Sashe 10
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 7 min read
Ta'be baki ta yi tare da furta." Haba ko yanzu na buga na bada ruwa wallahi zuciyata wasai nake jin ta. Murmushi takaici kawai na yi na yun'kura na tashi cikin zuciyata nake fad'in ba za ki ta'ba canzawa ba Hauwa, ba ki takali rigimar kina jin dad'i ba abinda zai biyo baya shine damuwar domin kuwa nasan akwai rikici akwance a tsakaninmu da shi uban gayyar. Shiga ta d'aki da kamar minti ashirin na fara jin hayaniya na tashi. Murya Hauwa a sama da wata murya da na kasa tantance ko ta wacece. Cike da zullumi da fargaba na fito falon na same su a tsaye cirko cirko har da yaranmu k'ananu a tsaye kusa da baba Tabawa dake ko'karin shiga tsakani.
Nabila ce 'kanwar Momi mutuniyata ce sosai kuma tun lokacin rasuwar Alhaji Amadu muke zumunci don har musayar lamba muka yi. Sai ta d'an ja baya da ni ta rage kiran wayata bayan auran 'yar uwarta da maigidan. Ni kuma ban ta'ba nuna mata komai ba don wasu lukutan har magana nake yi mata idan na ga ta d'ora status a Whasap amma dai duk da hakan ta kasa sakin jikinta kamar lukutan baya.
"Ba ku isa ku kashe Momi ba Hauwa. Idan ba zata iya ba, ni zan kar'bi rigimar akan me? me ta yi muku da za ku tisa ta a gaba, mace tana sonku da zaman lafiya, tana d'awainiya da yaranku amma kuna cin dunduniyarta. Idan kun had'e mata kai sai me? Mijinta yana sonta fa kuma ita alheri a jininta yake, wallahi ba za mu lamunta ba, za mu iya d'aukar kowane irin mataki akan hakan."
Ido na zuba mata kawai kaina ya gama d'aurewa da maganganunta amma ba zan ce mata komai ba Hauwa kadai ta isheta tunda dama mai neman kuka ce.
Aikuwa ta bugi kirji har tana had'awa da tsalle tana fad'in." Karya banza da wofi an had'e mata kan don Allah ku d'auki mataki, matsafa masu kauce hanya domin neman duniya menene ba mu sani ba asalin dukiyar da uwar guzumar taku ta tara daga majiya mai tushe cewa kudin tsafi ne uwarta da ubanta ta bawa gumaka suka shanye jininsu. Har mu za a zo a yi wa wata burga, mun ce ta yi dawainiya da yaranmu ne? Ita taga zata iya. Mu dai in sha Allahu ba zamu rayu da kudin Haram ba. Ba zamu fake da Allah da addini mu ciyar mu tufatar da kudin jinin mutane ba."
Nan da nan Nabila ta rikici sai ta fara rawa murya idanuwanta suka ciko da ruwan hawaye ta ce." Wallahi tallahi Hauwa sai mun yi shari'a dake sai kin tsaya a gaban alkali kin bada sheda abinda ki ka fad'a, ba za mu yarda da wannan kazafin ba.
Ta ce." Ashe babu dadi kazafi ko. Mai yasa kuka take gaskiya da gangan, yanzu ke nabila har kina da bakin da za ki zo ki tsaya a gabanmu da wata banzar magana. Ki je ki tambayi 'yar uwar ki irin zaman da muke yi da ita a gidan. Ai ba a banza ta ri'ke mana yara ba. A shirye nake ki kalleni da kyau babu wata 'yar iska da ta isa na ji tsoronta wallahi."
Nabila ta kasa cewa komai domin ta yi mutukar kaduwa da jin maganganun da suka fito daga bakin Hauwa. Duk yadda ta dinga kokarin hana kanta kuka hakan bai samu ba cikin gaggawa ta kama hanyar fita ba tare da ta iya mayar da martani ba.
Cike da mutuwar jiki na dubi Hauwa da take ta numfarfashi na ce." Tsakani da Allah Hauwa idan rai ya baci yana da kyau a sanya hankali da tunani. Yanzu ke don Allah a Ina ki ka ji wannan maganar kada fa ki d'auri kanki Hauwa mai ya yi zafi ne, ni dai idan har a kaina ki ke wannan balo'kokon to don Allah ya isa haka, yaran da suka asassa wannan rikicin na d'auke su da gidan fakat mu zauna lafiya, babu ruwanki da matar nan da duk abinda zai shiga tsakaninta da mijinta a kan hakkin kawai ya kamata ki yi magana, amma ki yi kokarin kawar da kanki daga barin ji da ganin abinda yake yi a kanta."
Baba Tabawa ta jijjiga kanta cikin alhini da damuwa ta furta." Don Allah ku zauna lafiya, wallahi ba na jin dad'in abubuwan nan da suke faruwa."
Tsaki ta ja kafin ta ce." A shirye nake da abinda zai biyo baya Amina, wallahi yadda na tsani mutuwata haka na tsani matar nan, kuma abinda na fad'a ai ba k'aharu ba ne, ni ma ji na yi ana fad'a a duniya." Daga haka sai ta tashi ta shige dakinta fuskarta babu rahama ko kad'an. Ni da Baba Tabawa muka bi ta da kallo cike da tsantsar mamaki. mai ya yi zafi haka, a ganina abinda take yi ai ni ya kamata na yi amma ban yi ba, ita lamarin nata yana nema ya wuce gona da iri fa.
To ita rigima dama akwance take shiyasa tashinta bashi da amfani domin kuwa muddin ta tashi akan sha mutukar wahala wajan samun ruwan da zai kashe. A wasu lukutan ma ana kashetan shaid'an da mukarrabansa suke shiga cikinta su yi kane-kane, su bugi wannan bangare su bugi wancan b'angare.
Lokacin da na ga kiran wayarsa hankalina ya tashi sosai dalili ban san mai yake 'kunshe a cikin Kiran nasa ba, daga jiya zuwa yau abubuwa masu muni sun faru wanda na tabbatar da cewa muddin ba a kai zuciyoyi nesa ba to rayukan kowa zai 'baci har da wad'anda ma ba su ji ba, ba su ga ni ba.
Na daidaita yanayi kwarai da aniya ban bari raunina ya bayyana ba na d'aga wayar a nutse gaisheshi na fara yi bai amsa mini ba ya ce." Kai ni 'kara wurin Mahaifiyata bai gamsar da ku ba har sai kun had'a ba ki kun cutar da baiwar Allah ko Amina?"
Na ce." Ban fahimci maganarka ba."
"Nabila ta kira ni yanzu ta cikin tsananin damuwa tana fad'in irin abinda kuka yi mata yanzu daidai kenan Amina, ko kina so ki nuna mini hassadarki a fili domin Allah Ya suturta Maryam ta fi ku kyau da ilimi da goge, ta fi ku dukiya da kyauta da tausayi, kana ta fi ku mutunci da karrama dan adam. Idan har za ku yi kishi akan soyayyar da nake yi mata wannan ba zai dame ni ba, tunda zuciyata ce ita ta za'ba a madadinku, amma ba zan lamunci cin zarafi da sharri ba, zan shige mata gaba domin ganin an hukuntaku bisa sharrin da ku ka yi mata."
A nutse na ce." To muna sauraran sammanci, ita Maryam tana da kai Tajo, Amina da Hauwa kuma suna da Allah, maganar da ka ke yi akan cewa muna yi mata hassada wallahi tallahi ni ban ga abin kyashi da b'akinciki a tare da wannan matar ba. Kudi dai kasan daidai gwargwado ina dasu babu wata mummunar hanyar da na bi wurin nemansu gumina ne, halak dina ne, babu wani mahaluki da ya ta'ba ba ni kwabonsa da zummar na yi jari, don haka wallahi babu wata mace da zan yi hassada akan wata banzar dukiya. Sai abu na karsh wanda nake so ka sani cewa ni Amina Tajo ba a gabana yake ba balle har raina ya sosu domin hankalinsa ya karkarta can wani gefe, ai ita soyayya guda daya ce tuntuni na bada ita a wani wuri har abada kuma wani namiji ba zai ta'ba samunta ba a wajena."
Tsaki ya ja kafin ya ce." kuna abu sai ka ce jahilan farko. Duk da wanda ya ji wannan dabbancin da kuka yi ba zai yi muku kallon girma."
Bai bari na ce wani abu ba ya kashe wayarsa. Ban damu ba, ni ma na ajiye tawa wayar zuciyata kamar ta tsage saboda tsananin tashin hankali da fargaba kafafuna sai kyarma suke yi tun a falo lokacin da Hauwa da nabila suke musayar yawu nake jin marata na murda mini kad'an kad'an. Sai da na shiga bandaki na tsuguna da zummar fitsari jini ya biyo baya.
Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! kalmar da na fara ambata kenan na tashi tare da mayar da pant dina na fito tsakiyar d'akin na tsaya Ina dawurwura alamun zubewar ciki ne ba wani abu ba. Tunda aka shiga wannan rintsi wallahi na manta wai ina da wani ciki sai yanzu da naga jini ciwon marar ya tsananta.
Jikina na gyara na fito falo a kintse Hauwa tana d'aki sai Baba Tabawa a falo da yara sun zagayeta tana basu labari.
Kai tsaye d'akin na bi Hauwa tana kwance saman gado da wayarta a hannunta har yanzu babu sukuni a tare da ita ta tashi zaune tana kallona kafin ta ce." Ina kuma za ki je na gan ki da hijabi."