← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 43

Sashe 6

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read

Tun fitar nan da ya yi bayan mun yi musayar yawu bai sake shigo mana ba, dama girkin Momi ne, cikinmu babu wadda ta neme shi. Gabad'aya muna falo ni da Hauwa da Baba Tabawa muna kallo da hira jefe-jefi. Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin jallabiya yana ta k'amshi turaransa wanda na tabbatar da cewa Momin ce ta bashi domin turaran gaskiya irin na manya ne mai dadin k'amshin. Muddin ya shiga waje sai kowa ya ji shi k'amshinsa.
Cikin nutsuwa duka ya gaisa da kowa. A dan sanyaye ya ce." Momi ba lafiya fa." Hauwa dai ko kallonsa ba ta yi ba. A takaice na ce.'' Mai yake damunta?"
"Ciwon kai ne mai tsanani ba su jima da dawowa daga asibiti ba tare da Baba."
Na ce." Allah Ya sawwa'ke. Ya amsa da amin."
Baba Tabawa ta ce." Allah Ya sawwa'ke idan ka koma ka yi mata sannu da jiki kafin na mu shigo."
Ya ce." To.''
Falon ya yi shiru na 'yan mintina kafin ya ce." Mama za ku je dubata ko?"
Shiru na yi ban ce masa komai ba. " Ya sake maimaita maganarsa Hauwa ta dube shi tana harararsa ta ce." Wai kai wane irin yaro ne Kamalu?''
Ya dubeta a hankali yana dan murmushin. Ta ja tsaki tare da juyar da kanta gefe guda..
Murmushi kawai ya yi ya sunkuyar da kansa kasa. Baba Tabawa ta dubi Hauwa da yanayi na damuwa na lura maganace a bakinta amma ganin yadda fuskar Hauwa take a cud'e ya sanya ta kasa cewa komai sai ma ta tashi ta nufi kicin tana cewa." Bari na kwa'danta maka zogale mutuminka."
Tana shiga kicin Hauwa ta kalleshi fuska babu fara'a ta furta.'' Kamalu kalle ni nan."
Ya dubeta da sauri. Ta ce." Ka gaya mini gaskiya tsakaninka da Salim mai kuke aikatawa?"
Cike da zullumi da d'an tsoro ya furta." Anti ban fahimci maganarki ba." Ta sake zare masa ido a karo na biyu tana cewa." Baka fahimce ni ba menene tsakaninka da Salim.?"
Ya ce." Rigima yake nema na dashi kullum da abinda zai yi mini na rashin kyautatawa."
"Gaskiyar abinda yake faruwa kenan a?" Ta fad'a idonta tsaye a kansa.
"Wallahi anti shine gaskiya bayan wannan babu wani abu, kuma duk abinda yake yi mini ba na kula shi."
Ta ce." To yau d'aya don Allah ka je ka zage k'arfinka a kansa ka had'a masa jini da majina ba zai ka'ra ba. Nasan duk da ya girmeka amma ka fi shi san girma da 'barage, ka nuna masa bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne."
Da mamaki nake kallonta kafin na ce." Mai yasa ki ke bashi wannan shawarar Hauwa. "
Ta ce." Ita ce mafita kawai dole su gwada k'wanji muddin Kamalu ya kai Salim k'asa wallahi sai ya daina yi masa shegantaka."
Na girgiza kaina a nutse na ce." A a Hauwa wannan ba dalili ba ne, idan kuma wata matsalar ta faru fa, masifa fa zamu shiga gabad'ayanmu. Ta ce Daga nan sai ayi fad'an k'arshe kawai."
Girgiza kaina na yi na ce." A'a Hauwa."
shi ma yaron lamarin ya bashi dariya yana yi ya ce." Anti mai yasa zan dake shi?"
Ta ce." Saboda d'an-iska ne masharranci." Ya gyada kansa a nutse ya furta." Gidansu zan bar musu ai, wallahi rashin lafiyar Momi yana da ala'ka da abinda yake yi mini, wannan shine dalilin da ya sanya nake rangwanta masa tausayi take ba ni."
Ni ma na tabbatar da hakan sanin halinsa na zuciyata da saurin kai duka tun yana yaro karami."
Hauwa ta ce.'' Kasan mai ya ke gaya Baba akanka?"
Ya girgiza kansa yana kallonta.
"Wai kana nemansa da daddare?"
Cike da rashin ganewa ya ce." Nema wane iri abinda ba a d'akinmu yake kwana ba."
Ta ce." Sharri ya shirya maka wai kana cire masa gajeran wando."
Ya zuba mata ido fuskarsa cike da zallan mamaki da al'ajabi. Ni dai zukud'un na yi ina kallonta. Na rasa azancinta na gaya masa akwai nauyi.
Ta dube ni tana cewa." Ba za a munafurceshi ba domin kema na ga baki da niyyar sanar masa abinda aka shirya masa na k'azafi.''
Na ce." To fadar ai bata da amfani Hauwa." Ni kaina nauyin gaya masa nake yi ni da na haife shi.
Kafin mu yi aune dukkaninmu muka ga ya mike zumbur! hanyar fita ya kama. Da sauri na tashi tsaye ina kiransa Bai juyo ba ya bud'e kofa ya fice a gaggauce!
Na dubeta tare da cewa." Kin ga ni ko Hauwa!"
A sanyaye ta tashi tsaye itama tana fad'in haka yake da zuciya da dama.
Na gyada kaina ban ce komai ba na nufi daki. Hijab na sako na fito ta ce." Ina za ki je kuma?" Ina ko'karin fita na ce." Bayansa zan bi dalili nasan halinsa shiyasa Hauwa ban so ki ka gaya masa ba wallah..... Kafin na rufe baki Yusi ya shigo a guje. Cikin rud'u da tashin hankali ya ce." Mama gasu can suna fad'a a harabar gidan Momi sai kawai ya fara hawaye.
Na fita da gaggawa ya rufo mini bayana ban san inda nake jefa kafata ba gate din gidan a bud'e hayaniya na ta tashi.
Ina shiga na hango ana rirrike Kamalu yana ta han'koran kaiwa Salim naushi duk ya fasa masa hanci da baki masu gadin gidan sun ri'ke shi da kyau shi kuma maigidan yana ri'ke da Salim da yake ta tare jinin da yake fita daga hancinsa da tissue.
Ina isa wurin na ri'ke hannunsa sai suka cika shi. Da kyau na ri'ke shi domin sai zillo yake yi yana kallon Salim jikinsa na karkwarwa jijiyar kansa ta tashi radau botiran jallabiyar jikinsa duk sun zube. Salim kam jikinsa ya yi 'kwatakes hanci da bakinsa sai fitar da jini suke. Jamilu direbansu yana ta ko'karin fito da mota da zummar tafiya asibiti. Kafin mu fita daga gidan Hauwa da Baba Tabawa suka shigo yadda na lura da fuskar Hauwa wasai! Baba Tabawa ce kawai take salallami tare da tambayar ba'asin abinda ya had'asu.
Ban ce komai ba na ja shi muka fita. Hauwa ta rufo mini bayana ko kallon inda maigidan yake tsaye ba mu yi ba. Muna dai kallon lokacin da Baba Tabawa ta nufe shi da tsananin damuwa a tare da ita.
Muna shiga gida Hauwa ta ce." Ka yi daidai Kamalu na rantse da girman Allah ka cika d'an halak, ka haifu kuma ni zan tsaya maka idan ma ya ce zai bi kadin jinin da ka zubar masa."
Na zauna saman kujera kaina yana juyawa wannan wane irin bala'i ne. Gabad'aya ma na rasa abinda zan ce. Yana zaune a gefena ina jin yadda kirjinsa ke fitar da wani irin nishi na juya na kalleshi wallahi gumi yake yi sosai kamar babu Ac a falon. Kamalu ne fa ba'a ta'ba shi ba ma yana siyan fad'a ballantana an ta'ba shi. Wannan ya tabbatar mini da cewa lallai sharri Salim din ya yi masa bai aikata ba.
Yusi ya shigo idonsa ya kada ya yi jajawur! Ya tsaya akan d'an'uwan yana fad'in." Mai yasa ka yi haka Yaya, mai yasa ka dake shi har sai da jini ya fita, Yaya Salim ne fa, duk abinda zai yi maka ka ai sai ka duba Momi, ita kanta fa ba ta goyon bayansa matsalarku ce fa ta haddasa mata mugun ciwon kai. Yaya ba ka duba hakan ba Momi tana kwance amma kuke yin fad'a abinda ba ta so.''
Hauwa ta buga masa tsawa tana fad'in." Rufe mana baki shashasha kana abu sai ka ce mace, ya dake shi din, ai haka ake son namiji ya kasance."
Maganarta ta yi daidai da lokacin da maigidan ya shigo. Gabad'ayansa a ki'dime yake rigar jikinsa har da jinin Salim. Ido jawur yake duban Hauwa ya ce." Kin kyauta Hauwa, abinda ku ka yi mini shine daidai ko? Ni ban isa na yi iko da hukunci a gidana ba, ban isa ba, kun had'a kai kun sanya kafa kun shure umarnina." Ya nisa kafin ya cigaba da ce wa." Ke tun kafin mu zo nan na gargadeki akan maganar kada ta fita saboda gudun tashin masifa ba ki ji, ki ka samu uwar yaron nan ki ka gaya mata. Hakan bai isheki ba har sai dai ki ka cire nauyi da kunyar yaron nan ki ka gaya masa. Hauwa kin zama wake d'aya. Dake zan yi kuka duk abinda ya biyo bayan wannan masifar domin kuwa ke ce sanadi kuma wallahi sai na hukuntaki."
Shiru ta yi uffan ba ta ce masa ba.
Na ce." Jikinka ne yake kyarma ka rasa nutsuwa saboda an daki dangwal ko, kuma d'an matar so. Amma ai bacci ka ke yi har da munshari kuma ba ka fasa hurd'odinka ba a lokacin da yaron nan ya nannako sharri ya alakantashi da yarona. Kamalu mutum ne kamar Salim sai da ubansa talaka ne ba irin abokin Alhaji Amadu ba. Amma ni Amina ni ce gatansa. Idan har kun ce ba za ku yarda ba ku kaishi k'ara kotu, sai ku yi amfani da dukiya mu kuma za mu yi amfani da karfin addu'a. Wanda ya rike Allah shi yake dahir."
Baba Tabawa ta zo da sauri ta rufe mini baki da hannunta tana fad'in." Kina da hankali kuwa Amina kin manta wanene a gabanki mijinki ne fa, wai mai yasa kuke nema ku 'bata rawarku da tsalle, ku dubi alheri matar nan, kada ku sanya zazzafan kishi akanta, idan har kuka had'e mata kai duniya za ta zage ku."
Cikin kuka na ce." Baba Tabawa ke ce duk abinda yake faruwa ba ki sani ba, ranar wanka ba a boyon cibi. Duk wannan husumar da ta wanzu Salim ne sanadi ya sanya Kamalu a gaba da neman fitina ta yau daban da ta gobe. Ya kira shi b'arawo dan'ta'adda. Ya zo ya yi masa sharri mafi muni wai yana nemansa da daddare, dukkaninsu guda nawa suke idan ba lalacewar zamani ba. Na yi kawaici na yi hakuri duk don kada a ga kamar na za'bi nawa. Amma dashi da matarsa basa gani to mai yasa yanzu ba zan fito na kare kaina na kuma kare yaron nan ba."
Chapter 6 · 0% Book details