Sashe 8
Gudun Aure Part 5 Hausa Novel · about 7 min read
Matsananciyar damuwa ya shiga wadda baki ba zai iya misalta irinta ba. Ina kallonsa yana ta ko'karin mayar da hawayen da ya cika kwarmin idonsa amma duk dubararsa sai da ruwan hawayen ya kwaranyo kumatunsa. Murya na rawa ya ce." Mama mai yasa za ki yanke wannan hukuncin, ki dubi Allah da Annabi ki janye kada ki hukuntani akan laifin da ba nawa ba. Ki dubi k'auna da soyayyar da Momi take yi wa jininki kada ki sanya 'yan uwanta su yi mata dariya. Mama ni da Adam akwai k'auna da sha'kuwa sannan ba na so na rabu da Baba, ba zan ta'ba mantawa da hallacinsa a gare ni ba. Sannan Momi tana nan tana yi mana shirye shiryen tafiya karatu saudia makarantar da Yaya Salim ya yi karatu, ki yi hakuri Mama, kada ki hukunta Momi da laifin da itama ranta yake soyuwa."
Ga'bo'bina ne suka yi sanyi ganin yadda hawaye suke zarya a dakalin fuskarsa. Ya kama hannuna ya ri'ke kamatau jikinsa har karkwarwa yake yi.
Na ce." Yusi ba ka ji wani iri a cikin ranka ba a lokacin da Salim yake yi wa dan'uwanka sharri, abu mafi muni fa ya jingina masa. Da farko ban d'auka abin ya yi tsanani ba na danni zuciyata duk domin a zauna lafiya. Amma Yusi ba abu ne mai wahala ba a yanzu dai na tsaya da Momi da Salim a gaban alkali domin yin shari'a dasu akan wannan mummunan sharrin da Ubangiji ya halakar da wani gari kacokan akan aikatawa.
Hawayen da nake dannewa suka goce da karfinsu duka dinga fafara gudu a kumatuna. Na ri'ke hannunsa da kyau na ce." Ka ture maganar sabo da hallaci da kyautatawa Yusi duka nasan mutanan nan biyu sun yi mini, ni ma ina rokon Allah ya ba ni ikon rama musu, amma ba na ji a zuciya za a samu zaman lafiya da juna muddin Kamalu da Salim suna zaune a makwanci d'aya. Kun girma da kai dashi ku tafi ku taimakawa kanin babanku ku nemi arziki ta hanyar halak, ina da shaguna da dukiya a hannun Hamusu sai mu 'bullo da hanyoyin nema domin mu gina kanmu da gobenmu, watarana za ku yi aure, za ku hayayyafa a wannan lokacin ya kamata ace kun dogara da kanku Yusi ba wai a ce koyaushe kuna ra'be-ra'be a gidajen mutane ba."
Kuka kashir'ban yake yi yana fad'in." Mama na fahimci azancin ki, na gane abinda ki ke so na gane, amma don Allah Ina neman alfarma a wajanki duk rintsi kada ki yi rigima da Momi wallahi mutuniyar kirki ce, ina kaunarta kamar yadda nake kaunarki Mama, kuma duk abin nan da yake faruwa babu sanya hannunta ko da anti Nusaiba ta dawo muku da yaran nan wallahi bata sani ba lokacin tana bacci da ta tashi ta samu labari wallahi sai da ran anti Nusaiba ya 'baci da kuka ta bar gidan. Ita kanta Momi ta rasa yadda za ta yi da su. Adam ne kawai bai shiga rigimar ba, Yaya Salim da anti Nusaiba sun had'e kansu sun daina jin maganar Momi."
Na ce." Sai ka ce mara hankali Yusi, ba zan yi rigima da ita ba, to akan me? ai ta yi mini alheri, abinda dai nake so da kai shine ka samu nutsuwa ka kuma kwantar da hankalinka, maganar cigaba da karatu kuma ko ba ku fita waje ba sai ku d'ora a bayaro university ku kai matakin da kuke buk'ata in sha Allahu
Lokacin da muka fito falo Kamalu da Adam ne a zaune suna magana da sauri yaron ya zame daga kan kujerar da yake zauna yana fad'in."Mama ina kwana mun tashi lafiya?"
A nutse na amsa da kulawa sai ya koma saman kujerar ya zauna jikinsa duk a sanyaye. Hauwa ta fito daga d'aki da tawagar yaran a bayanta tana fad'in." Kun shirya kenan?" Kafin na amsa Adam ya gaisheta ba tare da ta dube shi ba ta amsa kamar ba ta so. Na gyada kaina tare da kallon kamalu da kansa yake sunkuye na ce." Tashi mu tafi."
Baba Tabawa ta fito daga kicin hannuntà ri'ke da madaidaicin baho da dabino a ciki. A nutse muka gaisa kafin na d'ora da fad'in." Baba zan kai yaran nan tasha zuwa kano yanzu zan dawo in sha Allahu."
Ta ce." To shikkenan sai kin dawo Kamalu a gaishe da mini da Gwaggo da kyau sai kun dawo Yusuf." Yadda take magana shi ya sake tabbatar mini da cewa ba ta fahimci nufina ba domin kuwa da ta gane hukuncin da na yanke sai ta yi magana akan hakan.
Adam da sanyi jiki ya dubi Yusi yana cewa." Za ku je kano amma babu labari Yusi babu neman rakiya, ni ma ina so na je na gaisa da Gwaggo da Baba Hamusu."
Yusi ya riko hannunsa ya tashi tsaye muryarsa sanyi kalau ya ce." Wallahi ban san da tafiyar ba sai yanzu ka yi hakuri d'an uwa, idan har za ka je sai mu je ai babu damuwa."
Da farinciki a fuskarsa ya furta " Zan je mana bari na sanar da Momi kai kun yi sallama ko?"
Yusi ya girgiza kansa a hankali ya ce." Zan shigo yanzu na yi mata sallama.
Adam na fita ni ma na kama hanyar fita zuciyata cike da zullumi da nazari nasan ba karamin gagarimin rikici ne zai 'balle a gidan ba dalilin wannan matakin da na d'auka. Amma a shirye nake da tarar dukkanin kalubalen da zan fuskanta daga maigidan koda kuwa ta rabuwa ce. Ai an yi abinda aka yi, Allah Ya shige mini gaba.
Muna fita harabar gidan Masa'udu shine babban direbanmu da maigidan ya ajiye mana domin zurga-zurga dukda ba kasafai muke fita ba amma tun farko dama ya hana mu tu'ka mota a wasu lukutan ma ya gwammace shi da kansa ya ja akan wata daga cikinmu ta ja
Ya taso da sauri tare da risinawa yana gaishe ni na amsa a gurguje domin ba na so Adam ya sake shigowa ya same mu ban san mai zan ce masa ba.
Cike da girmamawa ya ce." Hajiya za fito da mota ne?"
Kaina na girgiza a takaice na ce." A a.'' Ya biyo bayanmu da sauri Yana fad'in." Hajiya ki yi hakuri na kai ku don Allah" Ya k'arasa maganar a raunane. Na Dan dube shi sai ya ba ni tausayi sosai suke ko'karin ganin sun ri'ke aikinsu sam ba sa son abinda zai 'batawa ogonsu rai ko su sa'ba umarninsa.
Na ce." Yi sauri to." Da dan gudu ya nufi wurin da motocin suke ya fito da daya da gaggawa har zuwa wurin da muke tsaye.
Kamalu ya bude mini na shiga na zauna kafin ya dubi Yusi cike da tsare gira ya ce." Malam shiga mota.'' Ya shiga ba tare da ya ce masa komai ba sai da akwai damuwa Mai yawa a tattare dashi don sai waige-waige yake yi.
Sai da muka hau titi sosai hankalina ya kwanta domin ni kaina ina jin nauyi da kunyar yaron ina kuma fargabar ya zo ya riskemu ba zan iya ce masa tafiyar ba zata yiwu dashi ba.
"Hajiya Ina muka nufa."
Muryar Masa'udu ta katse tunanin da nake yi. na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Kai mu jabi park."
Cike da bin umarni ya ce." An gama.
Motar ta yi shiru ni da yaran duka muna cike da zullumi mussaman Yusi da nake hankalce dashi yana goge hawaye a fakaice. Ban tsawatar masa ba domin kuwa ban san mai yake ji a zuciyarsa ba, amma zahiri wannan shine iya gatan da nake ganin zan yi musu a duniya. Ba zai yiwu a ce koyaushe rayuwarsu ta kasance cikin kyara da hantara ba. Sun fara kaiwa munzali na girma a wannan lokacin ya kamata ace mun had'u ni dasu mun gina gobe dalili watarana za su yi aure su tara iyali suma. Sannan zuciyata ba za ta iya cigaba da jurar ganinsu cikin kaskanci ba, arziki Allah ne yake bayarwa su fita su nema kowa ya tsaya da k'afafunsa.
Cikin ikon Allah motar dana sanya su ta yi lodi saura bai fi mutum hud'u ba. Cike da dauriya da ko'karin kara musu kwarin gwiwa muka yi sallama na ce lallai idan sun sauka Kamalu ya kira ni.
Ban gushe daga wurin ba har sai da na tabbatar da tashin motarsu sannan na sauke ajiyar zuciya na gyara zaman nikab din da yake fuskata kai tsaye na nufi wajan da Masa'udu ya ajiye mota.
Yana ganina ya taso daga inda yake ya bud'e mini na shiga na zauna sai a lokacin na ji wasu gagariman hawaye masu radad'i sun k'wace mini. Wato ni kuma haka kaddarata take, ina ro'kon Allah Ya ba ni ikon cinyeta ya kuma saukakawa yaran nan rayuwa ya basu hakurin maraici.
Ina komawa na samu Hajiya maryam da Hauwa a falo suna d'an hira jefe-jefi amma yanayin fuskokinsu kadai shi zai tabbatar maka da cewa zuciyoyinsu babu dadi.