← Book details Gudun Aure Part 5 Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 43

Sashe 7

Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 8 min read

Cike da mutuwar jiki ta juya tana kallon wajan da maigidan yake a tsaye wanda shi tun lokacin ma da na fara magana ya haye samansa. Sai ta nemi wuri ta zauna jikinta a mace ta ce. Amma kuwa wannan yaro bai kyautawa kansa ba, wace irin magana ce wannan mara dad'in ji, mai Kamalu ya yi masa da zai yi masa wannan 'kagen, jama'a wace irin rayuwa muke ciki ne?"
Hauwa ta ce." Babu abinda ya yi masa kawai Yana b'akinciki da k'yashin yadda Ubangijina ya daukakashi fiye dashi shikkenan fa, sai kuma gadarar yana cin arziki uwarsa.
Yana nishi ya furta." Daga yau an daina cin arzikin banza arzikin wofi wa yasan ma ta yadda uban nasu ya nemi kudin da ya tafi ya bar musu. Mamansa kawai ita nake dubawa itace take ba ni tausayi"
Babu wanda ya ce komai sakamakon saukowar maigidan daga sama ya canza kaya amma nasan duk ya ji maganganun Kamalu. Bai ce mana komai ba ya kama hanyar fita ransa a tsananin 'bace!
Yusi ya bi bayansa shi ma ba tare da ya yi wa kowa sallama ba.
Hauwa ta ja tsaki tana fad'in." Haba ai ni yau kwanan farinciki zan yi wallahi."
Yusi ya sake dawowa daga bakin kofa ya tsaya yana fad'in." Ka zo in ji Momi."
Hauwa ta kalleshi amma ba ta ce komai ba. Sai harara da ta ke wurga masa. Ya sake maimaita maganarsa "Momi ta ce ka zo."
Ya ce." Ka je ka ce mata gani nan."
Har ya juya zai fita na ce." Yusi zo nan." Ya juyo yana kallona na ce." Zo."
Ya zo ya durkusa kusa da ni.
Na ce."Ka za'bi Momi ko?" Ya yi shiru bai ce mini komai ba.
Cikin tsawa na sake cewa." Momi ce uwarka ba ni ba ko Yusi?"
Sai ya sa kuka yana cewa." Mama don Allah kada b'acin rai ya sanya ku yi abinda zai janyo muku nadama, Momi duk abin nan da yake faruwa wallahi ba ta da laifi, tana sonmu dukanmu na yarda Yaya Salim ya yi laifi amma kada abin ya shafeta itama cike take da takaici da b'acin rai."
Hauwa ta ce." Idan abin ya dameta tunda farko mai yasa ba ta shigo an tattauna ba." Da sauri ya ce." Bata da lafiya wallahi."
Yana rufe baki Nusaiba ta shigo ta ci kuka ta k'oshi domin kuwa fuskarta har ta d'an tasa idonta ya yi ja wata'kila d'an uwan ne ya kira ta a waya a gaya mata. Yaranmu kaf tun daga kan Khalil Hassana da Usaina Minal suna bayanta.
Ba tare da ta gaishe da kowa ba tana daga tsaye take cewa." Mun gode bisa abinda aka yi mana, Allah Ya saka da alheri, mu ba mu gaji fitina ba, domin tarbiyar da iyayenmu suka yi mana kenan, koyaushe Mominmu cikin yi mana nasihar mu zauna lafiya da kowa take yi. Mahaifinmu kafin ya rasu karshen maganarsa shine mu ri'ke Babanmu Alhaji Tajo a matsayin uba. Wannan dalilin ya sanya ba za mu yi fad'a daku ba domin muna kallonsa a matsayin uba, kuma muna buk'atar kwanciyar hankalinsa." Ta sauke ajiyar zuciya kafin ta cigaba da ce wa."
Sannan yaranku gasu nan Momi ba ta da lafiya, dama kokari ne kawai irin nata na ce kowacce ta raini abinta."
Da sauri Hauwa ta ce." Dama ai ba mu sanyata ba, ita taga zata iya, rashin lafiya kuwa kowa ma a cikinta yake mara kunyar k'arya, wannan tabarmar kunya ki ke nadewa da hauka. Wanene musababbi idan ba d'an'uwan naki ba. Shi za ki jawa kunne a matsayinki na wadda take gaba dashi, cikinmu dai babu sa'arki da za ki zo ki yi wa d'ibar albarka, sai mai dan yara sun dawo gidan ubansu dama ai ita ta nema ba wani ne ya ce mata ta d'auke su ba."
Ba tare da ta sake cewa komai ba ta kama hanyar fita jikinta duk a sanyaye. Duk da abinda suka yi wa Kamalu sai da na d'an ji wani iri a zuciyata. Gabad'aya ma yaran ba su iya fad'a ba daga ita har Salim din domin kuwa da sun iya fad'a ina ga da wutar ba ta mutu ba. Shi Adam ma tunda ake hatsaniyar bai ce komai ba sai share hawaye yake yi gwara Yusi ya zo yana kalubalantar d'an uwan nasa.
Da zai tafi kiran da Momin take yi masa ban hana shi ba, amma hukuncin da na yanke a zuciyata yana nan ban janye shi ba sai yaran sun bar gidan da garin ma gabad'aya domin kuwa ba zan iya ba. A shirye nake da tarar kalubalen da zan fuskanta.

Washe gari da safe kalau ya shigo mini tsaf dashi cikin Pakistani ni. Muka gaisa da yake a d'aki ya same ni ban kai ga fita falo ba tukkuna na ce masa ya je ya gaishe da Hauwa da Baba Tabawa ya dawo. Ya fita minti biyar ya dawo ya zauna a gefena. Na dube shi a tsanake na ce." Jiya mun gama magana da Hamusu a waya zan sanyaku a motar haya zuwa kano sai ku dinga waya dashi kafin ku sauka. "
Ya ce." Na ji dadin hakan Mama, kin ga kuma Baba bai jima da tafiya kanon ba don har d'akinmu ya same mu ni da Yusi yana tambayarmu zai je kano ko muna da sa'ko wurin Baba Hamusu."

Shiru na yi Ina d'an nazari tafiyarsa kano da gaggawa irin haka tana da ala'ka da kiran Hajja dama ta ce zata kira shi babu tamtama kuwa wurinta ya tafi.
Na ce. " Hakan ya yi daidai ni ma na ji dad'i, ka je ka kira mini Yusi Amma kada ka gaya masa komai."
Ya ce." To shikkenan. Ya tashi ya fita da sauri. Ni kuma cikin gaggawa na shiga toilet domin yin wanka. Ina fitowa su Hassana suka shigo tsaf gabad'ayansu Baba Tabawa ta shiryasu. Na ce." Kun zo mu gaisa ne, ashe kun san ni?"
Husaina dariya ta kama yi ta haye gado ta kwanta tare da sanya babban yatsanta a baki tana totsa.
Na ce." Ke ba ki daina tsotsar hannun nan ba dama." Ta yi shiru ba ta ce mini komai ba sai ma ta janyo rigar baccina da na cire da yake mai laushi ce ta dinga shafa rigar da hannunta.
Hassana ta je ta cire hannun daga bakinta cikin tsamin baki ta ce." Momi fa ta hana ki."
Na dubesu Hassanar na cire hannun ita kuma Husainar na mayarwa bakinta. Na juya da niyyar bude wardrobe na d'auko kaya na ji kuka da k'arfi da sauri na dube su. Husaina ce ke kuka sosai ta cukume Hassana da kokawa Minal na gefe a tsaye tana kallonsu.
Wajan na nufa ina fad'in." Mai ya had'aku." Cikin tsamin bakinta tana kuka ta ce." Dutana ta yi, ina luwanta da ni."
Dariya nasa na ce." Ke Hassana mai yasa ki ke duteta?"
"Momi ta hanata tsotsar hannu." Ta ba ni amsa tana zumbura baki.
Kamulu ya shigo ya ce." Fad'a suke yi ko Mama." Na ce." E dama haka suke yi a gidan Momin"
"Wallahi yini suke yi fad'a ai Taburni tana aiki kuma Hassana ce mai zalinci. Wataran Momi idan ta gaji dai sai ta cewa da Taburni ta goya Husaina don a samu mafita nan sai ta ce ba ta yarda ba dira kuka. Momin da kanta take cewa a d'auko mata zani sai ta goyata ake samun zaman lafiya."
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 104
Na ce." Allah Ya kyauta ka ja su ku je falo kafin na shirya amma ina Yusi din yake ?''
"Gashinan zuwa, amma mama kin san ba lallai ne ya shigo shi kadai ba duk inda ya ajiye kafarsa anan Adam yake ajiye tasa.
Shiru kawai na yi ina nazari. Babu fa wani dalili da a yanzu zai hana yaran nan barin garin nan. Na ce." Je ka falo, idan sun shigo tare ka turo mini shi." Ya amsa da "to shikkenan. Kafin ya sanya yaran a gaba suka fita.
Gama sanya kayana ke da wuya Yusi ya shigo ya sha ado cikin yadin kufta d'inkin kansa abin kallo ne ballantana takalmin da yake kafarsa. Babu shakka matar nan ta na hidima da yaran nan kuma duk abinda za ta yi babu bambanci abinda Adamu zai sanya a jikinsa shi Yusi zai sanya duk tsadarsa kuwa. Ko turarukan da suke amfani da shi wallahi sai mai karfin jari. Jikina ya yi sanyi kalau a yayin da nake duban yaron cikin Kamala da nutsuwa tare da kwarjini fatarsa luwai alamar hutu da jin dad'i sun ratsa jikinsa.
Kafin ya zauna a gefana sai da ya d'an risina tare da furta." Mama ina kwana, an tashi lafiya?"
Na amsa a nutse ina sake nazartarsa har yanzu babu walwala da sukuni a tare dashi tabbacin abubuwan da suke faruwa na damunsa. Ya nisa kafin ya sake fad'in." Momi ta ce tana gaisheki ta ce na gaya miki za ta shigo idan an jima."
Sai da nutsu sosai na dube shi babu fara'a a tare da ni na ce." Yusi ina so ka bud'e kunnuwanka da kyau ka ji abinda zan gaya maka, hukuncin na yanke kuma babu mahalukin da ya isa a wannan ga'bar da tura ta kai bango ya dakatar da ni." Na yi shiru Ina kallonsa yayin da gabad'aya ya shiga nutsuwarsa alamun fargaba da tashin hankali sun bayyana a fuskarsa.
Na cigaba da ce wa." Hukunci na yanke akanka kai da d'an'uwanka Kamalu za ku bar garin nan gabad'aya rikonku zai koma hannun Hamusu za ku cigaba da ri'ke mini harkokina yanzu shirin da na yi kenan domin tun jiya na gayawa Hamusu halin da ake ciki saboda haka yanzu za mu je tasha tare na sanyaku a mota in sha Allahu.
Chapter 7 · 0% Book details