Sashe 12
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Ya ce." Mu zuba ni dake 'yar iska shege ka fasa zan ga karshen iyashenki."
Daga haka bai sake cewa komai ba ya dubi Baba Tabawa tare da ce wa." Ki had'o mini kan yaran nan ki biyo bayana da su. Da sauri cikin bin umarni ta ce." In sha Allahu ranka ya dad'e.
Ya juya ya fita da saurin gaske.
Na dubi Hauwa da mataccen jiki sai kuka take yi gabad'aya ta fice daga hayyacinta. Kafadarta na dafa ina fad'in." Sakin ki ya yi ne Hauwa?" Sai ta daga mini kai hawaye na silalowa ta ce." Kuma har abada ni da shi in sha Allahu." Ta wuce dakinta da sauri. Cikin sagewar gwiwa na bi bayanta ta shiga bandaki sai na zauna gefan gado har ta fito wanka ta yi ta fara shiryawa tana yi tana kuka. Na ce babu fa inda za ki je wallahi ai saki daya ne ki zauna ku daidaita."
Shiru ta yi mini ba ta ce komai ba kuma ba ta fasa shirya kayanta cikin akwati ba.
Na yi jigum da mataccen jiki, wato dai mutumin nan indai akan sha'ani na Momi ne baya ji baya gani, ai ban ta'ba tsammanin zai iya sakin Hauwa ba, a iya tunanina je ki gida ki huta kawai zai yi mata idan har an yi duba da matsananciyar dangantakar da take tsakaninsu. Duk kuwa da abinda za ta yi masa karfin zumunci da albarkar zuri'ar da ta ratsa tsakaninsu ba ta cancanci hukuncin saki daga wajensa.
Ina zaune zukud'un ina tunani lallai kamar maganar Hauwa da 'kamshin gaskiya ko dai matar nan ba a haka ta bar mutumin nan ba, yakan rufe ido ya yi cin mutunci ga kowa muddin aka ta'ba nasabarta ko wani abu da ya dangance ta .
Don kyautawa tabbas Hauwa bata kyauta ba ni ma a wurin na nuna mata rashin goyan baya, kuskure ne mai karfi kazafi ko tabbatar da abinda ba ka da shaida akai. Iyayen baiwar Allah nan daga ni har ita ba mu da masaniyar abinda ya kashe su. Mijinmu ta aura kawai bayan haka duka ba mu da wata ala'ka da juna. Wata'kila ita Hauwa ta jima tana bin 'kwakkwafi akan Momi din idan ba haka ba ta ina take samun irin wad'annan labaran masu muni. Tabbas idan gaskiya ne to momi abar gudu da kyama ce, idan kuma kishi ne ya rufe idon Hauwa ta kirkiro maganar ta fad'a bata kyauta ba ta aikata abinda ba shikkenan ba, amma a ganina a matsayinsa na namiji jagora mai nisan tunani bai kamata ya zartar da wannan d'anyan hukuncin ba.
Gabana ya buga da karfin gaske a lokacin da na tuna irin abinda yake kwance ciki ya zube na shure umarninsa nasa yara a mota ba tare da yawunsa ba. Idan ya sake ni akan hakan ba zan wani damu ba, ai na yi abinda na yi daidai gwargwado sai na ha'kura da auran ma gabad'aya idan na mutu na riski Yaya Aminu a matsayin matarsa ta aljanna tunda ban tafi da zargen igiyar auran wani ba.
Sai dai tsorona da fargabata shine ina shakkun ya sanar da Baban Saude domin kuwa yanzu shine yake tsaye akan al'amarina tun bayan sasancin da ya yi mana a shekarun da suka gabata. Kuma ba tun yau ba na lura da k'akkarfan zumunci da abotar da ta 'kullu a tsakaninsu. 'Bacin ran Baban Saude da tijararsa ita kadai nake gudu amma don ta kalubalen wannan mutumin baya damuna.
Jan kofar da Hauwa ta yi shine ya dawo da ni hayyacina na daga kaina da sauri na ga gilmar fitarta da akwati madaidaiciya. Da azama na tashi na bi bayanta Allah Ya sa falon babu kowa tunda ya kwashe yaransa Baba Tabawa Kuma tana dakinta. Na ri'ke akwatin ina fad'in." Baki da hankali Hauwa ina za ki je a wannan daran ki yi tunani fa a abuja ki ke."
Ta ce." Sai me idan a Abuja nake zan iya kwana a tasha a halin yanzu domin na yi rantsuwa ba zan kara kwana a wannan gidan ba."
Na ce." Ke ma fad'a kawai ki ke yi, an ji ya sake ki, amma ai gidan d'an uwanki ne kuma uban yaranki, sannan addini cewa ya yi idan an saki mace ta zauna a dakinta ta yi idda idan da sauran rabo mijin zai iya mayar da ita kafin kammaluwar iddar don haka babu inda za ki je."
Shiru ta yi tana kallona can kuma sai ga hawaye shaa! Murya a sarke ta furta." Wai saki Amina, ni mutumin nan zai furtawa saki ai ina ganin ko zai saki kowa wallahi ni ban cancanci hakan ba.
Murmushi na yi Ina nazarin maganarta, ashe shiyasa ta mike kafa take iyashege saboda tasan ta taka tudu biyu a iya wautarta duk iyashegen da za ta yi masa ba zai iya sakinta ko wani hukunci mai tsauri ba. Rauni da gajeran tunani shine abinda yake cutarmu mu mata amma duk inda muke tunanin akan sha'ani na maza wallahi mune a k'asa dalili Allah Ya hallicesu daban da hallitar mata. Kuma dai dole duk isa da kasaitar mace sai dai idan ba ta yi auran ba.
Ta nemi wuri ta zauna tana share hawaye na zauna gefanta a sanyaye na ce." Ke ma fa kina da laifi Hauwa tunda naga irin abubuwan da ki ke yi nasan lallai akwai abinda zai faru wanda gabad'aya ba zai yi mana dadi ba. Na sha gaya miki ki fita daga sabgarsa da matarsa idan ma tsuguna mata zai dinga yi babu ruwanki da su amma kin 'ki ji, kin ga a cikin igiyoyin auranki uku daya ta girgiza ita nata suna nan daram!
Sai ta rufe fuskarta da tafin hannunta tana kuka cikin jajantawa kanta ta ce." Sai na gayawa mahaifiyarsa wallahi."
Da sauri na ce." Aikuwa da kin da'bawa kanki wuka Hauwa, kin san ya tsani fa a kai shi k'ara wannan yana masifar 'kona masa rai, kuma dole Hajja ta bi ba'asin komai idan har za a yi adalci a lamarin dole ke ma a nuna miki rashin gaskiyarki. Kuma da yawa mutane za su ce kin shigar mini fad'a mun taru mun had'e mata kai muna azabtar da ita fassarar da za a yi mana kenan."
Ta bude fuskarta tana kallona ta ce." To yanzu ya ki ke ganin zan yi, ni da wallahi gabad'aya hankali yana gida na gama shirya tafiya Bauchi."
Na ce." Ki yi zamanki ki kyaleshi kuma don Allah kada ki sanar da inna Uwani kada sanadiyar hakan zumuncinsu ya raunana kin san mas'ala ta auran zumunci tana da wuyar sha'ani.
A sanyaye ta ce." Shikkenan ba zan gaya mata ba amma wallahi matar nan yadda ta sanya ya sake ni saboda ita sai na wulakantata."
Da mamaki mai yawa na ce." Wane irin wulakanci kuma Hauwa, don Allah ki samu nutsuwa gabad'ayanmu fa babu yaro, yanzu ke za ki gyara auranki da zumuncin da yake tsakaninki da shi, na gaya miki idan kina so ki samu nutsuwar zuciya don girman Allah ki fita sha'aninsa da matarsa."
Shiru ta yi ba ta sake cewa komai ba, ta dai sunkuyar da kanta kasa tana tauna lebanta tabbacin abin da ya yi mata ya yi mata ciwo a zuciyarta.
Sai wajejan tara da wani abu tukkuna muka rabu ta shiga d'akinta da zummar shan maganin ciwon kai ta kwanta dalilin kukan da ta ti'ka, abinci ma ni na bi bayanta da shi kafin na fito falo na zauna na ci nawa muna hira jefi jefi da Baba Tabawa wajan goma da rabi ya shigo Baba Tabawa da saurin gaske ta yi masa barka da shigowa ya amsa babu wata kyakyawar kulawar da yake yi mata domin mutuniyarsa ce sosai a wasu lukutan har barkwanci suke yi ita dashi amma abin mamaki ko yau ni ma ban ji dadin abinda ya yi mata ba.
Ta dube ni tana fad'in." Ni ma kuna nema ku shafa mini kashin kaji Amina, Yallabai kamar fa haushina yake ji duk yadda nake ko'karin ganin na gyara ku abin zai shafe ni.
Yadda ta yi maganar da alhini da damuwa sai ta ba ni tausayi da dariya na d'an yi kad'an kafin na daidaita kaina na ce." To ke ina ruwanki Baba, kawai dai ransa ne a b'ace shiyasa ki ka ga bai amshi gaisuwarki da kulawa ba, kada ki wani damu ai ba ki da lefi."
Ta yi shiru tana jijjiga kai har da tallafe ha'ba. Na yi dariya sosai Ina fad'in " Hajiya Baba Tabawa ta mu ta gargajiya."
Ta dube ni da yanayi na zullumi amma ba ta ce komai ba. Daga can barandar samansa na ji maganarsa na juya da sauri yana tsaye hannunsa zube a cikin jallabiyar dake jikinsa ya ce." Zo."
Na yun'kura na tashi da tahamidi da kuma addu'ar rinjiye wannan lokacin nake jira, na kuma ji dad'i da ba a ja dogon lokaci ba gwara a yi ta ta 'kare kawai.
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 107
Na d'auka idan na shiga d'akin zan gan shi a rikice cikin matsananciyar damuwa, abinda ya ba ni mamaki bai wuce ganinshi a zaune a gefen gado da waya a kunnansa yana magana cikin rarrashi da wata kalar murya wadda tun tsayin zamana da shi ban san shi da ita ba.
Jikina ya d'an shika kad'an amma lokaci d'aya ban bari ya fahimci raunina ba, na zauna gefansa hankali da jina yana kansa domin fahimtar da wa yake waya.
Kasa gane kowacece na yi domin da da farko na d'auka Momi ce sai da na ji yana kiran Maman Hanif tukkuna na yi tsai ina tunanin wacece wannan kuma. Tunani ya katse lokacin da na ji sautin maganarta cikin reshin kuka ban dai ji mai take gaya masa ba, amma gabad'aya yanayin yadda take magana shi ya tabbatar mini da cewa cikin tsananin b'acin rai take. Na dinga nanata sunan a cikin raina Maman Hanif domin na kasa gane wacece can nazarina ya hasaso mini Nabila kanwar Momi tabbas ita ce babban yaronta sunansa Hanif hakane yakan zo wurinsu Adam a duk lokacin da aka yi hutun makaranta.
Ajiyar zuciya na sauke na sake kai duba na gare shi ya tak'arkare yana ta rarrashi da ban ha'kuri na gyada kaina ina jimanta matsayin momi da alhalinta a zuciyarsa. Maganar abinda ya faru tsakaninta da Hauwa suke tattaunawa da 'kyar dai da jibin goshi da irin rausayar da kai da muryar da yake yi ya rarrasheta ta ha'kura tare da kudirin janye 'karar da suke ko'karin shigarwa akan Hauwa. Na ji dad'i dai da bai gaya mata irin hukuncin da ya yanke ba ba domin a yadda yake a zaburen nan abu ne mai sau'ki ya gaya mata cewa ai ya saki hauwa. Wasu lukutan kuma zurfin cikinsa yakan burge ni ya kuma yi masa amfani. Tabbas Hauwa bata kyauta ba, kuma ni ban ga laifinsu ba don sun ce za su kai ta 'kara matsalar kawai idan har aka bari hakan ta faru gabad'aya rayukan kowa ne zai b'aci shiyasa Annabi ya yi hani da tayar da masifa domin idan ta tashi kafin ta kwanta sai an d'auki wani lokaci.
Ya kashe wayar ya dube ni fuskarsa kadaran kadahan. Kafin ya yi gyaran murya ya ce." Ina alkawarin da muka yi ni dake ranar da baban Saude ya yi mana sulhu."
Kallonsa na yi kafin na ce." Wane alkawari muka yi?"
Shiru ya yi yana kallona kafin daga bisani ya gyad'a kansa ya furta." Kun kyauta ke da Hauwa, idan an ce kuna yi wa matar nan ganin kyashi ku ce ba haka ba ne, yanzu tsakani da Allah Amina daidai ne ku sanyo iyayenta da suke kwance a kabari ku zage su har ku jingina mutuwarsu da abu mafi muni shin kishi hauka ne?"
Shiru na yi ban tanka masa ba, zuciyata kuwa in banda tsalle babu abinda take yi.
Ya cigaba da ce wa." Maryam ba ta cancanci wariya da k'askanci irin haka daga wurinku ba, ke Amina idan har Hauwa za ta yi d'amarar cin mutuncin Maryam ni a nawa tunanin ke ba za ki ba ta goyon bayan ba dalilin kyakykyawar alakar dake tsakanin yaranku da kuma alherin..... Bai kàrasa ba na katse shi domin ji na yi zuciyata ba za ta iya d'auka ba.
"Ni 'yar sharri ce ko, kuma muguwace 'yar hassada da ganin k'yashi saboda ba ni da gata ko?" Bai ce mini komai ba. Sai na cigaba da ce wa." Ita Nabila ai sharri ta yi mini domin wallahi ban san menene yake tsakaninta da Hauwa ba hayaniyarsu kawai na ji Ina d'aki a kwance kuma babu yawuna duk abinda Hauwa take yi babu hannuna amma ban ce lallai ku yarda ba da kai da su ba, don girman Allah kada ku bari mu sha ruwa, ku turo mota mai cike da sojoji su tafi da mu."