← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 43

Sashe 20

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 7 min read

Baban Saude ya sa dariya yana fad'in." Hauwa don Allah zuciyarki ta d'auka domin kuwa akwai sauran tazara maigidanki bai cikashe ba idan yana da rabo kafin ya bar duniya watarana za ku zama ku hud'u a karkashinsa, ki yi hakuri idan har abinda ya fad'a gaskiya ne, ki d'auka ki kawar da kanki, abinda ma ke tudu biyu ki ka ci, ga ki kuma uwar Khalilullahi."
Ta shi shiru ba ta ce komai ba sai sauke ajiyar zuciya take yi har ta ba ni tausayi domin ita kadai tasan irin zafin da take ji a cikin zuciyarta.
Ya sake furta ki yi hakuri kin ji salihan mata ba a san su da irin wannan sakarcin ba, suna d'aukar kishiyarsu 'yar uwarsu kamar yadda ki ka d'auki lamarin Amina to itama Maryam ki d'auki lamarinta ku zauna lafiya kada wadda ta cutar da 'yar uwarta maigidanku matsalarku kawai yake fad'a mini tunda na zauna ita yana ta yabonta har sai da na ji wani iri a raina mai yasa ba za ku yi koyi da ita ba?"
Shiru muka yi gabad'ayanmu. Sai ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Ni ban zo gidanku domin na sanya ku koke-koke ba, ita Amina ta san wanene ni, ta kuma san halina ciki da waje babu yadda za a yi na goyi da bayan karya na take gaskiya ba na so a sake gaya mini kun aikata wani shashancin makamancin wannan, ku dinga sanar da maigidanku matsala idan ta taso tunda ai ba zaman kan ku kuke yi ba ko?"
Babu wanda ta ba shi amsa. Ya cigaba da cewa." Na gode da nutsuwar da ku ka yi kuka saurare ni, ina fatan a ce kada na zama dattijon banza a idonku bayan na gusa ku cigaba daga inda ku ka tsaya, Amina hakan ba za ta yi muku kyau ba."
Jin ya ambaci sunana na ce." In sha Allahu rabbi hakan na za ta sake faruwa ba."
Ya saki fuskarsa kamar ba shi ba ne wanda ya gama dankara mana bakaken maganganu ba ya dubi Hauwa yana fad'in." Ke ma na ci arzikin furfurata ko ?"
Ta gyada kanta tare da sanya gefan hijabin jikinta tana share hawayen da ya kasa tsayuwa daga idanuwanta.
Ya furta." To na gode tafiya zan yi yanzu nan tunda na gama abinda ya kawo, na gode sosai da tarba da karramawar da ku ka yi mini."
Ba mu ce masa komai ba sai maigidan ne ya amsa masa a lokacin da yake rufe Loptop din gabansa yana fad'in." Ba za dai ka bari ka bi jirgin yamma ba kenan."
Ya ce." Motar ma za ta kai ni gida cikin koshin lafiya, abinda na saba da zamanta tunda ni ba mazauni ba ne. "
Ya gyada kansa kafin ya furta.'' To babu damuwa idan mun tashi sai mu shiga can wajan Maryam din ku gaisa ko."
Baban Saude ya furta." Ai ya zame mini dole ranka shi dad'e wannan alatun da aka shirya mini yana da kyau na je yin godiya."
Ya kuwa fashe da dariya yana d'an dukan kafad'arsa."
Takaicin abinda suke yi ya dinga nukurkusata don sai nake ganin kamar ma da gayya suke yin hakan. Abin mamaki da al'ajabi wai yau Baban Saude ne da mijina suke wasa da barkwanci irin na abokai. Na girgiza kaina a yayin da nake jin wani irin bala'in takaici na taso mini ban ankara ba na ji motsin Hauwa ta mike tsaye kafin ta d'an rankwafa tana fad'in." Baban Saude a sauka lafiya don Allah a gaishe da mutan nan gidan da kyau."
Da sauri ya dawo da hankalinsa kanta yana fad'in." Za su ji in sha Allahu rabbi Hauwa." Tashi na yi ni ma ina dan d'auke kaina domin gabad'aya ba na son kallonsu saboda b'acin rai na furta." Baban Saude ina zuwa yanzu akwai sa'ko da za a kai wa Dada."
Ya ce." To, amma ki hanzarta domin na himmatu." Ban ce komai ba na bi bayan Hauwa wadda na hange ta can bakin kofa tana daf da fita.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 112
Haka muka jera tafiya ni da Hauwa babu magana kamar wasu kurame. Abinda dai ya sanya na k'ara ganin mutuncinta bai wuce yadda ta jure cin fuskar da Baban Saude ya dinga yi mana a fakaice ba, kuma bata yi yun'kurin ta mayar masa da raddi ba, duk kuwa da cewa lefin ta bai kai a ce an yi mata wannan titsiyar ba, amma ta jure duk domin yi mini kawaici hakan ya sanya ni jin kunyarta kwarai da gaskiya wannan dalilin ne ma ya sanya muna shiga gidan na dube ta a nutse na ce." Hauwa ki yi hakuri don Allah bisa abinda Baban Saude ya yi. Na kuma gode sosai da karar da ki ka yi mini."
Murmushi kawai ta yi kafin ta furta." Wallahi ko kadan ban ji haushinsa ba Amina, idan da wanda nake jin zafinsa a raina bai wuce mijinki ba shine ma'kiyana lamba daya."
Tana gama fad'in haka ta shige dakinta ta barni a tsaye ina bin hanyar da ta bi da kallo. Na jima a tsaye a bakin kofar falon kafin na sauke wata zazzafar ajiyar zuciya na kama hanyar d'akina zuciyata cike da nazarin hanyoyin da zan bi wurin ganin mutumin nan ya yi kukan zucci. Idan da hali ma ya yi na zahiri zuciyarsa ta cika da damuwa tunda shi ya sayi hakan da kansa. Yadda ba ya so ana yawon tiritirin kai shi k'ara bayan yana aikata lefi, to ni ma abinda na tsana kenan a rayuwa kuma tun farko-farkon auranmu na gaya masa ba na so ya'ki dainawa. Zai gane idan kai ni kara shine zai daidaitani.

Ranar dai gidan na mu tsit ya kasance kowacce tana d'akinta dama ni da baba ne muke zaman falo Hauwa ba sosai ba kullum tana d'aki a kwance. Ban fito ba sai bayan magariba Baba ta kammala komai tana zaune ita kadai a falon tana kallo da carbi a hannunta. Gaisawa muka sake yi dalili ita haka dabi'arta take duk bayan sallar farilla sai an yi gaisuwa.
Ban fi minti goma da zama ba Hauwa ta fito da waya a kunnanta tana fad'in." E gata bari na bata sai ku gaisa ." Ta miko mini wayar tana fad'in." Inna ce take magana."
Cike da fad'uwar gaba na amshi wayar ina kallonta taje ta zauna saman kujera
Muka gaisa da inna Uwani cikin kulawa da sakin fuska har muka kare gaishe-gaishenmu ban ji ta yi wata magana ba wanda da farko na d'auka Hauwa ta gaza juriya ta sanar da ita abinda yake faruwa.
Wayar ta kar'ba suka d'an yi magana kafin su yi sallama ta kashe tana kallon baba Tabawa ta ce." Indomin nan nake so baba duk dai tsugar mini da ciki take yi amma idan ba ita na ci ba na jin dadi. Amma ki hada mini da dankalin turawa ki sanya wadataccen kifi."
Na ce." Hauwa Indomee fa basir ce da atini idan kin manta na tuna miki gashi sai ki ce a sanya mini attaruhu ya ba zata tsugar miki da ciki ba, ki rage cin ta don Allah."

"To mai zan ci Amina, ita kadai nake jin sha'awa wallahi ban ta'ba ciki mai azabar laulayi irin wannan ba, da farko fa shiru kamar ba zan yi ba Amma cikin sati biyun nan ina jin ciki kwarai."
Na dube ta sosai ta dashe lebanta duk ya bushe ta ba ni tausayi. Dama kuma can tana da laulayi wannan ne ya yi tsanani.
Baba ta tashi ta kama hanyar kicin din na ce" don Allah Baba Tabawa kada ki biye mata ki sanya attaruhu kad'an kuma kada ta yi da roman nan."
Tana yar dariya ta ce." Haka kuwa za a yi, Hauwa ni ma na daina biye miki gaskiya."
Ta dube ni tana ce wa." Kin san roman shine abinda ma na fi so na dinga lasa dad'i yake yi mini."
Na ce." Mu bar maganar nan Hauwa, ni fa jikina ya yi sanyi ina fatan dai ba ki sanar da inna Uwani wani lamari ba ko."
Girgiza kanta ta yi a hankali ta ce." Babu abinda na gaya mata wallahi, mun yi waya ne mun gaisa ta ce na ba ki wayar ku gaisa."
Ajiyar zuciya na sauke domin har cikin raina na yarda da maganarta.
Chapter 20 · 0% Book details