Sashe 37
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 9 min read
***
To alhamdulillahi cikin ikon Allah kwana daya da dawowar Hauwa na fahimci sun samu daidaito a tsakaninsu, na ji dad'in hakan sosai kuma na jinjina mata domin ta yi kokari kwarai da aniya wurin ganin ta sassauto da zuciyarsa a lokaci k'ankani ba tare da an jima suna kai ruwa rana ba.
Sannu a hankali muka cigaba da gudanar da rayuwarmu cikin rufin asiri da kulawa. Mun ajiye wani abu wai shi kishi muna mutuntuna junanmu tare da bawa juna shawarwari masu kyau. Maganar maigidan kuwa duka mun fahimci halayensa dai tunda namiji ne wahainiya ne mai rikida a koyaushe wata'kila akwai wasu darrusan da bai gama fahimtar da mu ba. Yana dai ko'karin bawa kowacce hakkinta kwana bibbiyu muke yi abinda na sani shine a cikin kwanakina biyun nan yana bani hakkina na aure don bai ta'ba tsallake rana daya ba sai ya neme ni. To Ina kyautata zaton ta bangaran Hauwan ma hakane tunda gaskiya ban ta'ba ganin wani canji ko jin haushi a ranar girkinta ba.
Yara kuma muna yin daidai gwargwado da kiyayewa don ma rabin zaman nasu a skull ne sai ranakun hutu tukkuna muke yini tare Kuma sun fi sakin jiki da Mairo. Minal ce mai nacin zuwa wurina tunda dama tun fil'azal mun saba kuma ba ta da rashin son mutane irin na su Hassana.
Na kan tambaye shi su Salim a wasu lukutan ya ba ni amsa suna lafiya. Bai ta'ba cewa mu shiga mu duba su ba, kuma bai ta'ba turo mana su ba. Sai idan Khalil ya je can gidan nasu a wasu lukutan Adam yake ba shi sakon gaisuwa zuwa gare mu.
Ya dai gaya mini idan zai koma legos tare da Salim za su tafi zai d'ora shi akan wasu harkokin nasa. Ya nuna masa yadda zai kafa kansa nan gaba. Na yi addu'a sosai da fatan alheri.
***
Watarana ina duba status kamar almara naga nambar Nabila wadda sama da shekara da wattani ta yi blocking dina tun lokacin rigimarsu da Hauwa dama kuma can jefe jefi nake ganinta to tun daga sannan ban kara ganinta ba sai yau tunda dama ni already Ina da lambarta ban goge ba.
Kamar wadda aka tankwabewa hannu na shiga status din ina dubawa. Tsala-tsala hotonanta ne ta yi kyau kwarai babu karya tunda suna da gadon haske da kuma boko da gayu sai da ita Nabila har ta fi Momi wayewa irin ta duniyanci kar take. Na duba kasan wani status din da ta yi ta rubuta (Mrs Tajo Dambatta to be in sha Allahu 💕) da manyan harafi. Gabana ya yi wata iriyar bugawa mai tsananin gaske. Hannuna na rawa na shiga next status din da ya zama na karshe shi kuma ta rubuta (Mun zama kujera. Ni kuma warki ce daidai 'kugun kowane shege. Zan shigo za mu zuba shege ka fasa dan halak sai yanka")
[12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: 121
"Ni warki ce daidai da kugun kowane shege." Wannan magana ta Nabila itace ta fi tsaya mini a raina. Na kuma zauna a tsanake na fara yin nazari akanta. Idan har maigidan nan zai auri Nabila a yadda na d'auki duniya a yanzu ba komai ba ce ai a ganina ba abin damuwa ba ne. Matsalar anan shine yadda salon yake nema ya canza. Ni da Hauwa a yanzu babu wata 'baraka a tsakaninmu mun zamewa juna 'yan uwa domin duk wani kishi da jin haushin juna mun ajiye shi a gefe. Mun had'e kan yaranmu gabad'aya muna taimakon juna. Idan da gaske ne zai auri Nabila alwashi da irin shirin da take yi akan shigowarta zai haifar da d'a mai ido kuwa. Ya zama dole a wannan ga'bar na taunawa mutumin nan tsakuwa ba don komai ba sai don dakushe shi daga barin irin ibtila'in da yake ko'karin d'auko mana. Idan har babu mugun nufi ko mugunta a sha'anin Nabila babu wata damuwa fa ni dai a bangarena ya aureta ta maye gurbin 'yar uwarta. Amma wannan rubuce-rubucen nata ya sanya ni a cikin shakku tare da 'kyamatar lamarin. Idan har aure yake so ya kara ba zamu hana shi ba amma fa banda Nabila wannan shine magana ta gaskiya.
Ko Hauwa ban gayawa ba na ja bakina na yi shiru har sai dai girki ya dawo hannuna tukkuna. Duk wasu sabgogi da nake masa ban fasa ba. Kwalliya ma na yi sosai irin wadda na jima ban yi masa irinta ba. Ya kuwa dinga washe baki yana nan nan da ni. Har da su zolaya wai na yi kama da sauraniya. Na ce masa ai itace amma ta birnin zuciyarka. Ya kamo ni ya makale a jikinsa yana abinda ya saba. Na tashi ina gyara daurin dankwalina da ya tuje ya sake cakumoni Yana fad'in." Benu ba kya tsufa sai dai ki yi girgiza ki dawo sabuwa dal. Da gaske fa kamar amarya."
Maganarsa ta yi daidai akan ga'ba.
Na gyada kaina da d'an murmushi ina dubansa gabad'aya duk ya burkice a bukace yake alamu duka sun nuna.
Na ce." Haka ake amarya Allah Ya taimaka amaryarka dai tana nan tafe ko ka dauka ban samu labari ba."
Ya yi kasa'ke yana kallona kafin ya ce." Ban gane abinda kike nufi ba.
Babu yabo babu fallasa na ce." Nabila fa."
Ya tsira mini ido yana kallo. Na yi murmushin takaici a hankali na ce." An kusa daura auran ne?"
Tsaki ya ja kafin ya ce." Ba na son shirme ke ba kya son zaman lafiya Amina."
Na furta." Ka fito fili ga gaya mini gaskiya domin rufewar ba ta da amfani.
Ya ce." Akan me zan boye muku neman aure Amina, ke a Ina ki ka samu labarin ina zawarcin Nabila?"
Kai tsaye na ce." A wurinta mana!"
Ya maimaita maganata "A wurinta?" Da sigar mamaki a tare dashi."
Na ce." Wallahi kam kasan ina da lambarta jiya naga ta yi status da hotonta ta rubuta matar Tajo mai zuwa har tana had'awa da zaginmu ni da Hauwa."
Sosai ya shiga mamaki kafin ya ce." Ni kam babu soyayya a tsakanina da ita. Ai ba na tsammanin zan sake auran bazawara Amina kishina ba zai barni ba balle ita da bata da alkibula ta yi nan ta yi can da sunan neman kudi gari gari. Matata da ta rasu Hajiya Maryam ita daban take gaskiya kuma ita din rainon abokina ne shiyasa ban yi kokwanto wurin auranta ba.
Na ce." Wannan cin fuska ne a fakaice fa menene illar zawarawa ai ba duka aka taru aka zama daya ba. Ni kenan kawai don ba yadda za ka yi dani ne ko?"
"Ban fad'a ba, tunda ki ka ga Ina zaune dake ai kina da matsayi a zuciyata don haka mu rufe wannan maganar ba na neman tashin hankali."
Na ce." Magana kam ba za ta rufu ba, don gaskiya ba zan yadda da cewa babu ala'ka ta soyayya a tsakaninka da Nabila ba, gaskiya kawai za ka gaya mini."
Ya 'bata rai ainun yana fad'in." Makaryaci ne ni kenan, Amina kin yi bala'in raina ni wallahi ke yanzu ba ki ji kunya ba dattijo Irina da furfura biyabiya a fuskata ki dinga titsiyeni har ki na cewa karya nake yi. Ko ban haife ki ba na kusa da na yi aure da wuri."
Na ce.'' Yaushe ka ji na kira ka da makaryaci ni ban fad'a ba, kawai na ce ka gaya mana gaskiya kada ka boye domin hakan ba zai haifar da d'a mai ido ba."
Ya ce." To iya gaskiyar kenan na gaya miki babu komai a tsakanina da yarinyar nan ko aure zan yi ni budurwa zan aure matashiya mai jini a jika."
Shiru na yi ban ce komai ba amma zahiri maganar ta ta'ba mini zuciya mu kenan mun tsufa ba mu da jini a jika komai ya dakushe. Ai sharrin rijalu kenan.
Cikin takaici na ce." Ai gasu nan masu jini a jikan suna yawo a gari sai dai can wurin da kuke kwakwa bai zama lallai ku same shi a rufe ba. Domin su da kansu suke bud'e kayansu. Ko kuma gayu su bud'e muku hanya ku kuma dattijai makwadaita ku kwaso kuna rawar jiki."
Ya ce." Ai muna da nagartattu a dambatta sai na sanya Hajja ta bincika mini mara waye wa."
Na ce." To Allah Ya ba da sa'a." Daga haka na yun'kura domin tashi na fita.. sai ta riko hannuna na koma na zauna d'abas! Takaicin hakan ya sanya ni rushewa da kuka. Ya tallafo ni da saurin gaske yana rawar jiki. Na daddage da k'arfi na fizge. Na kama hanya na fice daga d'akin ina goge fuskata.
Kwanakin girkina suka fita muna ta rigima domin zahirin gaskiya raina ya baci da maganganun da ya furta mini. Yanzu a yadda yake sai iya auro 'yar sha shida a ganina mai zai tsinta a jikinta. Wannan wulakanci ne kawai.
Hauwa ta sake kar'bar girki ta fita na kar'ba duka raina babu dadi kuma ban gaya mata halin da ake ciki ba saboda ba na so na hada ta da mijinta duk haukan kishina ta fi ni. Nasan rigima ce za ta tashi idan ta ji cewar neman auran Nabila duk da babu tabbas amma ai har yanzu ba ta daina yin status tana dorawa da sunanta da nasa a hade ba.
Ya dinga bina yana rarrashi na bashi kaina domin samun hadin kaina shine zai karawa lamarin armashi irin wannan sabgar idan ana jin haushin juna bata dadi.
Da wannan hanyar kawai nake gasa shi kuma nan da nan yake saduda ya nuna rauni da damuwa. Ni kaina nasan na tsaye masa a zuciya domin bai yi fiye yin annashuwa ba muddin muka yi fad'a fara'arsa k'alilan ce. Amma idan muna shiri mussaman ranar girkina Yana kasancewa cikin nishadi da walwala.
Mun fi sati biyu a haka ga dai Hauwa nan ai yana kwana da ita idan hakane ta d'auke masa duk fitinarsa mana. Kana amfanuwa da mace kana fito da sabbabin iskanci kala-kala.
Ya rintsa ni a d'akina misalin sha biyu da wani abu. Girkina ne amma tunda na kai masa abinci na sauko ban kara hawa ba. Da rantsuwarsa da komai yake gaya mini babu maganar auran Nabila ya miko mini wayoyinsa yana fad'in." Ki bincike wayata tsaf idan kin ga lambarta ki hukuta ni."
Na ta'be bakina ban ce komai ba, kuma ban kar'bi wayar ba. Ya nanike ni sosai yana nuna mini inda lambobin mutane suke yana fad'in." Kin gani ko ki duba ki ga ni, ni me zan yi da wannan yarinyar ne Amina."
Na gyada kaina a tsanake na ce." Ita ai tana da abinda za ta yi da kai, ko baka sonta na tabbatar da cewa ita tana sonka."
Na d'auki wayata dake saman dirowar gefan gado na lalabi status dinta na yau ina nuna masa hotonta wanda ta cakare ta yi gayu kwarai da gaske kasan hoton ta rubuta (Amaryar Tajuden I. Dambatta)
Ya jima yana kallon hoton wayar a hannuna kafin ya ce." Wannan bata ta da tunani Amina Allah Ya kyauta amma zan ja mata kunne idan ma tana yin hakane domin ta hargitsa mini iyali."
Ban ce komai ba na kashe wayar tare da ajiyeta Ina kallonsa gabad'aya yanayinsa ya canza ya yi zuru-zuru kamar b'arawo a masallaci. Dariyar zucci na yi kawai na kawar da kaina. Ya cigaba da binbini da kalamai sai kace maroki ina jinsa ban ce komai ba. Ya d'ora hannunsa saman cinyata tare da sake matsowa. Na sauke ajiyar zuciya kamshin jikinsa ya sake saukar mini da kasala. Ya d'an tura ni na kwanta saman gado sai ya hayo sosai ya yi mini rumfa tare da hade yatsunmu wuri d'aya ya d'ora bakinsa a saitin wuyana ya saki wani goron numfashi kamar irin na macen da take dabda haihuwa.