← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 43

Sashe 19

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read

"Ashe kenan ba ni da hurumi ko ban kai abokiyar zamanki ta taso ta gaishe ni ba kenan Amina, ai ni tambayarki ita kawai na yi na ce da ke ina take ai ita din ma 'yata ce kamar ke din ko ba haka ba ne."
Na gyada kaina tare da sanya hannu na ja hanci cikin reshin kuka na ce." To Baban Saude ai ban san me ya gaya maka game da mu ba. Shine dalilin da ya sanya ka ji na ce haka, idan har ba zai iya yadda da kaddara da abinda Allah Ya shiryo ba ai bai kamata ya na hada ni dak.....Ban kàrasa ba ya buga hannun kujerar da yake zauna ya furta." Me ki ka ji na ce miki Amina, wato a gabana din ma kaifin harshe za ki yi, idan shi kin raina shi saboda kuna kwanciya a shimfida da d'aya ai ni ya wuce a ce ki yi mini jayayya bisa umarnina, shin wai ko kin manta wanene a gabanki ne."
Shiru na yi gabana na bugawa da karfi da karfi, don sasasucin dana hanga a fuskarsa ya 'bace bat ya dawo asalin baban Saude mafada ci.
"Idan na isa ki tashi ki je ki kira wo mini ita."
Ya fad'a cikin sigar bada umarni.
Ban ce komai ba na tashi na kama hanyar fita kafafuna kamar an doke mini da tabarya. Allah Ya yi wa Baban Saude wani irin kwarjina da haiba da wata baiwa wadda idan ya yi magana ko babu fad'a a ciki sai mutum ya nutsu. Yanayinsu daya da jarumin film din nan na Hausa (Tahir fagge)
Ina shiga d'akin na sameta ta yi wanka tana cin indomin da Baba ta dafa mata
Ganin yadda na shigo ya sanya ta tsira mini ido har na isa wurin da take zaune. Kafin na furta komai ta riga ni ta hanyar fad'in." Lafiya na ga idonki a kumbure ko mutuwa aka yi ne ban sani ba ina ta baccin asara.''
Na girgiza kaina tare da fad'in." Babu wanda ya mutu Hauwa mijinki ne ya kai kararmu wurin Baban Saude."
Ta yi shiru tana maimata sunan baban Saude kafin ta furta." Oh Yayan mamanku na maiduri ko?"
Na ce." Shi fa, bai jima da sauka ba, yana can sashensa na baki ya ce na kira wo ki muje tare.
Karamin tsaki ta ja kafin ta ce." To akan me Amina ba ki gaya masa cewa zaman idda nake yi ba babu igiyar aure a tsakaninmu, akan me kuma zai sanya ni a cikin abinda ya shafe ku."
"Saboda yana zargin mun had'a baki tare mun zubar masa da ciki. Hauwa musabbabi akan 'barin da na yi kwanaki bai yarda zubewa ya yi da tsautsayi ba. Ga ni yake yi zubar da shi na yi ina sane."
Ta dube ni da mamaki kafin ta ce." To shine me, ai ina ganin ni ba ni da hurumi anan Amina, wallahi kwata-kwata ma ni fa ba na jin dad'in jikina don Allah kada ku sanya ni cikin wannan cakwakiyartaku."
Na ce." Na sani Hauwa, ki ta so dai mu je don Allah idan ya so ni zan gayawa Baban Saude ba ki da lefi, kada ki ce ba za ki je ba, wannan zai sake tabbatar musu da cewa babu gaskiya a tare da mu."
Jim ta yi na sakkoni kafin ta ce."shikkenan mu je to." Ta ajiye plate din indomin wanda dama saura karashe kad'an ta d'auki ruwa ta kurba sannan ta tashi ina tsaye ina kallonta ta d'auko hijabin dake ta salla ta zura sannan ta dube ni. Ban furta komai ba na juya da niyyar fita ta rufo mini baya.
A ka ci sa'a kuwa baba Tabawa ba ta fito ba tana d'akinta.
Yana cin abinci a lokacin da muka shiga. Cima ce iri iri da snakes tabbacin an shirya sune domin shi akwai wad'anda ma bai bud'e ba suna cikin wamars
Wanda dai yake gabansa farfesu kayan cikin rago ne ya yi kyau sosai da katon biredi yana dankwala gefe kuma bakin tea ne babu madara tunda dama tun asali sanin da na yi masa ba ya shan nadara da zuma sai idan ya zama dole, amma ko zaman da na yi a gidansa haka yaransa suke sayo mana madara ta gwangwani duk ranar da suka yi shayi kowa da tasa amma shi haka wadda take da girki zata d'auki tsurar fulas dinsa daban da ba'kin shayinsa a ciki ta kai masa dakinsa.
Cike da nutsuwa Hauwa ta gaishe shi ma ya amsa da kulawa. Wurin ya d'auki shiru tun bayan gaisuwar da suka yi. Sai da ya kammala tukkuna a nutse ya goge bakinsa da tissue ya dube mu gabad'aya kafin ya furta." Hauwa da gaske ke ce ki ka tura Masa'udu direbanku ya sayowa Amina maganin wankin mahaifa?"
Ta dube shi a tsanake ta furta." E, ni ce Baban Saude."
Da d'an mamaki a tare da shi ya ce." Kenan da gaske hade baki ku ka yi ba kwa tsoron Allah dama?"
Murmushin takaici ta yi kafin ta furta.'' Ko daya Baban Saude kaddara ce ta gifta wani lamari mai rikitarwa ya faru a gidan nan gabad'aya muka shiga cikin gigita, to wannan ya assasawa Amina abortion bisa tsautsayi cikinta ya zube . Ganin yadda ya fice ba tare da an samu wata tangarda ba ya sanya na rubuta magani jikin takarda na sanya aka sayo mata domin ya kara taimaka mata wurin wanko abinda ya rage a mahaifarta?
Ya ce." A lokacin mai yasa kafin ki yanke hukuncin yin hakan ba ki yi yun'kurin sanar da mijinku ba, ko ko cikin bashi da uba ne?"
Shiru ta yi ta kasa cewa komai sai da ya sake maimaita maganarsa tukkuna ta ce." Wallahi ban san abinda yake tsakaninsu ba domin kuwa na d'auka ita Aminar ta gaya masa shine dalili kuma dai ni kaina ba magana yake yi mini ba a lokacin."
"Shine dalilin da ya sanya ki kenan yin gaban kanki a matsayinki na ma'aikaciyar lafiya ai kin fi karfin ki yi masa magana dalili yana fushi dake, doka ce babba a kowane asibiti amincewa da sanya hannun mai ruwa da tsaki, ina nufin wanda yake da hurumi akan abu, akan wane dalili zai amince cewa da gaske kaddara ce ba shirya zubarwa kuka yi a tare ba."
Ta fashe da kuka tana ce wa." To ni dai Allah ne shaidata Baban Saude ni ma cikin ne fa da ni, a ganina kafin na bada goyon bayan wata ta zubar da nata ai ni zan yi yun'kurin zubar da nawa dalilin abinda ya ratsa tsakanina da shi, ai gashinan a zaune yana ji ni ba matarsa ba ce yanzu."
Baban Saude ya dube shi da saurin gaske domin maganar Hauwa ta karshe ta kidima shi.
Bai ce komai ba still hankalina na kan computer dake gabansa kuma bai dago ya dubi Baban Sauden ba..
Sai ya juyo gare mu yana fad'in." Ban san da haka ba Hauwa, kuma ni nan ban titsiyeki domin naga iya gudun ruwanki ba. Abinda ya sanya ita Amina muke zarginta da aikatawaa saboda ta ta'ba yunkurin yin hakan a shekarun baya, abinda ku ka yi ba daidai ba ne, ko ni nan babu wata mace da za ta yi mini haka na amince da gaskiyarta. Sannan ya sanar da ni cewa kun had'a kai kun ware d'ayar mutuniyar kirkin cikinku, ai duk macen da mijinta zai zauna ya dinga yabo tare da fad'in kirkinta ita ta amsa sunan mace ba irinku 'yan amshin shata ba, to me ta yi muku, mutuwa ce fa ta raba tsakaninta da mijinta mai rasuwa Alhaji Amadu, kuma ya barwa Amininsa wasiyya akan ya aureta domin cigaba da kula da ita da yaranta. Ban ga matar nan ido da ido ba, amma zaman nan da na yi kaf alheri da kyautatawa mijinta yake gaya mini, ni ma gashi na ga ni yadda ta sauke ni da hidima daban daban tamkar wani basarake. Ba ku ji kunya ba Hauwa, ita fa macen da ta fi biyayya ga miji itace sauniyarsa wannan matar ta dame ku ta shanyeku a komai sannan kun yi sake wanda kuke jin haushinta dominsa ya fi sonta kun hade mata kai shi kuma ya hade kai da ita, ina kara gaya muku Kun cika shashasha!"
Tsit! wurin ya dauka bayan yin shirunsa, zuciyata ban da dokawa babu abinda take yi wannan wane irin cin mutunci ne da cin fuska Baban Saude ya shirya yi mini. Menene lefin Hauwa anan da za a sanyata a gaba da cin zarafi haka. Shikkenan a rayuwa mutam ba zai yi kuskure ba.
Wasu hawaye masu d'umi da yaji suka fara simiyowa suna bin kumatuna. Wannan karon hawayen ne kawai suke fita masu zafi da ciwo babu damar yin gunji sai dai ciwon zuciya.
Ya d'auki kofin shayinsa ya kurba kafin ya cigaba da ce wa." Gaskiya ku gyara domin kuwa babu wata gadara da za ku yi a karkashin ikon namiji, mijinku gashi nan yana ji ko shine ya yi ba daidai babu ruwana zan titsiye shi na gaya masa gaskiya ko ta yi masa dadi ko ta yi masa zafi wannan shine zaman tare Alhaji Tajo ba surukina ba ne a yanzu abokina ne, mun yi sha'kuwa ta ban mamaki a sha'aninsa zan yi tsalle na dire a ciki koda kuwa bai shafi Amina ba. Kuma za ki koma dakinki Hauwa kin ji ko?"
Tana kuka ta ce." A, a Baban Saude ni kam na ha'kura gaskiya wallahi zuciyata ba za ta iya d'auka ba."
Baban Saude ya yi shiru yana kallonta da mamaki kafin ya ce."Zuciyarki ba za ta iya d'aukar me ba?"
Kafin ta furta wani abu ya rigata ta hanyar fad'in." Ka ji abinda na ke gaya maka ko, gabad'ayansu fa Maryam ta tsone musu idan ba haka ba menene na fad'in wannan maganar, zuciyarta ba za ta iya d'aukar ganin Ina tare da Maryam ba, idan har ina son zama da ita amsar kawai na saki Maryam sai zuciyarta ta d'auka."
Chapter 19 · 0% Book details