← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 43

Sashe 5

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 6 min read

"To ni kuma muddin a karkashin ikona ki ke yaran nan babu inda za su je muna tare har abada."
Na dube shi ina gyada kaina na ce." Haka ka ce ko?''
"Kwarai kuwa, haka na ce, sai ki yi duk abinda za ki yi tunda ke ba ki da fahimta."
"Zan kuwa yi, ai ba kai ka haifar mini su, baka da wani ji'bi dasu don haka baka da hujjar da zakace dole sai ka rikesu anan zan nuna maka karfin ikona."
Ya ce." Sai ki nuna din ina jiranki..'' Daga haka ya ja tsaki ya juya ya fita yana fad'in." Sakarai kawai kullum kina girma kina cin tasono."
Silalewa na yi a kasan d'akin na yi zaman dirshan na dinga tikar kuka. An dake ni an hana ni kuka kuma an bi ni da bakar magana. Wace irin masifa ce wannan mutum bai haifi yara ba ya ce lallai sai ya rike su.
Ina cikin wannan yanayin Hauwa ta shigo sanye da hijabi a jikinta idonta jawur! Na tashi tsaye da sauri Ina kallonta gabana na fad'uwa. Minal ta dire mini a gabana tana fad'in.'' Ga takwararki nan Amina ubanta ya ce na tafi gidanmu."
Cikin kad'uwa da muguwar fargaba na ce." Ki tafi gidanku akan wane dalili Hauwa?"
"Saboda na gaya miki magana." Ta fad'a tana juyawa da niyyar fita. Na bita da sauri yayin da Minal din ta tawo kataf katafi ta rike gefan hijabinta tana kuka. Na ce." Shine kuma ke sai ki tafi."
"To dama ai kamar akan 'kaya nake wallahi na gaya miki a gajiye nake." Na ce." Ita Minal din mai tayi miki to?"
"Cewa ya yi na ajiye masa yarinya."
Wani takaici ya yun'kuro mini lallai Alhaji Amadu ya mutu ya bar baya da kura. Iyalinsa na nema su tarwatsawa aminin nasa rayuwa. Na tabbatar da cewa ba kowane ya janyo wannan hayaniyar ba sai Salim.
Na ce." Yana ina maigidan?"
"Shi ya sani.'' Ta fad'a a takaice tare da sake nufar hanyar fita. Na ri'ke hannunta ina fad'in." Babu fa inda za ki je Hauwa."
Dariya ta yi irin ta takaici ta ce." Ai ba ke ki ke aurena ba Amina, maigida ya ce na fitar masa daga gida zaman me zan yi."
Jan hannunta na yi muka zauna kan gado na sau'ki Minal na d'ora mata a cinyarta sannan na d'auki wayata. Kiransa na yi bugun farko ya d'aga kamar yana jira.
Na ce." Yanzu kai don girman Allah ba ka ji kunya ba, tsofai tsofai da kai kake aikata irin abun yara?"
"Mai na yi kuma? Ke ba kya jin nauyin furta mini maganar da duk ranki ya so ko Amina?''
Na ce." Hauwa dai ko babu aure tana da 'yancin zama na dindindin a gidanka, to balle bayan wannan alakar akwai ta aure da zuria a tsakaninku, da ka ce ta tafi gida kai ba ka ji nauyi ba?"
"Bata da wani 'yancin zama a gidana sai na so, tunda ba ta ji nauyin shure maganata ba, ni ma babu wani nauyinta da zan ji, kuma ina ruwanki matarki ce?"
'Dan sassautawa na yi domin kuwa ba zan so a ce dalilina sun samu matsala ba. Na ce." Idan saboda ta gaya mini wannan maganar nan ya sanya har ka yanke mata wannan hukuncin ka yi hakuri ka ji."
Shiru ya yi bai ce uffan ba. Na ce." Ka janye abinda ka kudirta akanta domin kuwa sam bai dace ba."
"Kin yarda ta yi ba daidai ba yanzu?"
Shiru na yi ban ce komai ba. Ya sake maimaita maganarsa nan ma ban ce masa komai ba. Ya ce." To tunda bakinku daya kin ga kuwa babu amfanin zama da macan da bata buk'atar zaman lafiya da kwanciyar hankali. Hauwa kawai ta tafi gidansu kafin na gama yanke hukunci ta san matsayinta."
Gwiwa a sanyaye na kashe wayar ina kallonta babu damuwa a tare da ita tace." Ai na gaya miki Amina mutumin nan kaf dabi'unsa sun canza muddin akan lamarin matarsa ne yakan iya cin mutuncin kowa."
Na ce." Babu da inda za ki je." Ta yi shiru tana kallona ina laluban wayar Hajja bugu daya ta daga. Cikin rawar murya na gaisheta ta amsa tana fad'in duk kuna nan lafiya ko Amina."
Na ce." Lafiya lau Hajja don Allah ki yi masa magana matsala suka samu da Hauwa shine ya ce wai ta tafi gida."
cike da mamaki ta furta." Hauwa ta tafi gida akan wane dalili?"
Shiru na yi ban ce komai ba.
Cike da kulawa ta ce." Amina ki gaya mini menene yake faruwa kin ji ko kada ki rufe mini komai.''
Hawaye suka silalo mini na ce." Hajja Hauwa ba ta yi masa komai ba wallahi, asalima ma matsalar ni ta shafa saboda kawai ta gaya masa gaskiya shikkenan yake jin haushinta."
Ta ce." To gaya mini wace matsala ce, ni zan yi maganinta, Hauwa kuma ki gaya mata kada ta fito."
"In sha Allah, gata nan a kusa da ni, na hana ta fitowa."
"To hakan ya yi ina sauraranki." Tafad'a cikin nuna damuwa. A nutse na fara gaya mata tun daga farko abinda yake faruwa har zuwa yanzu da ake wannan rikicin.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 103
Hajja ta jima cikin alhini da takaici kafin ta ce." Ki yi hakuri a matsayinki na babba kuma uwa. Amina tabbas ko ba ki fad'a ba nasan idan za a tona zuciyarki to tanan cikin kunci da b'acin ran wannan lamari. Ki jure lallai kuma ya zama dole a yi wa tufkar hanci saboda gudun abinda zai afku anan gaba na rashin dadi. Zan nemi shi zai kuma zo nan inda nake akan maganar nan domin ni kaina ban yarda da hakan ba. Sannan duk abinda zai yi muku kada ku saurareshi. Ki jadaddawa Hauwa cewa da yawuna ban amince ta fito ba. Ke kuma ki yi hakuri kin ji ko, nasan abinda da ciwo a zucci amma in sha Allahu gaskiya za ta bayyana halinta."
Cikin ko'karin danne damuwata domin kada ta ga kamar ban ji nasiharta ba na ce." Shikkenan in sha Allahu Hajja za mu yi yadda ki ka ce din, Allah Ya saka da alheri."
Ta amsa da "Amin." Cike da damuwa muka yi sallama. Na dubi Hauwa tare da cewa." Kin ji yadda muka yi da ita ko?"
A sanyaye ta ce." Na ji, amma kin san Allah wallahi ba na so na bude ido na ga mutumin nan Amina, wani irin haushinsa nake ji." Na ce. Ki daure zuciyarki, kuma duk abinda zai yi miki kada ki kula shi."
Shiru ta yi ba ta ce mini komai ba tana ta girgiza kafarta.
Cikin raina na ce Hauwa ita ma ba lefi yar bala'i ce.
Haka muka wanzu a d'aki muna tattauna matsalar da yadda za mu maganceta.
Chapter 5 · 0% Book details