← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 43

Sashe 39

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ya shirya tafiya legos kuwa bai nemi tafiya da kowa ba. Ya dai gaya mana tare za su tafi da Salim. Hakan bai wani dame mu ba. Akan tafiyar da zai yi babu wata daga cikinmu. Na gaza dai ha'kuri na ce ban yarda ba zan bi shi, domin a lokacin sai shaidan ya fara raya mini wani abu." Wata'kila an daura auransa da Nabila ya boye mana shiyasa bai nemi wata ta daga cikinmu ba. Zai d'auketa su lula can nesa domin su ci amarcinsu hankali kwance.
Na tubure lallai sai na bi shi fa. Abin ya dinga ba shi mamaki ganin yadda yake daga da ni a duk lokacin da zamu tafi na dinga zillezille kenan ina nokewa na ce wannan gobe na ce wannan. Yadda na tubure sai na bi shi haka Shima ya tubure ya ce bai shirya tafiya da kowa ba dalili aiki ne zai kai shi mu zauna kawai ya ma canza tsari ya daina tafia damu shi kadai zai dinga tafiya abinsa
Wannan maganar tasa sai ta kara haska mini hanya a daran ranar muka dinga rigima tun Yana biye mini da ko'karin mayar da abin wasa har dai ya bud'e wuta tunda maganganu na dinga saki masu zafi. Har yana fad'in ban isa na hana shi auran nabila ba idan ya yi ra'ayi kuma Hakan ma da nake yi ya kwadaita masa sha'awar auranta. Na ci kuka na koshi yadda ban rintsa ba haka zalika shima bai rintsa ba. Da asuba na sauka kasa raina a dagule gari yana yin haske na kira Hajja a waya duk abinda yake faruwa na gaya mata da irin zargin da nake yi domin kuwa shi abin zargi ne tunda yana yin wasu abubuwan a dukunkune. Ya za a yi a ce zai tafi Legos tsayin watanni shida babu mace a sanin da na yi masa mabukaci ne kwarai idan ba da wata a kasa ba.
Ta yi mamaki sosai ta dinga fad'in itama bata san komai ba amma lallai zata bincike shi kuma tilas ya gaya mata gaskiya idan ma da maganar auran to zata rushe tunda ba ma sonta amma ba zata hana shi ya nemo wata ba muddin ta kwanta mana.
Maganganunta sun dan sanyi mini sasaauci a raina. Wallahi tallahi itace rantsuwar musulmi Nabila tana zama matarsa na bar gidansa har abada domin ba zan iya kunsar wani takaicin ba bayan wanda na kunsa a baya. Yanzu wanene yake irin wannan kishin jahilcin babu burin zaman lafiya a tattare da ita. Zan kuma nuna mata iko da k'arfina akan wanda take yi wa fafutuka karyar banza take yi. Ya nemo wata da ba mu sani ba kamar yadda hajjan ta fad'a amma ban da Nabila.
[12/26, 7:56 PM] bintaumarabbale: *122*
Da ya dawo da daddare duk da girkin Hauwa ne bai iya ha'kura ba ya kira ni a waya. Dama na yi shirin hakan, sai a lokacin ne ma Hauwa ta san abinda yake faruwa domin a saman na sameta tana had'a masa abinci. Na yi zaton zan same shi cikin b'acin rai domin nasan babban abinda ya tsana shine a kai kararsa wurin mahaifiyarsa. Sai naga akasin haka. Na gaishe shi ya amsa yana kallona kafin ya nisa ya fara da ce wa." Yanzu Amina duk irin titsiyar da ki ka yi mini anan ni dake bata gamshe ki ba har sai kin sanar da mahaifiyata saboda rigima na gaya miki babu wannan maganar amma kin 'ki aminta da maganata na gaya miki ba na sha'awar auran Nabila ko kad'an a cikin raina wallahi amma irin wannan iyashegen da kike yi mini ya sanya nake so na aurentan sai na ga iya gudun ruwanki."
Hauwa ta dago a slow da tashin hankali tana dubanmu ni dashi domin daka gani maganar ta dake ta kwarai da gaske.
A nutse na furta." To ai ga hanya nan Nabila ta shigo gidanka Amina kuma ta yi waje shikkenan karshen zance domin na riga na yi wa kaina alkawari babu wata mace da zan zauna ta dasa mini kunci da takaici akanka. Abinda nake nusashka anan shine itafa ba don komai take yun'kurin shigowa rayuwarka ba saboda mune abubuwa masu kyau da marasa kyau sun faru a baya kowa ya kar'bi kuskuransa ya kuma gyara wallahi idan da zummar son zaman lafiya take cuso kanta gare ka bai dame ni ba, yadda take nunawa tana so ta zo ta ramawa 'yar uwarta abinda aka yi mata shine abinda yasa na tsaneta."
Dariya ya sanya kawai Bai ce komai ba ya fara cin abincinsa bayan ya yi Bismillah.
Hauwa ta tsaya daf da ni tana fad'in." Wace Nabila wai?" A tak'aice na ce" Kanwar Momi mana abokiyar rigimarki.''
Ta yi jim tana kallona kafin ta juya kansa tana fad'in.'' Yanzu don Allah kai sai ka auri wannan karuwa ce fa babu wanda bai san tana bin maza ba, duk ga mata nan a gari."
Ya dube ta da mamaki yana fad'in." A a Hauwa wannan kaifin bakin naki shine yake jefa ki a matsala, ke yanzu za ki iya rantsewa da Allah kin ta'ba ganinta tana zina, irin wannan kazafin fa yana da wahalar warwara Hauwa."
Na ce." Ai ba ita ta fara fad'a ba kaima ka fadi hakan idan ka manta na tuna maka da bakinka ka ce ba zaka iya auranta ba saboda kana zarginta da biye biye."
Hankalinsa a kwance ya ce." Ni ban ce ina zarginta ba, nasan dai na ce ba zan iya auran bazawara ba saboda Ina da kishi."
Ban san lokacin da da maganar ta subce daga bakina ta fito ba na ce." Ai ka iya 'karya da lauya zance dama."
Ya kalle ni da saurin gaske yana cud'e fuskarsa ya ce." Ni ne makaryacin." Share shi na yi tare da juyar da kaina.
Hauwa ta furta." Allah Ya taimaka mu ajiye duk wata magana mu yi wadda take da amfani ya kamata fa dole ka so abinda muke so domin zaman lafiyarka, a gaskiya ba mu yarda ba."
Ya kai lomar abinci bakinsa a tsanake ya ce." Ai ba ku biyo hanya ba, duba fa ki kun yi mini kerere a kai, kuna so ku tursasani ne, ai muddin ni nake auran mace tana kasan kafafuna ban yi lalacewar da za ta gindaya mini sharadi ba. Ba zan auri Nabila ba in dai a son raina ne wallahi babu soyayyarta ko kad'an cikin raina. Ku kwantar da hankalinku don Allah, mu rabu lafiya."
Na ce." Idan gaskiya ne to zan shirya mu tafi Legos din tare."
Ya girgiza kansa yana fad'in." Ki huta kawai a gida zan tafi ni kadai shawara na canza, Kuma zan kula muku da kaina sosai in sha Allah."
Don dole muka ha'kura da abinda ya yanke amma har zuwa ranar da zai tafi zuciyata bata aminta da maganarsa ba. Ilai kuwa bayan tafiyarsa da kamar minti talatin tawagar yaransa da suka yi masa rakiya zuwa airport suka dawo amma banda Sukairaju da Dahuru wannan duk inda za shi tare suke tafiya mussaman Sukairaju. Cikin wad'anda suka bi shi har da direbanmu Masa'udu da ya shigo kawo kular dake zuba musu abinci abinci kamar wanda aka sanya wa batiri ya tsaya suna hira da Baba Tabawa da yake mutuniyarsa ce yake gaya mata a cikin masu rakiya har da Hajiya Nabila domin da motarta ta tsaya a kan hanya shine ma ya daukota ya dawo da ita gida.
Mamaki ne mai yawa ya kamani. Har ya juya zai fita na dakatar dashi tare da tambayarsa abinda yake cikin raina. Ya ce." Eh kwarai kuwa ba tare suka tafi ba yanzu haka ban jima da sauke ta ba ta shiga gida, amma dai Yallabai din tare suka tafi da Salim."
Na gyada kaina a nutse na ce." To shikkenan je ka kawai." Ya fita da sauri ita kuma baba Tabawa ta shiga kicin. Hauwa tana d'akinta Bata fito ba. Na yi yun'kurin tashi kenan Baba Tabawa ta fito daga kicin ta zauna kusa da ni tana fad'in." Hajiya Amina akwai abinda na fara fahimta da matar nan Nabila."
Na dube ta amma ban ce komai ba zuciyata tana can tunani. Me yasa mu bai bari mun yi masa rakiya ba ita ya gayyaceta, wannan amsar kawai nake son sani.
Ta furta." Ba na yi wa Yallabai sha'awarta ai ya yi rashin mata sai da mu ce Allah Ya gafarta mata, amma dai wannan tana tattare da matsaltsalu masu yawan gaske."
Na gyada kaina a d'an sanyaye na furta." To yadda dai yake gaya mana duk abinda take yi bai sani ba domin dai babu sha'awar auranta a tare da shi, amma kin san makirci da dadin baki na maza Baba Tabawa za mu iya sakin jikinmu wataran katsam mu ji gud'a, ba mu da yadda za mu yi. Kin ga sai ya sake zuwa ya raina mana hankali ya ce. " Kaddara ce ko ya kawo mana wata hujja ya ce ga dalilin da ya sanya ya aureta "

Ta girgiza kanta tana jimantawa domin ita da ta fi mu yawan shekaru ma abin ya tsaya mata a rai. Hauwa ta fito ta same mu muna tattauna maganar. Taja tsaki kafin ta dube ni a nutse tana fad'in." Amina don girman Allah ki kyale shi ki daina damun kanki wallahi nasan ko ya aureta da wuri gayyar za ta watse shiyasa ban damu ba. Ki daina damuwa haba Nabilan me bagidajiyar banza da wofi."
Murmushin takaici kawai na yi cikin raina na ce magana kam na bar ta shima na daina nuna masa damuwata a fili amma ina nan na kudire abu a raina.
Chapter 39 · 0% Book details