← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 43

Sashe 18

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 5 min read

Ban ce mata komai ba domin duk bayanin da zan yi mata akan mutumin nan ba zata gane ba. Idan na ce mata shekarun baya na ta'ba yun'kurin zubarwa za ta fara wasu tunanuka marasa kyau akaina kuma bai zama lallai ta fahimci nufina ba tunda ita ai mutuniyar da ce. Akwai tauhidi tare da k'adaita Allah. Shi kam ai ko zan kwana ina rantsuwa ce wa zubewa ya yi babu wata hujja da rantsuwar da zan yi masa ya yarda kan cewa ba hada ba ki muka yi da Hauwa ba.
Hijab na zura a jikina mai fuska har kasa muka fito tare da ita tana ta jadadda maganar har zuwa lokacin Hauwa ba ta fito ba..
Kai tsaye hanyar fita na nufa ita kuma ta nufi kicin babu karsashi da kuzari a tare da ita.

Wuri ne k'ebantace ya ware a gidan domin ganawa da manyan bakinsa na mussaman. Gabad'aya wajen ya fi ko'ina kyau da tsaruwa a gidan. Masu hidima da aikin wajan su kansu na daban ne. Yadda ya sau'ki Baban Saude a sashen ya tabbatar mini da ce wa bai ajiye shi a nesa ba, suna tare domin tun bayan sulhunmu na farko na fara fahimtar abota mai karfi ta shiga tsakaninsu.
Ina dosa kofar da zan shiga falon escort dinshi Sukajiru da Emanuel sune dai amintattun nasa da basa rabo dashi mussaman ma Sukairaju da duk inda zai tafi tare suke tafiya, bayan wasu jami'ai guda uku da naga ba sa rabo da shi.
ina isa suka fara gaisheni na amsa sama-sama kafin da sauri Sukairaju ya bud'e mini k'ofar na shiga a nutse.
Suna zaune a kujera d'aya hira suke yi cikin fara da barkwanci tsakiyarsu Loptop ce ta maigidan da alama akwai abinda yake nuna masa a ciki. Center tablet din da yake tsakiyarsu kuwa sha'ke yake da manyan kuloli akwai tazara sosai tsakanina da inda suke tunda girman falon ya shahara sosai. Kafin na kàrasa gabad'aya gwiwata ta sage saboda ban san irin tozarcin da Baban Saude zai yi mini a gaban mutumin nan ba

Cikin nutsuwa na isa wajan da suke zaune na d'an rangwafa kusa dashi kafin na bude baki a nutse na ce." Baban Saude sannu da hanya, fatan duk mutan gidan suna nan lafiya ya su Dada da sauran 'yan uwa."
Ya fuskanceni sosai yana dubana da wani irin yanayin da na kasa tantance shi. Ya ce." Kowa lafiya lau Amina, Dada tana gaisheki ai dana gaya mata cewa zan zo nan wurinki har ta sanya mini rigima wai sai ta biyo ni da k'yar na zame na gudo ba ta sani ba.
Murmushi na yi wanda babu nisha'di ko na miskala zarratin cikin dusheshiyar muryarta da ta ga ji da kuka na ce." Dada kenan ai ba ta ta'ba zuwa ta ga inda nake zaune ba."
Ya sake fuskantata sosai yana fad'in." Tabbas hakane amma ai tana samun labarai a kanki masu dad'i da akasin haka."
Shiru na yi tare da yin kasa da kaina gefe guda Ina ta nazarin manyan mazuban abinci masu daukawar hankali dake jere a saman center tablet din da yake daf da su.
Cikin zuciya na dinga tunanin akan haka. Akwai masu yi masa hidima nau'i daban-daban domin sai na ce duk tsayin zama da shi wasu daga cikin yaransa ma ban san su sosai ba. Amma dai zuciyata ta fi aminta da cewa wannan aikin ba na kowa ba ne face na matarsa da ya rataya fulawar so da k'auna irin ta indiyawa. Momi ce ta yi masa wannan hidimar domin fitar da shi kunya. Ko kad'an hakan bai burge ni ba duk da cewa ta yi ne bisa bin umarinsa amma sai nake zargin babu abinda bai gaya mata ba na abinda ya shafi tsakaninmu da shi. Na sake jin wani irin nauyi da kunci a cikin raina, gabad'aya sabgar mutumin nan ta fice mini daga rai domin kuwa kansa kadai ya sani bai da adalci ko kad'an.

"Ina ita abokiyar zaman naki ai tare nake so na zauna da ku domin tattauna masla'ar da ta kawo gidanki Amina."
Wannan maganar ita ta datse tunanin da na lula na daga kaina cikin kasala da zullumi amma abin da ya ba ni mamaki bai wuce ganin idanuwansa a kaina ba gabad'aya ma hankalinshi na kan 'kafafuna. Har cikin raina kallon ya ta'ba ni domin irin na mutukar 'kurrula ne, nan da nan na fahimci abinda ya assasa hakan bai wuce lallen da ya fito ya zanu radau a kafafuna ba. Da sauri na gyara zaman da na yi na mayar dashi zaman rakuma kafafun suka koma can baya ganin haka ya sanya shi da sauri ya janye idonsa tunda ya fahimci na gan shi sai ya cigaba da duba Loptop din dake gabansa bai ce mana komai ba yana jin Baban Saude yana tambaya Hauwa na kasa ba shi amsa domin kuwa ba na so ko da wasa sunanta ya fito a cikin sha'anina. Hauwa ba ta da wani lefi magani ta ba ni a amtsayinta na ma'aikaciyar lafiya bai yiwuwa saboda yana jin haushinta ya jingina mata lefin da ba ta da hurumi a ciki.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 111
Ya sake maimaita tambayarsa. Sai kawai na rushe da kuka mai tafe da gunji na ce." Baban Saude ita Hauwa ina ruwanta, kowa rai ya yi dad'i ai barin mai shine kuma ai idan d'an adam yana rayuwa a duniyar nan dole sai ya hadu da jarrabawa iri-iri."
Shiru ya yi kawai yana kallona cike da mamakin ganin irin kukan da nake sharba kuma mai tafe da jan majina da shashsheka. Yanayinsa ya d'an nuna sanyi da sasaauci, ganin haka ya sanya na cigaba da rerawa da babban sauti Ina yi ina jan hanci. Wajan in banda sautin kukana babu abinda yake tashi. Baban Saude kawai ya zuba mini ido, shi kuma wanda ya assasa zaman kansa yana dukufe a computr kanzil bai ce mana ba."
Chapter 18 · 0% Book details