← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 43

Sashe 28

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kwana daya biyu har uku ban ji daga gare shi ba. Gabad'aya ma yau kusan kwanaki biyar kenan rabon da mu yi magana tun ranar da na sanar dashi haihuwar Hauwa ban sake ganinshi a online ba. Sai na fara trying din lambar da yake kirana da ita busy bata shiga hankalina ya d'an tashi domin tunda suka tafi bai ta'ba kwana biyu bai ta'bo ni ba.
Na gaza ha'kuri har sai da na sanar da Baba Tabawa halin da ake ciki itama ta taya ni zullumi tana ta addu'a Allah Ya sa lafiya ina amsawa da Amin.
Idar da sallar magribata kenan na d'auki wayata dake saman dirowa ba na iya minti ashirin yanzu ban bud'e data na duba ba. Cikin ikon Allah kamar iska sakonshi ya shigo. Amma kalmar Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un dana fara gani tun kafin na bud'e sakon shine abinda ya assasa mini 'barin jiki da kakkarwar hannu. Na bude gabana na bugawa da karfin gaske...
_"Allah Ya yi wa Maryam rasuwa bayan sallar la'asar ki sanar da duk wanda ya kamata Amina."_ Abinda yake rubuce kenan
Wani irin tsananin tashin hankali da d'imuwa na shiga Ina daga zaune na dinga jin tafin kafata na wani irin yammm! Hannuna da ke ri'ke da wayar ya sandare wayar ta fad'i saman cinyata. Ni kaina saukar hawaye na ji a saman dakalin fuskata suna kasa tsare da babban sauti na furta." INNALILLAHI WA'INA ILAIHI RAJI'UN! Allah Ya jikanki Maryam, Ubangiji Ka yafe wa baiwarka, ashe ciwo ba na tashi ba ne."
Wani mahaukacin kuka mai gunji ya taho mini a guje! Na sanya tafin hannuna na toshe bakina ina fad'in." Mun shiga uku a wannan duniyar da bata da tabbas Ya Allah!!"
Wayar na laluba da saurin gaske tabbas wannan shi zai zama izna ga Hauwa ya nuna mata cewa babu abinda yake cikin wannan duniyar face rikici da firgici tashin hankali da rashin tabbas
Bugu d'aya wayar ta yi ta daga cikin kukan da na kasa jimirin danne shi na ce." Hauwa Momi ta rasu d'azu da la'asar yanzu nan maigidan yake sanar da ni....
[12/17, 7:36 PM] bintaumarabbale: *116*
Cike da rikicewar murya ta furta." Wac...wace Momin kike nufi Amina?"
Yadda ta fad'i maganar shi ya tabbatar mini da cewar a ki'dime take... Na ce." Momi dai da kika sani matar mijinki Hajiya Maryam."
Dif ta yi sai sautin shuhhh! ne yake tashi a kunnana. Na daga wayar na duba tana ta tafiya. Sunanta na kira ta amsa a sanyaye "Na'am. Na ce." Ki sanar da inna Uwani halin da ake ciki Hauwa kin ga dai duniyar ko ita kenan fa."
Ta yi shiru dai bata tanka ba. Na ja ajiyar zuciya ina jin yadda wani kutittiran abu ya tokare mini a wuya ba komai ba ne face damuwa da tsananin kidima da tashin hankali.
Jin ta yi shiru ba ta ce komai ba sai kawai na datse kiran na nemi lambar Hajja domin ba na tsammanin ta san da rasuwar tunda a sa'kon da ya rubuto mini ya ce na gayawa wanda ya dace.
Sosai Hajja ta gigice da ta ji labarin rasuwar dan har sai da na yi dakacen sanar da ita tunda ita kanta ba ta da koshin lafiya. Kasa jimirin sauraran kukanta na yi na datse kiran hannuna na rawa na ajiyeta saman cinyata hawayen suka sake zubo mini a saman fuska. Hannu nasa na sharce na sake saukar waya a karo na uku anti Yagana na kira na sanar da ita domin ta gaya duk wanda ya dace a yi jana'iza da shi. Na kira Babanmu na sanar dashi shi ma ya tabbatar mini da cewar za su kamo hanya gobe da sassafe shi da Baba Sule.
Jiki a sabule na fita falo baba Tabawa tana d'akinta sai na bita can. Na sameta ta ninke kayanta ganin yanayina ya sanya jikinta mutuwa. Rashin kwarin kafafuna ya sanya ni zubewa gabanta na furta." Baba Tabawa Momi ce ta rasu fa?"
"Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Kalmar da ta fara furtawa kenan kafin ta tallafe ha'barta cikin alhini da tace." Baiwar Allah nan ashe ciwo ba na tashi ba ne." Hanci na ja tare da furta " Baba tunda ranar da muka je duba baiwar Allah nan wallahi hankalina ya kasa kwanciya haka kawai daga ta fad'o mini sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi ciwon nan nata ya tsaya mini a rai na sosai."
Ta girgiza kai cike da kasala ta ce." To a Amina abin ne da ban tsoro ga yanayin yadda hallittunta suka jirkice ba ke kad'ai ba ni kaina da ita nake kwana da ita nake tashi a rana wallahi Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya yafe mata, halinta nagari ya bita don arzikin Annabi."
Da "Amin na amsa tare da cigaba da nanata Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un domin samun nutsuwa da k'adaita Allah da kuma tabbatar da cewa gare shi muke kuma gare shi za mu koma.
Mun jima muna cikin alhini tare da tariyo kyawawan halinta kafin mu yi sallama babu batun cin abincin dare domin gabad'ayanmu babu wannan kuzarin a tattare da mu.
Ban ta'ba tsoron mutuwa ba sai a kan matar nan ni kadai a d'aki ta dinga yi mini gizo. Dana rintse idona sai na ga suffarta mussaman karshen ganina da ita lokacin da ta shigo yi manna sallama da za su tafi. Na cigaba da kiran sunan na d'auki waya na kira Sahura ganin kiran bagatatan cikin dare sai ta tsorata ta fara tambayata a ki'dime! Da kyar na iya gaya mata halin da ake ciki. Ita kanta sai da ta rude tana fad'in." Amina ban ta'ba ganin matar nan ba Amma wallahi mutuwarta ta gigitani. Ubangiji Allah Ya gafarta mata ya sanya karshen wahalarta kenan, mu Kuma da muka d'auki zunubinta Allah Ya yafe mana, amma ni kaina na jima da sanin cewar matar nan baiwar Allah ce duk kazafin da wasu daga cikin mutane suke yi mata ba gaskiya ba ne, kin san haka siddan Ubangiji ba zai d'aukaka bawansa ba sai da jarrabawa. Allah Ya yi mata rahama.
Babu kuzari na ce." Amin suma Amin Sahura ni kaina a gigice nake wallahi a yanzu a cikin raina sai nake tunanin mai yasa na yi abinda na yi a baya dana sani na ha'kura kawai tunda duniyar guda nawa take. Zahiri matar nan alherinta na sani ban san wani sharrinta ba, domin idan zan bude baki na furta ga abinda tayi mini na rashin kyautawa wallahi na yi mata sharri Sahura, ba ki ki yadda nake ji ba a raina na tsorata da wannan duniyar gabad'ayanta. Ita kanta Hauwa tana can cike da gigita domin kasa magana ta yi da na kira ta a waya na sanar da ita wallahi sai kashe wayata na yi domin bakinta ya mutu murus ta kasa furta komai."
Chapter 28 · 0% Book details