Sashe 25
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read
Sai kawai na saki bakina ina kallonta har ta fice daga d'akin ban d'auke idona ba. Na jima a zaune Ina tufkewa da warware kafin na tashi jiki a sabule na shiga bandaki domin watsa ruwa a jikina. Gabad'aya cikina ya cushe babu dandano a bakina ko kad'an yunwar ma sam ba na jin ta, daga zarar na tuna halin da muka riski matar nan a ciki sai hankalina ya tashi. A haka na shirya cikin kayan bacci ina tsaye gaban madubi ina busar da gashin kaina. Ya turo kofar d'akin ya shigo. Ban yi zaton shigowarsa ba. Muka had'a Ido ya nufo wurin da nake tsaye daf da ni ya tsaya na gama abinda nake yi yana ta kallona ta madubi na juyo kirjinmu ya hadu waje daya. Kusan a tare muka sauke ajiyar zuciya. Ya riko hannuna muka zauna gefan gado. Yanayin fuskarsa kadai shi ya nuna mini cewar ya ji dadin abinda na yi. Ya furta." Kin kyauta sosai kuma na ji dadin abinda ki ka yi, idan haka kuke yi mini kara akan abinda nake so mai zai sanya ni ma na 'bata muku ai babu abinda ya fi zaman lafiya dadi ko." Kanzil ban ce masa ba. amma maganarsa ta d'an dake ni wato shi baya jin nauyin gaya mana irin son da yake yi wa matar nan tasa. Ya d'ora hannunsa a tudun kirjina wanda tun zaman da muke yi a wurin hankalinsa yake kai. Ya nisa kafin a kasalance ya furta." Momi ba ta da lafiya Amina cikinta da wajenta wallahi." A nutse na furta." Allah Ya yaye mata, da sauran al'ummar musulmi." Ya amsa da Amin kafin ya dora da cewar." Kin san yanzu wani result din ya sake fitowa bayan gwajin da aka yi mata satin da ya wuce cancer mahaifa." Da saurin gaske na dube shi. Ya gyada kansa "Wallahi ni kaina na kadu Amina na tausaya mata k'warai da aniya yanzu haka za mu yi booking domin zuwa india akwai kwararrun likitoci a can da za su caje mini ita sosai." Jiki a masifar sanyaye na furta." Tabbas Ubangiji shi yake saukar da ciwo ya kuma saukar da maganinsa, ina yi mata fatan alheri tare da addu'ar samun lafiya madawamiya, kai kuma Allah Ya baka ladan jinya." Ya sake amsa da "Amin Ya Allah." D'akin ya d'auki shiru har yanzu hannunsa na saman kirjina yana dan tattabawa. Ban hana shi ba kawai dai ina mamakinsa ne a ganina yanayin alhinin da yake ciki da damuwa akan rashin lafiyar maidakinsa bai kamata a ce wani sbu na jin dad'in duniya yana bijiro masa ba, to mai ma zai fahimta bayan yana cikin tashin hankali a haukana fa kenan Na dube shi yana lumshe idonsa kamar wanda ya samu audiga na dan ture hannun nasa muka kalli juna a sarke na ce." Dama ina son magana da kai." Kai tsaye ya furta." Idan har akan zuwa maiduguri ne to kada ki bata bakinki babu inda zakije." Na ce." To saboda me, kafi kowa sanin matsayin anti Yagana a wurina ko?" Ya gyada kansa a tsanake ya ce." Da dai ban rantse ba ne sai na bari ki je, amma wallahi na riga na rantse ki yi hakuri bayan bikin sai ki je ki ga d'akin amarya." Zuciyata ta dinga tiriri na dinga danne abinda yake yun'kuro mini domin ba ni son na nuna masa damuwata a kan haka a gaba ya samu abinda zai kuntata mini idan wata matsalar ta faru a tsakaninmu. Na gyada kaina tare da furta." Shikkenan mu ajiye wannan maganar ina so ka gaya mini matsayin zamanka da Hauwa a gidan nan, domin ni har yanzu na kasa gane abinda kuke nufi da kai da ita." Ya dube ni sosai kafin ya ce." Ke ina ruwanki kuma?" Na ce." Ni ce kuwa nake da ruwa tunda duk wata mas'ala da kuka samu da kai da ita a kaina ne, yanzu a matsayinka na babba mai hankali da jagoranci abinda kuke aikatawa daidai ne." Ya ce." Ai taki ta amince da cewar ta yi lefi, sannan taki ta bi umarinina idan tana so magana ta shige mai yasa bata biyo ki zuwa duba Momi ba. Ta cigaba da zama a haka duk ranar da ta gaji sai ta nemawa kanta mafita." "Gaskiya hakan ba daidai ba." Ya 'bata rai yana fad'in." To nuna mini daidai Amina." Shiru na yi ban sake magana ba. Ya ja tsaki yana fad'in." Na yabe ki sallah za ki kasa alwala, Hauwa ai ba yarinya ba ce idan tana son zama da ni ta ba ni ha'kuri ta Kuma bi umarina." Na ce." To ai kaine babba ha'kurinka shine zai fi rinjaye." "Na yi iya wanda naga zan iya yi a kanta Amina, wannan ya zama na farko ya kuma zama na karshe, kada ki sake titsiyeni akan lamarin Hauwa ko ni din sa'anki ne?" Shiru kawai na yi Ina kallonsa. Ya cigaba da ce wa." Dangane da maganar kwanan aure kin ga Momi bata da lafiya ya kike ganin za a yi?" Na ce." Yadda muke yi mana." Sai ya yi shiru yana tunani kafin daga bisani ya furta." Shikkenan sai a cigaba da tafiya a hakan, zan kwana biyu ban koma legos ba, domin idan na kai ta asibitin na dawo zan dan jinyaceta." Uffan ban ce masa ba, ya tashi tsaye yana kallona cikin sigar kulawa ya furta." Ki same ni a sama zan shiga in yi wanka." Ban iya ce masa komai ba har ya fita daga d'akin Ina zaune zuciyata ta kasa tsayuwa wuri d'aya. A daran na gurzu a hannunsa kwarai da gaske kamar wata sabuwar amarya sai da na yi ruwan d'umi domin kusan sau uku ya yi mu'amula da ni. Farkon dare da asuba bayan ya dawo daga sallah. Still Yana gama breakfast nan ma ya sake yin wani haka na sauko daga saman a galabaice. Na yini ciye ciyen kayan da zasu saukar mini da ni'ima domin na tabbatar da cewar a wannan daran ma ba zai daga mini kafa ba. Bayan kwanaki shida mun d'an samu daidaito kad'an. A lokacin kuma sun gama shiryin tafiyar da za su yi. Har gida ya yi mata jagora domin ta yi masa sallama. Zamanta ke da wuya Hauwa ta yun'kura ta tashi ta shige dakinta. Hakan kuwa bai yi mata dad'i ba, amma dai ba ta ce komai ba, muka d'an ta'ba hira sama-sama kafin ya sauko daga saman suka fita tare. Sosai na yi mata addu'a da fatan alheri ta dinga godiya da murmushin nan nata wanda duk rintsi baya ta'ba d'aukewa daga saman fuskarta..... [12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: *115* Bayan tafiyarsu da kwana ashirin da shida Hauwa ta haihu. Cikin ikon Allah ta haifi d'anta namiji kama da ubanshi har ta 'baci duk abinda ya kamaci ta yi wa kanta ta yi tunda haihuwar gida ta yi kuma lafiya lau ita da yaron da ta haifa, a matsayinta na ma'aikaciyar lafiya taimakon da muka yi mata kad'an ne. Sai bayan da muka samu nutsuwa gabad'ayanmu ni da tukkuna na nemi maigidan da yake koda suka tafi ba kasafai yake kiran waya ba sai dai mu had'u ta whasap to baya jurar typing sai da vedio call. Sai na ajiye masa sa'ko ta whasap din tare da hoton yaron nasan daga zarar ya hau zai gani. Ina idar da sallar la'asar na bud'eta sakonshi ya shigo yana online din muka sake gaisawa na tambaye shi mai jiki ya ba ni amsa mai dadi jiki yayi kyau domin a karshen watan da muke ciki ma za su dawo domin an d'orata akan maganguna kuma alhamdulillahi an samu cigaba.Sai ya d'ora da fad'in na yi wa yaron hud'uba da sunan Ahmadu domin shine sunan da ya rad'a masa. Rashin abin cewa ya sanya ni yi masa shiru kawai domin tunda Hauwa ta haihu take kiran yaron da sunan mahaifinta wato Ishak, ban san kuma mai zan ce mata ba gaskiyar magana kenan. Ganin na yi shiru ban ce komai ba ya sanya shi kiran sunana na kalle shi tunda bidiyo call ne ya furta." Ko akwai wata matsala ne domin na karanci damuwa a cikin kwayar Idonki." Na girgiza kaina a nutse na ce." Babu matsala amma gaskiya ba zan iya gaya Hauwa ga abinda ka yanke ba, mai zai hana kai ka gaya mata naga tare kuka samar da yaron nan ku biyu mai zai sanya ni ka saka ni a tsakiya. Hauwa tunda ta haihu take kiran yaron nan da sunan babanta, to ni mai kake so na ce kuma." Ya yi shiru yana kallona kafin daga bisani ya ce." Shikkenan zan gaya mata hukuncin dana yanke hakan ya yi ko." Na gyada kaina ina fad'in." Ya yi shine daidai sai ku tsyar da matsaya a tsakaninku, Allah Ya raya mana shi." Ya amsa da "Amin. Yana mai zuba mini ido." Ni ma na zuba masa nawa idon nan na fahimci canzawar da ya yi har da wani kumatu fatar nan ta sake yin fresh duk da bidiyo call yana sanya mutum muni da duhu to shi ban ga hakan ba, kamar ba wanda ya tafi jinyya ba ya yi kama da ango wanda ya tafi yawan sha'katawa da amaryarsa. Ajiyar zuciya na sauke yayin da nake ko'karin kawar da abinda na ji yana yun'kuro mini a game dashi na ce." Na canza kammanni ne Allah Ya taimaka ka." Sai ya rausayar da kansa yana ce wa." Sosai kuwa, wata na gani anan asibitin da muke mai kama dake duk sanda na yi ido hud'u da ita sai hankalina ya tashi wallahi yanzu ina cikin tsananin damuwa na yi missing d'inki my wife." Na dan bata rai tare da cewa." Matar kuma idan tana da aure fa, kana raya abun da bai dace ba akan matar wani daidai kenan a wurinka." Kansa ya girgiza kamar karamin yaro ya furta." Ba daidai ba ne, amma ba na tsammanin ai tana da aure budurwa ce, wallahi ba zan munafurceki ba Amina ba na iya d'auke kaina daga kanta domin yanayin hallitar jikinku daya 'yar duma-duma ce mai yawaltaccen kirji da tudun mazaunai." Dariya maganar ta ba ni na danne ban yi ba domin ganin abin nasa yana