← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 43

Sashe 23

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read

Shiru ya d'an ratsa wurin kafin ya nisa ya sake ce wa." Yanzu nawa ki ke ganin zamu ba su gudumawa ni dake?" A takaice na furta." Duk abinda Allah Ya hore maka."
"Ai shawara na tambayeki ni Allah Ya hore mini tuntuni. Kawai ki gaya mini abinda za a ba su ai auran fari za su yi."
Na kalle shi babu sukuni na furta." Ya za a yi na yanke maka abinda za ka bayar, ai ba kudina ba ne, naka ne, kuma dai daidai gwargwado sun yi hidimarsu ni ma kuma tuntuni na tura mata da tawa gudumarwar abinda ka ga dama shi za ka ba su."
Ya gyada kansa yana fad'in." Ok na ba su 5m ya yi ko?"
"Idan haka ka yi niyya ni ina ruwana?" Na fad'a tare da d'auke kaina domin har ga Allah zuciyata zafi take yi mini game da irin mummunan fatan da ya gama yi mini yanzu.
Ya ce." Kada ki gaya mini magana Amina, ba na son rashin kunya da fitsara ko kin ga na ta'ba jikinki ne, kin ga alamar sha'awarki a kwayar idona, Ina ce wannan shine yake kawo mini raini a wurinki to ki ri'ke kayanki ba na so."
Na fashe da kuka tare da cewa." To ai dama ban ce ka nemi shawarata ba ni ma, kuma ban ce ka neme ni ba, abinda ka yi niyya shi za ka yi, ni ma abinda na yi niyya shi zan yi, aljanna dai kuma babu wani bawan da yake bada ita ta Allah ce, ta hanyoyin alheri ana samunta ba sai ta dalilin wani ba."
"Na ji abinda ki ka ce ta shi ki tafi."
Na tashi haka kawai na tsinci kaina da buga siket din da yake jikina na kama hanyar fita raina a masifar kuntacce.
Ban sauka ba tukkuna sai da na daidaita yanayina na sauka na same su suna nan a wurin suna hira Hauwa hannunta ri'ke da apple tana ci babu abinda ya dame ta sai addu'a da ko'karin rabuwa da cikin jikinta lafiya.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: *114*
Ban zauna falon ba kai tsaye d'akina na nufa na yi zaune zugum a gefan gado zuciyata na ta yi mini sa'ke-sa'ke masu kyau da marasa kyau! Lallai cikin wannan duniya babu komai face rikici da tarin kalubale.
Babu yadda ban yi ba da Hauwa akan ta shirya bayan magriba mu shiga mu duba Momi amma fafur taki tace itama abar dubawa ce domin kuwa bata kaita jin jiki ba. Ganin taki fahimtata ya sanya na kyaleta kawai muka shirya da Baba Tabawa muka tafi dubanta.
A harabar gidan muka riski Salim da Adam a tsaye suna magana. Da sauri shi babban ya d'auke kansa yayin da karamin ya sassauta a nutse ya dube mu da ladabi yake fad'in." Mama ku ne."
Na ce." E, mune Adam mun shigo duba Momi ne. Sai ya yi yar dariya wadda babu annashuwa a cikinta ya furta." To shikkenan mu je na yi muku jagora."
Gaba ya yi muka bi bayan shi yayin da Salim din yake ta ciccin magani har da jan tsaki. Murmushi kawai na yi a zuciyata gabad'aya yaron ma ni tausayi yake ba ni, domin kuwa ya d'auki lamarin da zafin gaske.
Falo muka zauna ya nufi bedroom din ta yana fad'in ."Bari na sanar da ita." Ba mu kai minti biyar da zama ba daya daga cikin masu aikinta ta fito daga kicin da wata madaidaiciyar roba a hannunta Hassana da Minal suna biye da ita. Ganinmu a zaune ya sanya yaran suka tsaya. Ita kuma mai aikin ta karaso wurin da muke har sai da ta risina kafin ta gaishe mu gabad'aya.

Ina kallon yadda Baba Tabawa take jan yaran da wasa da tsokana amma suna can nesa da mu sun tsaya suna ta kallonmu kamar sun ga dodanni. Raina ya 'baci nan take zuciyata ta dinga raya mini abubuwa marasa kyau to idan ba an zauna da yaran an fadi wata magana ba mai zai sanya k'ananun yara irin wad'annan su dinga yi mini wani irin kallo. Abin b'akinciki da takaici ma har da 'yar cikina 'kiri-'kiri saboda kin gaskiya.
Idona na zare musu sosai na ce." Tsayuwar ta mecece idan ba za ku gaishemu ba to ku daina kallonmu, ko mun yi kama da tibi ne.''
Matashiyar mai aikin da take jigila da su tana dariya ta furta." Ke Hassana ku zo ku gaisa mama ce fa."
Na ce." A'a rabu da ita kada ta zo mu gaisa ta tsaya." Usaina ta fito daga kicin da shafciciyar wuka a hannunta tana fad'in." Mairo ga wukar ki yanka mana." Shiru ta yi tana kallonmu yayin da mai aikin ta je ta da sauri ta kar'bi wukar tana fad'in." A can sama fa na d'orata yanzu Usai sai da ya d'aukota."
Ba ta ce mata komai ba ta nufo wurin da muke zaune tana zuwa sai ta dora kanta a cinyata tare da zura yatsanta babba a baki tana tsotsa. Na yi shiru ina sauke ajiyar zuciya yayin da na d'ora hannuna a saman kanta.
Ganin haka ya sanya Hassana da sauri itama ta zo ta yi yadda Usainar ta yi dama tuntuni Kamalu ya gaya mini kishi ne da su, duk abinda daya tayi to babu shakka yar uwata ma sai ta yi. Da hannu na yi wa Minal alama ta zo wurina. Ta kuwa taho kataf-kataf domin yanzu itace take tashen ki'ba a cikinsu. Na ri'keta sosai Ina fad'in." Ina Khalil yake?" Cikin yanayin maganarta ta furta." yana can gidan anti Nusaiba."
Baba Tabawa sai murmushi take yi tana jan su da wasa. Hassana da Usaina iyayen miskilanci ne, Minal din ta fi su sakin fuska da son mutane. Tunda suka dora kawunansu saman cinyata babu wadda ta dago sai da suka ji muryar Babansu tukkuna.
Tare suka fito da Momin kallo daya na yi mata gabobin jikina suka shika wata irin rama ta yi mai ban tsoro kanta yana nema ya rinjayi gangar jikinta abinka dama da siririya idanuwanta sun yi kuru-kuru ta d'ashe kwarai da gaske ta yi fau, babu shakka babu karya a cikin lalurarta yadda mijinta ya dinga jadadda ciwon ya ci karfinta yanzu na sake gazgata kammaninta duka sun canza ta hadu da ciwuka masu hatsarin gaske sugar da hawan jini.
Ta zauna tare da taimakonsa suka zauna kujera d'aya yana dan gaya mata kafafunta ko daga inda nake zaune Ina kallon yadda jikinta yake rawa.
Ban ji haushinsa ba ko kad'an domin a yanzu dai babu maganar kishi ga matar da take cikin irin wannan yanayin na halin ciwo mai tsanani. Ta dinga fara'a a zahiri tana nuna jin dadinta. Muka gaisa cikin kulawa da mutunci. Na yi mata sannu da jiki haka zalika ma baba Tabawa ta dubata sosai. Ta dinga dariya ganin yadda twin's suka yi mini farincikinta ya kasa 'boyuwa tun kafin mu yi sallama take yi mini godiya har sai da jikina ya mutu tsabar tausayin halin da take ciki. Mairo ita ta janye yaran ta tafi dasu tana yayyanka masu mangwaron da tun farkon shigowarmu suke rigima a kansa.
Duk abinda muke yi bai ce mana komai ba, mun dai gaisa amma tun bayan gaisuwar bai sake magana ba, sa'i da lokaci dai yakan amsa waya idan an kira shi.
Misalin takwas da wani abu muka fito daga gidan tun a hanya muke alhinin yanayin da muka risketa baba Tabawa dai kasa daurewa ta yi a hanyarmu ta shiga gida ta fashe da kuka da sauri tasa gefan jihabinta ta rufe fuskarta . To ni ma dai kukan zucci nake yi domin na shiga rud'ani ba karami ba ganin yadda Allah Ya mayar da baiwarsa. Idan kudi na sayan lafiya nasan da ba wannan maganar ake yi ba. Wannan da duniya ta yi mata sheda cewa mutuniyar kirki ce wadda tun a duniya mijinta ya ce ya yafe mata itace cikin irin wannan yanayi to ina ga wanda ya shure umarnin Ubangiji kuma, Ubangiji Allah kasa mu dace Amin.
A haka muka shiga gidan Hauwa na kwance saman kujera 3str tana kallo abinta. Ganinmu sukuku ya sanya ta tashi zaune tana tambayar lafiya.
A takaice na ce." Lafiya lau." Na shige d'aki domin yadda kafafuna ke rawa ba zan iya tsayuwa a wurin ba. Na zauna gefan gado tare da rafka tagumi wani abu ne ya zo ya tsaya mini a wuya na tsananin fargaba da tashin hankali mace ta koma sai kace mai cutar kanjamau! ko mai farfadiya sai an rirriketa. Hawaye suka fara sauka a kumatuna. Haka kawai na ji duniyar ta fice mini daga raina gabad'aya.
Shigowarta ya sanya na daga kaina na dube ta. Ta zauna gefana babu babu fallasa ta ce." Ashe kema kukan ki ke yi Amina." Sai ta sa dariya kafin ta cigaba da cewa." Ga Baba Tabawa can ma tana yin nata, ni kam matar nan ko dame take yawo wallahil-azim kurwata tafi tata d'aci, wallahi ni zan yi maganinta."
Na gyada kaina ina ko'karin ture kutittiran abinda ya tsaya mini a wuya na ce." Hauwa k'ullaci da tsananta gaba da kiyayya wallahi babu inda zai kai ki sai tashar dana sani. Matar nan dai duk rashin Imanin mutum yaga halin da take ciki sai ya tausayata mata don Allah mu dinga sassautawa kanmu Hauwa."
Ta ja tsaki tare da furta."lalura fa kowa yin ta yake yi, wallahi na fita jin jiki, ni mai yasa ban lanjare ba, saboda ba ni da hakkin kowa a kaina, ita kuwa bari na gaya miki abinda ta shuka ne take girba tun a duniya hakkin mutane ne wallahi."
Chapter 23 · 0% Book details