Sashe 31
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 10 min read
Sai bayan la'asar tukkuna suka shigo da d'an yawansu duk muna zaune a babban falo. Maigidan tare da iyayenshi biyu 'yan uwan mahaifinsa da kuma Baban Saude Baba Madu da Babansu Fadila. Falon ya cika da sabuwar gaisuwa tare da yi wa juna ta'aziya. Ta mussaman suka yi mini gaisuwar na amsa yayin da nake jin cikowar ruwan hawaye idona. Ina jin Hajja tana tambayar Alhaji Haruna Hajiya saratu ya ce tana can gidan mai rasuwar tunda koda suka sauka nan ta shiga ba ta fito kuma har yanzu. Suna ta tattauna hirar marigayiyar yayin da maigidan ke sake basu irin wahalar da ta sha na jinyya farkon zuwansu asibitin a yayin da aka dora ta akan magani an ga sauyi sosai anga sau'kin ashe na tafiya ne, yana sake jadadda musu cewa ko ranar da zata rasu yini lafiya lau suka tashi ta ci abinci sosai kuma shi da ita sun jima suna hira irin wadda suka jima ba su yi irinta ba tun kafin kwanciyarta ciwo. Ya ce ya fita da zummar yin sallah ya dawo ya tarar da likitoci ce sun rufe kafin wani dogon lokaci kuwa rai ya yi halinsa.
Na daga kaina Ina kallonsa a yayin da yake basu labarin akwai alhini mai yawa a tattare da shi zahiri kuma yanayinsa ya nuna mutuwar ta dake shi kwarai da gaske kwarmin idonsa ya zurma fatar lebanshi ta bushe kamar wanda ya yi azimin shekara bai sha ruwa ba. Irin wannan yanayin ya shiga a lokacin rasuwar tsohon mijinta Alhaji Amadu da kyar ya dinga cin abinci. Yanzu ma ba na raba daya da biyu rabonsa da abinci tun da aka yi rasuwar kwana da yini kenan.
Gabad'aya sun jajanta sosai kuma kafin tafiyarsu sai da Baban Saude ya jagorancemu gabad'aya muka yi mata doguwar addu'a wadda take d'auke da surorin da ake karantawa mamaci. Yamma likis suka yi mana sallama gabad'ayansu har da Hamusu da Babanmu domin cewa ya yi shi ma ba zai zauna ba tafiya za su yi tunda sun yi abinda ya kawo su. Shi kansa maigidan ya so su kwana ko daya ne amma gabad'aya suka ki har da kawunan nasa. Hajiya saratu ce kawai ta zauna ta ce sai an yi sadakar ukku tukkuna.
Yallabai din ya bada umarnin mayar dasu Babanmu gida. su Baban Saude kuma dama a motarsa suke tafe. Sai bayan sun tafi tukkuna Hajja ta dinga fad'a wai mai yasa anti Yagana ba ta jagoranci Ummansu Hadiza zuwa gidan mai rasuwar ba.
Anti Yagana ta ce mata mantawa ta yi shiyasa ni kuma nasan ba haka ba ne ita da kanta ta gaya mini k'afarta ba zata sake taka gidan ba. Gaisuwar da ta yi wa maigidan ma ta isa ba sai ta je ta yi wa 'yan uwanta ba tunda dukkaninsu taron tsintsinya ba share ne.
Sai bayan magariba Hajiya Saratu ta shigo. Ina d'aki lokacin na idar da sallah ban ka ga tashi daga kan daddauma ba ta shigo.
Na saki fuskata sosai Ina fad'in." Mai sunan mamana ina yini?"
Ta zauna gefan gadona a nutse tana fad'in." Lafiya lau Yayata kuma diyata."
Na yi murmushi a hankali na ce." Ai tun d'azu aka ce kina can gidan marigiyar ina nan ina ta zuba idon ganin Momi."
Ta dafa kafadata tana fad'in." Ga ni na shigo ai Amina ya muka ji da hakurin Maryam lokaci ya yi Ubangiji Allah Ya gafarta."
Na amsa da "Amin Ya Allah." Cikin wata iriyar murya.
D'akin ya d'an yi shiru wanda ya yi daidai da lokacin da anti Yagana ta fito daga bandaki daure da alwala. Ta saki fuska tana fad'in." Hajiya kin shigo kenan?"
Ta ce." E wallahi Yagana ya gida ya yaran, ya muka ji da hakuri?"
Anti Yagana ta ce." Ha'kuri da godiya Hajiya Allah dai ya jikinta da rahama."
Da Amin ta amsa yayin da take sake dora hannunta a kafad'ata.
Anti Yagana ta d'auki daddauma da hijabi ta koma can gefe domin gabatar da sallar magriba.
Ta ce." Ai ni ban fito ba daga gidan ba sai da na gabatar da sallata tukkun." Na yi murmushi kad'an ban ce komai ba.
Sai ta ce." Amina akwai maganganun da nake so mu tattauna dake idan babu damuwa."
Cikin nutsuwa na ce." Babu damuwa Hajiya Ina sauraranki."
Ta sauke ajiyar zuciya a tsanake ta ce." Hajja ba ta jima da sanar da ni abubuwan da suke faruwa ba a gidan nan naku sai rasuwar Hajiya Maryam ta ratsa hakan sai ya kara ba ni kwarin gwiwar zuwa domin na ji komai daga gare ki, Amina da hankalinki za ki biyewa Hauwa da har yanzu ba ta san rayuwa ba, mai yasa kuka kasa bawa mijinku kwarin gwiwa da taimako wurin ganin ya rike amanar abokinsa. Jimawata gidan marigiya Maryam tana da dalili domin 'yan uwanta ne suka zaunar da ni suna wassafa mini irin zaman da kuka yi da ita da irin abubuwan da kuka dinga yi mata na rashin kyautatawa, idan har hakan gaskiya ne Amina ban tsammata daga wurinki ba domin kallon da nake yi miki kin wuce a ce a yanzu an zauna a nuna miki abinda ya dace idan Hauwa ta yi hakan ba zan musa ba dama na san halinta da na ji sunanki a ciki ne sai hakan bai yi mini dadi ba, mai ake gudu ne a zaman tare irin wannan fa, yanzu ina Maryam din take ta mutu ta bar duniya to mai zai sanya ba za mu yi hakuri da rayuwa ba. Ashe Hauwa har sai da ta yi sanadin da Tajo ya saketa saboda kuma bata da hankali ta tafi ta bar yaro jinjiri fisabillahi ina hankali da imaninta yake."
A nutse na dubeta tare da cewa." Mamana abubuwan da yawa sun faru masu dadi da akasin haka. Amma zan gaya miki wani abu da ba kowa ya san shi ba sai ni sai Ubangijin da ya hallice ni wallahi tallahi ban ta'ba kin Momi a cikin raina ba. Tabbas akwai kishi kuma kowace mace tana da nata daidai gwargwado amma ni Amina ban zafafa shi akan matar nan ba duk sanda zuciyata za ta kitsa mini mummunan abu akan kanta nakan yi tirr da ita da take bijiro mini mugun nufi akan matar da alherinta ya fara riskata kafin wata mu'amula mai karfi ta ratsa tsakaninmu. Duk abubuwan da suka dinga faruwa yaranmu suka had'a Amma ni da ita sa'insa mai muni bata ta'ba hadamu ba, kuma lafiya lau muka yi sallama da juna har ta koma ga Ubangijin talikai. Har yau har gobe ban kulleceta ba ban kuma k'ullaci yaranta ba ina jin tausayinsu kuma ina yi musu kallo irin na uwa." D'akin ya shiru bayan ajiye maganata na ja numfashi cikin bushewar ma'kogwaro na cigaba da cewa." Magana akan Hauwa kuma ni ba zan iya ce miki komai ba, abinda dai na sani shine Hauwa ta yi mini kokari kwarai kuma babu kishi da ganin kyashin juna a tsakanina da ita. Duk hanyoyin na bi domin na nuna mata abubuwan da take ba su da kyau na bi, na yi bakin kokarina amma ba ta ji ba. Dalilin rigimarsu da maigidan tana da ala'ka da ni da ita mai rasuwar da yaranta. Mun daidaita a wattanin baya har na so ni da ita mu je mu dubata a lokacin da ta kwanta a asibiti Amma fafur ta'ki sai tare da Baba Tabawa na tafi. Wannan shine abinda zan iya gaya miki Mamana bayan hakan ban San abinda yake tsakanin Hauwa da mijinta ba tunda tun kafin ta aikata haka na yi iyakacin bakin kokarina a kansu ita dashi amma babu wanda ya saurareni a cikinsu."
Ta jima sosai kafin ta yi magana cikin yanayi na damuwa ta ce." Dangin matar nan dai a ciki suke da ku Amina domin gani suke yi bakincikinku ne ya kashe musu 'yar uwarsu duk wanda ya zauna ya tashi sai sun amayar masa da abinda yake cikinsu.
Anti Yagana ta ja tsaki tana fad'in." To, abinda ya fi sai kawai su d'auki lasifika su fara bi sa'ko da loko suna shela tunda ba su da hankali, wannan ba k'auna ba ce abinda suke nunawa tsantsar jahilci ne kuma za su hana yar uwarsu kwanciyar lafiya a kabarinta muddin suka ce za su tashi rigima abubuwa da yawa ne za su faru. Dama zaman tare ai ya gaji haka dole a samu matsaltsalu ma bambamta sai dai kawai Allah Ya kyauta."
Ta girgiza kanta tana fad'in." Hakane amma Yagana daidai ne Hauwa ta ajiye jariri sabuwar haihuwa ta shilla wata duniya ko a waje Tajo ya je ya auri yarinyar nan ya kamata ta aikata mana wannan rashin mutuncin. Jininmu ce fa ciki daya fa ba wasa ba ne Yagana ya kamata Hauwa ta gane kuskuranta wallahi ni dai idan da yawuna da shawarata ba zan bawa Tajo umarnin mayar da ita dakinta ba, tunda ta za'bi ta tozartamu shikkenan sai dai zumuncin ya lalace ."
Anti Yagana ta ce." A a ba za a yi haka ba Hajiya, ai ko babu dangantaka ta jini an riga an zama daya tunda har yara suka ratsa tsakani. Don kyautawa Hauwa ba ta kyauta ba. A dai nuna mata kuskuran abinda ta yi a gyara ta dawo dakinta a ganina shine abinda ya fi dacewa."
Ta gyada kanta ba tace komai ba tabbacin maganar anti Yagana ba ta gamsar da ita ba.
Na ce." Anti Yagana idan Hauwa tana da lefi shima yana da lefi fa. Domin ya yi abubuwa sosai wanda ya kamata a ce ya gane kuskure ne a zamantakewa amma bai gane ba, ni na yi kokarin dannewa dalili nasan babu wani abun da yake dawwama sai ikon Allah wanda shi muka gani yanzu. Na yi ta ko'karin bata shawara kan cewa ta kawar da kanta ta kasa jimirin yin hakan har sai da bacin rai ya ratsa tsakaninsu. Ya kamata gaskiya a tsage Mamana. Shi kansa maigidan akwai tashi matsalar sai dai ace ta Hauwa ta rinjayi tasa."
Ta ce." Ni dai da yawuna ba zan bashi umarnin dawo da Hauwa ba duk hukuncin da ya yanke daidai ne."
Tana fad'in haka ta tashi tana cewa." Zan je na watsa ruwa can wurin su Hajja jikina duk ciwo yake yi mini na samu nasa wani abu a cikina."
Na ce." To shikkenan Mamamu dama na ce da Baba Tabawa ta tu'ka mana towo don zai fi manà dadin ci akan tsabar shinkafar nan."
Ta ce."Aikuwa kin yi shawara mai kyau Amina don tunda aka sanar da ni rasuwar nan wallahi ko na sanya abinci a gabana sai dai na kalleshi ba na iya ci. Kai rasuwar baiwar Allah nan ta ta'ba ni wallahi."
Anti Yagana ta ce." Ba ke kadai ba wallahi ni kaina na gigita kwarai da aniya Ubangiji Allah Ya yi mata rahama."
Muka amsa da amin gabad'ayanmu kafin ta yi mana sallama ta fita daga d'akin, anti Yagana ta dube ni tana fad'in." Na so na tambayi Ummansu Hadiza labarinta amma na sha'afa wallahi, ina so mu sake samun lokoci mu je mu sake dubata ko ya ki ka ce."
Na ce." Hakane anti Yagana ni kaina Hadiza tana raina wallahi, dalilin da ya sanya kenan na ce da Hamusu duk karshen wata ya dinga yi mata siyayya yana kai mata, zuwan namu yana da amfani ai hannunka baya rubewa ka yanke ka yar."
Ta furta." Ni har fargabar ganinta nake yi wallahi saboda Ina tuna irin kukan da ta dinga shirga a ranar da muke je kin san da kyar aka tura ciki muka fito, na jima ina kukan zucci duk sanda na tuna da halin da take ciki nakan shiga yanayi na damuwa mace a irin wannan wurin a ajiye Amina duniyar nan ta baci duk da ba ita kadai ba ce, amma su kansu ma'aikatan wurin wallahi wasu daga ciki ba su tsoron Allah."
Cike da damuwa na ce." Anti Yagana lefin Hadiza na kisa ne ta kuma tabbatarwa da kotu gaskiyarta ba mu da wani yun'kuri da zamu yi domin ceto ta. Hakkin rai ba abin banza ne. Idan Allah Ya kar'bi tubanta kuma tana da ragowar rayuwa sai ki ga ta fito ta hanyar da ba mu yi tsammani ba. Idan Kuma sun kasheta shikkenan sai ta riski Ubangijinta a wankakkiya. Ubangiji Allah Ya kare mu daga fadawa jarabawa da mummunar kaddara."
Ta amsa da Amin Ya Allah da yanayi na damuwa da nadama.