← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 43

Sashe 26

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 5 min read

nema ya wuce makadi da rawa na ce." To sai ka tuntubeta idan ba ta da aure ka aurota ko?" Ya girgiza kansa yana ce wa." A'a ai ba musluma ba ce addinin hindu ce." Na ce." To menene a ciki sai ka musuluntar da ita." Kansa ya girgiza tare da furta." A a, abinda ya sa ki ka ji Ina yi miki maganarta kamar da kuke yi da ita ne ya b'aci da gaske idan na ganta ina shiga yanayi na buk'atuwa sosai." Shiru na yi ban ce komai ba. Sai ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya furta." Ina nan dawowa my love za mu sha soyayya ko?" Na kashe idona tare da fad'in." Sosai ma irin wadda kake so za mu yi." Sai ya zuba mini idanuwansa babu kiftawa. Na kama dariya ina fad'in." Ka na ji kamar ka d'auko ni daga cikin wayar ko?" Ya gyada kansa yana lumshe Ido. Hakan ya sake jefa ni a damuwa da sha'awa na sauke ajiyar zuciya a kasalance na furta." Ni ma na yi missing din Baba Yallabai baban soyayya." Kafin ya ce wani abu kiran da aka yi masa a wayar ya katse video call din. Na kashe wayar tare da ajiyeta a gefe Ina sauke ajiyar zuciya gabad'aya hirar nan da muka yi ta tayar mini da hankali wani irin nake ji a jikina. Sai gefin magriba na fito falon daga cikin d'akin Hauwa na ji kukan yaron ya tsananta da saurin gaske na shiga d'akin na same shi kwance cikin net dinshi yana ta wutsil-wutsil towel ya toshe masa hanci. Da azama na zuge net din na d'auko shi fuskarsa ta yi jazur saboda da alama ya jima yana kukan. Na zauna gefan gadonta ina jijiigashi gabad'aya ya shid'e a tunanina tana bandaki na tashi tsaye dashi a kafad'ata na tsaya kofar bandakin Ina Kiran sunanta shiru bata amsa ba kuma babu motsin ruwa. Sai kawai na kutsa kaina ciki wayam babu alamunta. Da sauri na fito gabana na dan fad'uwa na tsaya ina rarraba idanuwana a d'akin ban ga alamun komai ba.. Na fita kai tsaye kicin na nufa Baba Tabawa ta kammala abinci dare tana gyara kicin din. Cikin kasala da sagewar gwiwa na furta." Baba ina Hauwa?" Sai kawai ta tsaya tana kallona kafin daga bisani ta furta." Ba ta dakinta ne Amina?" Na furta." Kwarai kuwa, fitowa daga d'aki kenan na ji kukan yaron nan koda na shiga d'akinta bata nan." Ta sanya hannunta ta kar'be shi a sanyaye ta biyo bayana muka tsaya a tsakiyar falon. Ina Hauwa za ta tafi to. Ni nake tambayar zuciyata dalili tunda ta haihu ban ga alamun fitina a tattare da ita ba asalima wani babin annashuwa da farinciki ta bud'e. Baba Tabawa ta sanya babban towel ta goya yaron ni kuma na d'auko hijabina na sanya na fita can harabar gidan. Daga nesa na tsaya Ina hangen securitys a bakin gate. Masa'udu ya shigo da mota ya ajiye a wurin da motocin suke ya fito daga motar ganina a tsaye ya sanya shi da sauri ya nufo ni. Ya risina yana gaishe ni na amsa tare da fad'in." Daga ina kake domin zuciyata ta fara hasashen wani abu. Kai tsaye ya furta." Daga airport nake na kai Hajiya k'arama ne za ta bi jirgi zuwa bauchi don haka na ji tana fad'a a waya kafin mu isa filin jirgin." Ba tare da na sake cewa komai ba na kada kaina na koma ciki gidan raina a masifar b'ace. Anya kuwa Hauwa tana da hankali ki haihu kwana biyu kacal saboda mugun abu ki gudu ki bar jaririn da ki ka sha dawainiya da wahala a kansa kafin ya zo duniya kici kwakwa. Da kuma d'aita irin ta haihuwa da rashin kwari a jiki Baba Tabawa ta dinga salallami tana fad'in." Wannan wane irin sakarci ne Hajiya Amina, to shi wannan din da ta tafi ta bar shi ai hakkinsa ba zai bar ta, ina ruwansa da abinda ya faru. Ban ce mata komai ba na shige na je na d'auko wayata layinta na dingi kira wayar a kashe na kira ya kai sau goma amma is switch off. Na zube saman kujera ina Kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!" Na jima cikin wannan yanayin kafin na d'auki wayata dake saman cinyata kai tsaye lambar dr Sailuba na nemo itace tsayayyiyar likitan da take duba ni a duk lokacin da na samu ciki mussaman cikin baby Nana ta taka muhimmiyar rawa kwarai da gaske. Abu na farko da zan yi shine samarwa da yaron abinci matsalar raino wannan mai sau'ki ne. Bayani na yi mata sosai amma ban sanar da ita cewa uwar yaron ce ta ajiye shi ba. Ba mu yi sallama da ita ba sai da ta tabbatar mini da cewa da kanta za ta shigo ta kawo mini duk abinda ya dace. Na kashe wayar tare da zubawa Baba Tabawa idanu tana ta faman safa da marwa a katafaran falon duk domin hillatar yaron da yake ta kusurkusur da alamun kuka. Sai da bacci ya d'auke shi tukkuna ta zo ta zauna a gefana tana fad'in." Ko a tarihi ban ta'ba ganin shashashar uwa irin Hauwa ba Hajiya Amina lallai ta gwadawa wannan yaro rashin Imani." Shiru na yi Ina nazari kafin daga bisani na furta." Tana so ta huce fushin abinda ubansa ya yi mata shine ta dire shi ta yi tafiyarta. Abin mamaki kuma ita da mijin nata jini guda ne mamansa ta cika nono ta bawa Mamanta wace irin zuciyace wannan." Kai tsaye ta ce." Zuciyar kafurai ce." Muka yi shiru cikin alhini kafin ta cigaba da cewa." Ita kanta na tabbatar da cewa wallahi hankalinta ba zai ta'ba kwanciya ba ciwon jiki da ciwon nono ma ya isheta. Murmushi na yi tare da cewa." Ciwon nono mai sau'ki ne a wurinta tunda likita ce tana da hanyoyin da zata magance abinta ciwon jiki kam zata sha ai haihuwa ba wasa ba ce." Haka muka kasance cikin zullumi da tararrabi har Dr Sailuba ta zo ta tafi muna zaune a falon cikin wani irin yanayi na mamaki da takaici.
Chapter 26 · 0% Book details