Sashe 32
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Misalin goma da rabi maigidan ya shigo tare suke da Kamalu ban yi mamakin ganinsu su biyu babu Yusi ba domin sai na ce ganina da Yusi daya kafin a d'auki gawar marigayiyar na hange shi tare da Adam a rakube a bayan kujera. Yanzu ma su Hajja da Gwaggo sai tambayarsa suke yi ina jin Kamalu na basu amsa da cewa yana can tare da Adam. Maigidan bai tsaya ba suna gaisawa ya haye sama hankalina gabad'aya yana kansa don haka ban yi jinkirin bin bayansa ba.
Na same shi zai shiga wanka da babban towel a jikinsa.
Muka zubawa juna ido. Na isa dab da shi na tsaye a sanyaye na ce." Ya karin hakuri tun d'azu nake ta so na yi maka gaisuwa ban samu dama ba, Ubangiji Allah Ya gafarta mata, kai kuma Allah Ya baka hakurin jure rashinta, Allah Ya albarkaci abinda ta bari."
Ya dinga amsa da "Amin Ya Allah cikin jin dadi. Ya nufi bandakin na bi bayan shi na taimaka masa wurin had'a ruwan wanka. Kallo yake ta bi na dashi babu yabo babu fallasa, amma kallon ya fara sa'bata sai na tsargu na fara tunanin ko shima ya fara yarda da abinda 'yan uwanta suke fad'a akanmu. Da na tuna kallon nasa babu harara da kyama a ciki sai na d'an samu sassauci, na fito na bar shi a bandakin domin ya yi wankan. Na zauna jigum cikin zullumi.
Ya fito yana tsane jikinsa na tashi da sauri na bude wardrobe dinshi jallabiya na fito masa da ita da gajeran wando. Na mika masa ya kar'ba na koma na zauna yana kintsa jikinsa ya ce." Ki kawo mini abinci Amina."
Da sauri na mike ina fadin." Dama abinda zan tambayeka kenan, tun yamma na ce da Baba Tabawa ta yi towo zai fi dadin tafiya."
A takaice ya ce." Kin kyauta kuwa."
Ya d'auki turare yana fesawa a jikinsa. Na sauka kasa cikin nazarin abinda ya yi a ganina wane turare zai fesa a cikin wannan yanayin da matarsa ta rasu ko kwana daya ba ta yi a kabarinta ba
Na koma saman da tire a hannuna mai d'auke da kwanonin abincin da duk abinda nasan zai buk'ata. Yana zaune gefan gado
yana waya da Sukairaju na ajiye tiren hannuna a saman daddumar da yake zama domin cin abinci...
[12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: 118*
Sai da ya kammala wayar tsaf tukkuna ya zo ya zauna saman daddumar da abincin yake a shirye. Na zuba masa guda biyu madaidaita ina ko'karin zuba miya ya furta." Wanene zai cinye miki wannan towon Amina?"
Na dube shi a tsanake kafin na ce." Kai ne za ka cinye?" Sai ya gyada kansa yana fad'in." A a d'aya ya ishe ni, kada ki zuba miya a kai a b'ata shi ki yi addu'a dayan ma na iya cinye shi."
Ban ce komai ba na cire dayan na mayar cikin fulas na fara ko'karin zuba miyar ya ce ki zuba ta yau'kin kawai kada ki sanya mini jar miyar, ki sanya mini man shanu akai wadatacce."
Na yi yadda ya umarta Ina fad'in." To naman fa." Ya ce." Ki tsamo sai ki sanya mini."
Ban ce komai na dinga tsamo naman ina zuba masa a saman towon har ya so yayi yawa." A nutse ya ce." Naman nan ya isa haka Amina, kina so na ci abinci jikina ya mutu ko?"
Na girgiza kai a hankali na ce." Kallo d'aya na yi maka d'azu na tabbatar da cewa akwai yunwa a tattare da kai wallahi."
Ya furta." Ba ki yi karya ba rabona da abinci tun yammacin jiya kuma ban wani damu ba wallahi."
A nutse na ce." To yanzu dai ka daure ka cinye wannan har naman duka."
Hannunsa ya sanya tare da bismillahi kafin ya ce." To ke ma sanya hannunki mu ci tare zai fi albarka.
Na sanya hannuna a hankali na gutsiro na kai daidai bakinsa.
Kallona ya yi na 'yan sakkoni kafin ya bud'e bakin na sanya masa towon ya fara taunawa a tsanake
D'akin ya d'auki shiru na wani lokaci kafin na ji maganarsa yana fad'in." Ina mai sunan abokina lokaci bai ba ni damar ganinshi ba ina fatan baya tare da matsala ko?"
Jim na yi Ina nazarin maganarsa can kuma na fahimci abinda yake nufi. Na ce." Lafiyarsa lau yana can wurin Baba Tabawa itace take d'awainiya dashi, alhamdulillahi babu wata matsala yanzu idan ka kammala cin abincin sai na kar'bo maka shi."
Ya ce." Na gode muku sosai na kuma yaba da ko'karinku Allah Ya saka da alheri."
'Dan tausayi ya ba ni domin yanayin yadda ya yi maganar ya nuna mini cewa ya ji ciwon abinda Hauwa ta yi kuma abin ya dame shi abubuwa ne da yawa suka yi masa dabaibayi. Ta bakin Hajiya Saratun Hauwa ko a waje ya aurota bai kamata ta yi wannan sakarcin ba. Yaro
d'anyar haihuwa ta ajiye saboda wani banzan dalili.
Na ce." Ni kam banga abin godiya ba duk abinda na yi maka ai kaina na yi wa."
Ya yi shiru bai ce komai ba yana dai ta kar'bar towon da nake bashi a baki har guda ya kusa k'arewa ya ce." Ban ga kin ci ba."
"Na ce." Sai ka koshi my love dina." Ya sa dariya wadda ban yi tsammani ba yana fad'in." Na ga sai wani ji ki ke da ni Amina."
Da d'an murmushi na ce." Tausayi ka ba ni." Ya gyad'a kansa da wani irin murmushi kwantacce a a tare dashi ya cinye malmalar towo daya na kara cire wani daga leda ba cigaba da bashi bai hana ni ba. Jefi jefi muna d'an ta'ba hira mafi rinjaye kan marigayiyar ne. Da kyar na daure na soko maganar da take ta damuna na ce." Akan lamarinka da Hauwa dukda ba ni da hurumi akai amma a shawarce don Allah kada ku bawa shaidan damar da zai shiga ya dagula muku zumunci domin na lura abinda ta aikata ya b'atawa mai sunan Mamana rai, ku yi hakuri a dubi zumunci da zuri'ar da ta ratsa a daidaita."
Ya gyada kansa yana fad'in." Ki yi mana alkalanci Amina tsakaninki da Allah abinda Hauwa ta aikata ta duba mini? Ko kuwa ta duba zumuncin da kike magana akai. Da ba ta samu sararin zubar da cikin ba sai ta haihu ta tsallake abinda ta haifa saboda tsabar rashin Imani da rashi mutuncin ta gudu ta bar shi, kin ga fassarar ai ba ta shirya rayuwarsa a tare da ita ba tunda ai abincinsa yana jikinta idan ya mutu bata da asara saboda ta gane ni abinda na fi buk'ata kenan a yanzu taruwar iyali to bari ta yi amfani da wannan damar wurin ganin ta b'ata mini rai, kada ki so zuciya Amina lefin da na yi wa Hauwa ai ban cancanci wannan rashin mutuncin ba." Ya kare maganar cikin wani irin yanayi na damuwa da b'acin rai."
Na yi shiru ina jajantawa. Babu shakka ko kaffara ba zan yi ba Hauwa tana can bauchi ne amma ruhi da zuciyarta suña nan dalilin abinda ta bari. Soyayyar d'a da uwa sai Allah. Ita kanta tana can Amma hankali da tunaninta na nan, ita a iya tunaninta hakan da ta yi shine zai sanyayyar mata da zuciya ta kuma k'untatawa wanda ya 'bata mata. Ko yana da lefi abinda ta aikata a yanzu ya shafe lefinsa nata za a yi ta hange kenan ta 'bata daya goma ba ta gyaru ba. Shiyasa masu karin magana suke fad'in." Duk abinda namiji ya yi ado ne mace idan tace za ta yi zai zame mata damuwa.
A sanyaye na ce." Ba ta kyauta ba gaskiya ni ma raina ya b:aci sosai kuma na kira ta a waya na gaya mata ta yi kuskure domin har cewa na yi zan kawo mata yaron ta yi tsalle ta dire ta ce ko na zo na yi a banza, dalilin da ya sanya ni yanke shawarar kiran Dr kan ta zo ta ga yaron domin ta dora shi akan abinda ya dace. Alhamdulillahi kuma yau kwanaki tara yana cikin koshin lafiya domin daidai gwargwado Baba Tabawa na kula dashi." Na yi shiru kafin na sauke ajiyar zuciya na cigaba da fad'in." Don Allah ka yi hakuri na ari bakinta na ci mata albasa wallahi ta yi kuskure amma kada ka dubi hakan ka ture ka dubi dangantaka da kuma yaranku, sannan kaima ka gyara wasu abubuwan da kake yi Wanda bata so."
Ya ce." Me na ke yi Amina, ni fa Samira na ce inaso ba Hauwa ba, zan gaya miki wata magana wadda ba ki santa ba har yau na kasa mantawa da matata ta fari Allah Ya jikanta domin soyayyar gaskiya ce a tsakaninmu. Ban ta'ba kallon Hauwa a madadin da za ta share mini kukan rashin Samira ba, kuma ban ta'ba yi mata kwatankwancin son da nake yi wa Samira ba. Idan na rabu da ita babu wata tangarda da zan samu tunda ni nasan bata da wani gurbi mai girma a zuciyata don haka wannan maganar mu barta kawai Amina."