maryam muna kiranta da Sahiba."
Da murmushi a fuskata na ce." Duk da haka dai ai ni ma alheri zan yi miki ganin irin yadda ki ka b'ata lokaci wurin yi mini ado da zananan henna mai kyau, shin ko ba kya so mu saba ne?"
Dariya ta yi kafin ta ce." Kai anti wannan ba komai ba ne akan wanda nake yi don na ji kin ce na takaita ne shiyasa amma da wanda zan yi miki sai ya fi wannan tsaruwa."
Na ce." Wannan din ma ya burge ni sosai na gode miki, amma ai ko turare kya kar'ba ko."
Ta yi kasa da kanta tana murmushi. Ni ma murmushi nake yi can kasan zuciyata kuma ina tunanin idan har mutane za su dinga yabonka tun kana raye tabbas babu abinda zai hana ka sha'kar rahamar Allah idan ka gushe! wato ita dai Momi ko'ina alherinta zagayawa yake yi duk wanda ala'ka ta had'aka dashi muddin ya santa to alherinta zai fara gaya maka.
Muna nan zaune muna hira da ita budurwar wadda take gaya mini sunanta Lad'ifa iyayenta yan asalin jalingo ne aiki ya kawo mahaifinsu nan abuja amma k'aramin ma'aikaci ne..
Ta duba agogon da yake tsintsinyar hannunta na dama wanda nake hasashen tana d'aura shi ne domin duba lokaci a sa'in da ta d'aurawa mutam lalle da kwance shi.
Ta ce." Yanzu sai a cire tunda ya samu awa biyu cikakku. Dama dalilin da ya sanya ban tafi ba kenan.. ta d'auko wata leda babba da cokali mai dan fadi daga sama cikin nutsuwa ta fara cire lallen kafin ta d'aye salatif din zanen ya fito d'au ya yi bala'in kyau da kamawa. Baba Tabawa fadi take yi "Ashe haka kike da cin lalle Amina amma ba kya damuwa da yi."
Na ce." Duk da haka dai ai lallensu daban yake suna yi masa hadi na mussaman."
Da kaina na cire na hannun ya tafi da ni sosai nan da nan na ga ba dawo mace har ina jin dadin duba hannuna. Na ji tana ce wa." Sai gobe zai sake fitowa sosai." Tsaf ta goge mini kaf ta shafe duk inda lallen yake da wani abu sannan ta sake had'a kayanta a karo na biyu. Baba Tabawa da kanta ta d'auko mini takalmin da da nake amfani da shi a d'akina ta kawo mini na sanya na tashi ina fad'in.'' Ladifa alwala ai ta zama dole da fatan babu matsala ko." Tana murmushi ta ce." Babu matsala anti."
Kai tsaye d'aki ba wuce na had'o mata Turaruka da sabulai.
Fitowa ta yi daidai da lokacin da ya shigo yana daga bakin kofa suna magana da yarinyar kamar sun d'an saba da juna ko da yake shi din ba ma'abocin shariya ba ne idan yau kuka hadu to zai mu'amulanceka kamar kun yi shekara da sanin juna, mutum mai sau'ki hali da nuna shi ba wani ba ne a rayuwa. Ledar hannuna na mik'a mata ina cewa "Ki gaishe da mutan gidan, tunda kin ki kar'bar kudi ga wannan sai ki yi amfani da su, na gode kwarai."
Ta kar'ba tana godiya sosai kafin ta kama hanya ta fita cike da nutsuwa. Baba Tabawa ta wuce dakinta itama. Sai mu biyu a falon na daure na ce." Barka da shigowa."
A takaice ya amsa kafin ya nemi hanyar matattakalar samansa. Ban yi kasa a gwiwa ba na bi bayansa. Ya shiga bandaki nasan alwala zai yi ya fito yana gyara hannun rigarsa dake tattare. Kallo daya ya yi mini ya kama hanya zai fita na ce." Idan babu damuwa Ina son magana da kai."
Bai juyo ya dube ni ba ya furta." To, bari na dawo daga massalaci." Ya fice a gaggauce.
Na samu gefan gado na zauna babu wani karsashi a tattare da ni, nasan da ban yi masa magana ba, ba zama lallai idan ya fita ya dawo ba, shigowar nan ma nasan ya yi ta ne akan dole domin sanin halin da muke ciki. Idan yana irin wannan nukufurcin da d'aukewar kai wani irin damuwa nake shiga mara dad'i.
To ban yi tsammanin amsa min din da ya yi ta bogi ba ce sai da naga har an yi Isha'i ta shige bai dawo gidan ba ya barni zaune a inda ya bar ni ina dakon shigowarsa. Bakwai saura ya fita yanzu gashi takwas har da minti ashirin na samu kimanin awa d'aya da wani abu zaune zuru a dakinsa.
Na tashi na sauka kasa raina a dagule haka kawai nake kasa jimirin jure shariyarsa akaina duk dauriyata gazawa nake yi, kuma da na ce ina son magana da shi zahiri ko ya dawo din wallahi ban san abinda zan ce masa ba.
Waya na d'auka na kira shi, bai yi jinkiri ba kuwa ya daga yana tambayata menene. Daburcewa na yi kafin daga bisani na daure na ce." Ka zo."
Ya ce." Akan wane dalili."
Shiru na yi Ina dan tunani sannan na ce." A lissafin da kake yi yau kwanan wanene a cikinmu?"
Kai tsaye ya ce." Kwana kamar yaya."
Na ce." Kwanan girki mana, wacece take da kai?"
Ya ce." Momi ce take da ni ma, saboda itace nagartacciya matar da take gudun fushina ita nake ganin zan iya kwanan aure da ita, domin zahiri da bad'ininta babu mugunta ko zagon kasa balle zalinci a tare da ita."
Shiru na yi maganarsa na dukan kaina. Na daure na furta." To mai kake nufi?"
"Ba na nufin komai, kawai dai ya kamata a ce na yi nesa daku dalili ban san menene a zukatanku ba ke da ita Hauwan mai aikawa a sayo miki maganin wankin mahaifa."
Maganar ta yi mini nauyi sosai, dama nasan abinda yake ta sa'barsa kenan. Na ce." Ai ba haka kawai ta aika a ka sayo mini maganin wankin mahaifa ba sai da dalili, idan ma kana ganin da hannunta a wannan case din to ka d'auki hakkinta wallahi."
Chapter 15 · 0% Book details