Sashe 34
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 11 min read
Don dole na dinga kar'bar towon da yake ba ni a bakina ina ci ina goge kwallar da take fitowa daga idona. Da kyar na ci rabin malmala na turje na daina kar'ba muka shiga toilet a tare wai zai yi mini wanka nan ma sai da muka yi kokawa kamar sababbin amare ina share hawayen takaici haka na yi wankan yana tattabe mini jiki muka fito. Towel ne kawai a jikina a daure na d'auki kayana zan sanya ya kwace. Cike da takaici na ce." Yaron zan je na kar'bo maka wurin Baba Tabawa fa."
Yana ko'karin kashe fitilar gefan gadon ya ce." A yanzu dare ya yi da safe na gan shi sai mu gaisa sosai, ke dai mu kwanta kawai." Ya tura ni na yi kwanciyar ringingine dogare kafafuna na yi da zummar tashi ya raba nasa kafafun a kaina ya dabaibayeni. Abubuwa na tashin hankali da gigita lissafi ya fara yi mini jikinsa na wani irin rawa. Na dinga matse jikina ina ya'ki da gangar jikina da zuciyata akan kin 'karbar abinda yake mini, amma ban yi nasara ba, cikin kankanin lokaci ya fitar da ni daga hayyacina na kasa gane shin a duniya nake ko ni din ma na shilla barzahu ne ban sani ba. Kidima kam da ficewa daga hayyaci mun yi tunda abin ai ba sabo ba ne a wurinmu ya riga ya gama zame mana jiki sosai ya gurje ni ya gamsu na gamsu babu 'karya..
[12/21, 7:01 PM] bintaumarabbale: *119*
Da asuba na sauka kasa bayan fitarsa sallah. Wanka na yi sosai da ruwan d'umi na gasa jikina. Anti Yagana duk tana zaune saman dadduma tana kallona na fito daga bandakin na kintsa jikina sannan na gabatar da sallah. Na shafa a nutse na juyo ina kallonta lokacin ta zame ta kwanta saman dadduma amma ba bacci take yi ba carbin da yake makale a hannunta take ja. A tsanake na gaisheta ba tare da tashi ba ta amsa mini tana kallona kafin ta sauke ajiyar zuciya ta furta." Gobe da wuri zan kama hanya Amina, jiya da daddare Babansu Fadila ya kira yake gaya mini mijinta ya kira shi wai bata da lafiya har da su karin ruwa."
'Yar dariya na yi kafin na ce." Anti Yagana ta kusa goya jika kenan."
Harara ta mako mini tana tabe bakinta."
Na ce." E, mana anti ai idan ki ka ji an fara da haka to k'aruwa ce."
Ta girgiza kanta tana fad'in. " Yaran yanzu ba sa saurarawa 'yayan mutane daka an kai maka yarinya wata d'aya ka had'ata da lalura wasu fa ko shekara ba sa yi suke haihuwa."
Da murmushi a saman fuskarta na ce." Hakane anti Yagana ai gwara matasan su yi auran da wuri ya fi alheri akan su dinga zinace-zinace kuma bari na gaya miki wani abu ba fa samarin ne kadai suke da wannan kawazucin ba har da 'yan matan wallahi dukkaninsu son auran suke yi."
Ta yi shiru tana ta'be bakinta. Na ce." Kawai ki yi mata addu'ar Allah ya raba su lafiya, domin tunda ki ka ji an fara da haka to an gamu."
Ta ce." To Allah Ya raba su lafiya." Na amsa da "Amin ko ke fa."
Muka dan yi shiru na dan wani lokaci kafin ta ce." Wallahi ina tausayawa jama'ar da suke karkashin matar nan, da yawa akwai wad'anda suke d'aukar dawainiya mai yawa ta iyali iyaye da yan'uwa duka a karkashinta yau gashi ta fad'i ta mutu dole za su shiga wani yanayi wanda ba zai yi musu dadi ba. Su kadai nake tausayawa sosai dalili yaranku da suke ri'ke a hannunta ai jajensu kalilan ne tunda kuna raye sai ku cigaba da kula da yaranku Amma jama'ar da suke ci da sha a kasanta Allah ne kad'ai ya san su."
"Hakane anti Yagana to ya za a yi ne? Lokacin ta ya yi cikinmu gabad'aya babu wanda ya isa ya dakatar da komawarta ga wanda ya halliceta hakika ya fi mu sonta shiyasa ya kira ta zuwa gare shi."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Ubangiji Allah Ya sa mu dace amma mutuwa kadai wa'azi idan har za mu hankalta."
Haka muka kasance a d'akin muna tattauna batutuwa da yawa har garin ya yi haske sosai takwas saura yaran suka shigo su biyu Kamalu da Yusi. Gabad'aya muka zuba musu ido ni da ita. Yusi ya fyade sosai jikinsa a sanyaye ya zauna a gefena. Ban zan yi mamakin ganinshi da rashin kuzari ba. Ni nasan wacece Momi a wurinsa yadda ya shaku da ita ina tsammanin bai shaku da ni hakan ba, iya so da k'auna da kulawa ta nuna masa kwarai kowa ya sheda hakan, shiyasa duk halin da zai shiga ba zai zama abin mamaki ba.
Muka gaisa da su cikin kulawa. Na dube shi a hankali na ce." Yusi ban yi maka gaisuwa ba ko."
Ya kalle ni sai kuma ya d'an yi murmushi wanda daga ganinsa 'kago shi yayi domin babu wani nishadi a tare dashi.
Na ce." Ka yi hakuri, lokacin ta ne ya yi kuma kowa ita yake jira babu wanda zai zauna a duniya, ai ita ta samu sheda da yabo ta kowane fanni don haka muna yi mata kyakykyawan zato in sha Allahu aljanna madaukakiya zata kasance yanzu gatan da za ku yi mata shine addu'a.
Kansa a sunkuye har na gama maganata bai iya cewa komai ba sai yatsunsa da na gani ya sanya yana goge kwallar da take ko'karin zuba a kumatunsa.
Na d'auke kaina jin zuciyata na nema ta karye na mayar da hankalina kan Anti Yagana da Kamalu ina jinsu suna tattauna batutuwan da suka shafi karatun da yake yi na neman da'awa. Ban ce komai ba ina dai sauraransu tana ta bashi shawarwari akan ya kula sosai ya san irin Malaman dai zai dinga bi domin neman fatawa dalili akwai Malaman da suke a dilmiye kuma su dilmiyar da mabiyansu idan suna kan a'kidarsu to sune masu gaskiya babu wanda zai kawo wata fatawa ko sahihan hadisan da suka inganta su aminta da hakan, babu wanda ya iya ya sani sai su. Babu zagi babu k'ago abinda babu shi a cikin al'kur'ani mai girma da hadisai a tabbatar dashi. Tana sake jadadda masa lallai ne ya kula ya san abinda zai fad'a mai inganci ne ya karanta cikin sahihan hadisan Annabi. Na ji dadin shawarwarin da take ba shi sosai domin ni kaina ni ma ina da burin na zaunar dashi domin na sake jan kunansa dalili ba na so ya yi zurfi akan a'kidar da yake kai a zo ana samu matsala da shi ko ana rigima da shi akan addini.
ranar dai Hajja da Gwaggo ne kadai suka koma gidan mutuwar anti Yagana ta kwanta a d'aki tare da fad'in jikinta ciwo yake yi mata. Ni kaina ban ji sha'awar sake shiga gidan ba domin Ina gudun abinda zai sanya wata matsalar ta tashi wadda ba fata ake yi ba, tunda dai su 'yan uwanta rashinta bai dame su ba.
Haka muka yi namu zaman makokin a gida duk wanda ya kamata yana shigowa ya yi mana gaisuwa ni da Hajja mussaman abokansa da matayensu. Ranar da aka yi sadakar uku Anti Yagana ta tafi kamar yadda ta fad'a maigidan ya sanya direba na mussaman ya d'auketa a mota ya kai ta har maiduguri.
Washe garin ranar da ta tafi ta kira ni take sanar mini ta sauka lafiya kuma a daran ranar taje duba yarinyar abinda muke hasashene cikine da ita da gaske. Addu'a sosai na yi mata tare da fatan Allah Ya sauke lafiya.
Washe garin ranar da akayi addu'a bakwai din Hajiya Maryam da safe Hajja ta had'a taro. Ban fito ba saboda ina ganin kamar abin bai shafe ni ba, Hajiya saratu da kanta ta shigo har d'aki ina kwance ta ce da ni na fito zaman har da ni za a yi.
Ba kuma ta bari na ce komai ba ta juya ta fita. Babu yadda na iya haka na sanya hijabi na bi bayanta.
Maigidan yana zaune kasan kafafunta Ita da Gwaggo da inna Uwani suna saman kujera. Ganinshi a 'kasa ni ma sai na zauna kusa da shi. Gaisuwa muka 'kara yi bayan wadda na yi musu d'azu. Sai na yi k'asa da kaina falon ya d'auki shiru kafin ta fara magana. Abinda dai nake hasashe ne zaman akan lamarinsa da Hauwa ne. A ganina kamar ba ni da hurumi amma ya zame mini tilas na zauna na saurara.
Tunda nake da Hajja ban ta'ba ganin b'acin ranta mai tsanani ba irin yau. Yadda take yi masa fad'a har sai da ya d'an ba ni tausayi. Kansa a kasa cike da ladabi kuma bai katseta ba. Fadanta take yi tare da ko'karin nuna masa bai isa ya lalata zumuncin da yake tsakaninta da 'yar uwarta ba. Yadda na fahimta ita bata ji ciwon abinda Hauwa ta yi masa ba sai ciwon sakin da ya yi mata shine abinda ya fi daga mata hankali. Tana sake gaya masa cewa duk inda aka tara mata a gida dole sai an yi hakuri an kuma kawar da kai ba a yankewa mace mai juna biyu hukuncin saki. Na yi kasa'ke jikina duk a mace ashe da na gaya mata ni ma ya ta'ba sakina abinda za ta yi masa sai ya fi haka. Ha'kuri kawai yake bata. Hajiya Saratu ta sanya baki tana fad'in." Hajja a duba abinda Hauwa ta aikata a kuma yi wa kowa adalci kada ki tauyi wani daga ciki. Ban ce bashi da lefi ba yana dashi rashin hakuri da abinda ya aikata na datse igiyar aure. Amma zahiri fa Hauwa ta aikata abinda ya zama lallai a nuna mata kuskuranta, ban Fadi haka don ina 'kinta ba, yadda Tajo yake a wurina haka itama take a wurina, abinda nake ta jadadda muku anan shine Yarinyar nan ko daga waje a ka aurota wallahi duk b'acin rài bai kamaci ta aikata mana wannan wulakancin ba." Hajja idan maganata ta bata miki rai ki yi ha'kuri.
Inna Uwani a sanyaye ta furta." Kina da gaskiya Saratu kuma ni dai da bakina ba zan ce Tajo ya mayar da Hauwa ba, ai dama ni na ce masa ya aureta ya kuma bi umarnina tunda hakan take ganin ya yi mata shikkenan sai ta zauna mu yi goyayya a gida."
Gwaggo ta ce." A a Uwani ai ba za a yi haka ba, menene amfanin zaman da aka yi kenan ai domin a samu maslaha ne tabbas Hauwa ta yi kuskure amma a yi hakuri duka a kuma yi mata nasiha sosai sannan tunda akwai sauran igiyoyi babu wanda ya ji ya gani sai a mayar da auran ta dawo ta rungumi yaranta."
Falon ya d'auki shiru kafin ya yi gyaran murya a nutse ya ce." In sha Allahu rabbi Hauwa zata dawo dakinta kamar yadda Baban Saude ya zame mini sheda a wattanin baya tun kafin haihuwarta na mayar da ita furta mata ne kawai ban yi ba. Amma Hauwa tana nan a matsayin matata har yanzu, ba ni da matsala da ita a yanzu smma abinda nake so anan shine inna Uwani ki gaya mata cewa ta ajiye wad'annan halayen nata da take yi mini anan ta zo mini da sababbi. Idan har zamu cigaba da tafiya da ita a haka ba ta canza ba to matsala tabbas ba zata mutu ba. Na yi hakuri na yafe mata sannan Ina neman afuwarku akan hukuncin da na yanke idan na 'bata muku."
Inna Uwani ta fashe da kuka tana fad'in." Ni ai da cewa na yi ka kyaleta ka nemi wata kawai ka aura ita kuma sai ta auri eanda ya fi ka. Wato idan Allah ya suturta mutum jin dadin hakan sai ya fara ko'karin butulce masa amma shekarar ta nawa a kasa ba ta yi auren ba ta samu da albarkar zuri'a tana hofintar dasu. Na gode sosai Alhaji Tajuden Allah Ya yi maka albarka.
Irin kukan da take yi sai da ya sanyayyar da jikinmu gabad'aya. Sai itama Hajjan ta fara share hawaye tana fad'in." Ni ba zan ga wannan masifar da jama'a suke kiranta ba in sha Allahu zumunci ba zai b'aci ba za a yi danasani ba. Allah Ya jikan Samira."
Gabad'aya sai suka ba ni tausayi na ji cikowar kwalla a kwarmin idona na sanya hannu a dabarance na goge ina yi musu fatan alheri a raina. Tabbas na ji dadin ganin yadda lamarin ya zo da sauki lallai shaidan bai yi tasiri ba don da ya samu galaba da ba a tsayar da matsaya ba ana dambarwa gashi cikin ikon Allah an daidaita komai sshe ma tuntuni ya mayar da ita mu ne ba mu sani ba, tunda lokacin da Baban Saude ya zo ta gaya masa ya saketa a ranar ya yi mata alkawarin zata koma dakinta. Baban Saude ya taka muhimmiyar rawa sosai domin zumunci da abotarsu na tsakani da Allah ne da nuna kuskure tare da tsage gaskiya duk d'acinta. Da wani ne ganinsa millionaire wanda ya fi arziki da manya mutane sai ya ji shakka nuna masa kusuransa. Amma Baban Saude ba haka yake ba tun fil-azal mutum ne mara tsoro da shakka. Na yaba masa sosai kuma na ji dadin hakan har zuciyata.