← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 43

Sashe 13

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wace hujja ce za ta nuna mini ba had'a ba ki kuka yi domin ku ci zarafin matar nan ba. Shin mai ta tsare muku ne, ni ba zan goyi da bayan karya na take gaskiya ba, domin alherinta nake ga ni, kuma ta yi mini ta yi muku."
Na ce" Saboda muna yi mata bakinciki dalilin dukiyar da ta tara shiyasa muka had'e mata kai. Uban wanene ya ce ta d'aukar mini yara. Idan ka mallaka mata twin's wannan naka ne, ban damu ba, nawa dai da baka da iko a kansu ban ce mata Maryam ga yarana ri'ke mini ba."

"Har da zagi a cikin maganarki saboda baki da mutunci ko Amina? Ni ban kira ki domin ki yi mini rashin kunya ba matsaya nake so mu nema ni dake zan 'bata miki rai wallahi tallahi!" Ya kai karshen maganar cikin tsananin b'acin rai."
Kuka na fashe da shi tare da furta." Ai gaskiya na fad'a ban fa nemi wani mahaluki ya rike mini yara ba, karfi a gwada mini, an yi kuma an biyo mu da sharri a ce ba zan yi magana ba.''
Ya ce." To yaran da ki ke ta ha'kilo a kansu ai an mallaka mini su ke ce ki ke haukanki kuma wallahi sai na so zaki gan su balle ki gwada gadara a kansu, kin haife su ne amma billahi ko kaffara ba zan yi ba sun fi ki hankali, dama tuntuni na gane karamin Yusi nake nufi ya fi ki nutsuwa da sanin ya kamata saboda ai ba tarbiyarki ba ne shi din."
Bakina ne ya mutu murus! na kasa tanka masa saboda tsabar takaici da b'akinciki wace irin masifa ce wannan nake cikinta ne, ni Aminatu. Hawayen rashin yadda zan yi suka dinga gudana a kumatuna. Wato ita 'ya mace ta ko'ina rananniya ce
Mutumin nan ya dabaibaye rayuwata ya d'aure ni ya hana ni motsi duk ta inda na b'ullo sai ya ci galaba a kaina.
"Yanzu daidai ne a matsayinku na iyalina ku tsaya a gaban alkali domin shari'a?" Kaina a sunkuye na gagara ce masa komai saboda gabad'aya ma tunanina ya tsaya cak kwakwalwata hutu take buk'ata.
Ya cigaba da ce wa." Ba ni da wata hujja mai k'arfi da zan dakatar da su akan abinda suka niyyata don cin zarafi da rashin kyautatawa kun yi musu, menene na sanyo iyaye a ciki Amina har da ala'kanta mutuwarsu da wani lamari mara dad'i, kun kyauta a hakan?" Ya kai k'arshen maganar a d'an raunane har ma da karyar da kansa domin ga dukkanin alamun kukan da nake yi ya fara ta'ba shi, kuma yanayinsa ya nuna gabad'aya masifar shi ma ta ishe shi.
Bance masa komai ba har sai da ya sake maimaitawa kafin na daure na ce." Ni fa laifina kake gani da gangan, amma wallahi ba ni da hannu akan duk abinda Hauwa ta yi, na gaya mata ba daidai ba ne, ta daina ta'ki ji, to ya zan yi mata, kuma kai ma me yasa ba ka tambayi dalili ba kawai sai ka dinga d'aukar laifi ka d'ora mini."
"Ya ba zan ga laifinki ba Amina, idan kin manta da alkawarinmu ni ban mance ba, mun yi dake cewa duk rintsi duk wahala za mu zama abu daya matsalata zata zama taki haka zalika matsalarki za ta zama tawa, amma lokaci guda kin karya alkawari har kina nuna mini iko da gadara akan yaran da ki ka haifa da wani namiji, ni za ki yi wa gori ko?"
Wasu hawayen suka sake silalowa saman kuncinta na ce." Ni ban ga ta inda na yi lefi anan ba, idan har gaskiya za a bi, yaron nan Salim ya fito karara ya nuna rashin kaunarsa ga Kamalu ya yi masa abubuwa masu muni amma da kai da ita matar taka babu wanda ya ta'ba nuna masa hakan ba daidai ba ne. A cikinku kuma babu wanda ya neme ni da maganar domin a ba ni ha'kuri ai ku din ba yara ba ne, kun san daidai da rashin daidai ba a kyauta mini ba in dai gaskiya za a bi, yaron nan Kamalu ba a yi masa adalci ba tunda sharri aka yi masa."

Shiru ya yi bai yi magana ba, d'akin ya cigaba da d'aukar sautin shashshekar kukana da sautin jan hancin da nake yi.
Ya nisa kafin ya ce." To yanzu ha'kuri ki ke so a baki kenan?
D'auke kaina na yi ban kalle shi ba don yadda zuciyata take tsalle ji nake yi kamar na rufe shi da bugu.
Ya rungumo k'afadata a hankali ya sanya ni a jikinsa yana jijjigani. Cirewa na yi tare da matsawa gefe ya dube ni a nutse kafin ya ce." Allah Ya huci zuciyarki ba a kyauta ba gaskiya, kuma zan gaya miki ni ma ban yarda ba. Shirun da na yi ba yana nufin na yarda da maganar Salim ba ne, ina ta nazarin yadda zan yi na kawo sasanci a tsakaninsu, tabbas Kamalu yaro ne da nake kyautata masa zato, ina so ki cire duk wani wasiwasi a zuciyarki ba na nufin yaranki da sharri sai alheri."
Shiru na yi jikina ya d'an yi sanyi kad'an domin na d'an hangi alamar nadama da neman sasanci a tare da shi.

Ya cigaba da ce wa." Ku zauna lafiya don Allah, ni na gaji da wannan fitinar taku. Kin tura yara kano ba tare da yawuna ba, tunda ba kya son zamansu a tare da ni shikkenan na kai su wurin Hajja tunda Gwaggwo ta mallaka mini su. " Ya fad'a cike da kwarin gwiwa."
Na ce." Ni ba damuwata ba ce wannan abinda ya fi tsaye mini a rai shine datse igiyar auranka da ka yi tsakaninka da Hauwa akan wannan matsalar kenan hakan yana nuna cewa a shiryeka kake duk lokacin da sa'ba ni ya gifta tsakaninmu da matarka ka yi saki tunda bashi da wahala a wurinka."
"Ni ba saboda wannan matsalar na saketa ba, Hauwa ba ta jin maganata domin duka wannan hargitsin itace mussababi domin da ba ta gaya miki ba ina ganin da duk hakan bata faru ba muna zaune lafiya, tun kafin mu zo nan na gargad'eta ta take umarinina, ke a ganinki abinda ta yi daidai ne ko rashin daidai ne.

"Ni ma ban ce ai ta yi daidai ba. Amma kai ma ai ba ka yi daidai ba, mai yasa za ka saketa. Kai tsaye ya ce." Saboda na gaji da halinta."
Na zuba masa ido da mamakin maganarsa a tare da ni. Wato ita mace cikin kowane hali za ta iya jure zama da namiji amma shi kuskure karami sai ya nuna rashin ha'kurinsa. Hauwa dai duk a cikinmu ta fi kowa kusanci da shi amma gashi yau yana fad'in ya gaji da ita.
Na ce." Ka mayar da ita tunda ciki ne da ita sanin kanka ne a musulunci babu kyau sakin mace da ciki, kuma idan Hajja ta ji hakan ranta ba zai yi mata dad'i ba."
"Ai ita Hauwa ba ta duba haka ba Amina, kuma cikinku wallahi kada wadda ta kuskura ta gayawa Mahaifiyata akan hakan rai zai 'baci."
"Ai kai zaka gyara matsalar gidanka kafin ta fita waje idan ba ka so Hajja ta ji abinda ka yi sai ka yi gaggawar gyara kwabar da ka yi."
Ya 'bata rai yana fad'in." Kina so ki ba ni umarni kenan?"
"Ba umarni ba ne ban isa ba, shawara ce nake ba."
"To ba zan d'auka ba har sai kun je ke da ita kun bawa Maryam da 'yar uwarta ha'kuri akan abinda ku ka yi musu.''
Ido na zuba masa ina kallonsa da mugun takaici.
Na gyada kaina tare da janye idona daga kansa ban ce komai ba..
Sai ya cigaba da ce wa." Wannan shine kawai, ki ja ta tunda tare kuke kulle-kullenku sai ku je ku ba su ha'kuri domin mun yi magana da Nabila ce wa gobe za ta koma jos, to kafin ta tafi din sai ku gyara kuskuranku"
Na juyo fuskata a d'aure na ce." Wannan kuma shine ba zai yiwu ba, idan hakurin da ka ba su bai isa ba, shikkenan don Allah ka cikashewa Hauwa sauran igiyoyinta da suka rage, idan hakan ma bai yi maka ba sai ka had'a har da ni gabad'aya."
Ya ce." To kada ki sake yi mini magana akan abinda ya shafi tsakanina da Hauwa, ba ke ki ke auranta ba, ni ne babu ruwanki wannan shine maganarmu dake ta k'arshe akanta."
Na dinga kallonsa zuciyata na sake suyuwa da kutun takaici da b'akinciki. Wannan wani abu ne da zai yi masifar wahala a ce Hauwa ta je ta bawa momi da nabila ha'kuri saboda iya zaman da na yi da ita na gane cewa macace mai mugun girman kai da kifad'i, ga taurin kan tsiya, bai shirya kwantar da rikicin ba, domin da ya shirya mutuwar matsalar ba zai 'bullu da wannan abinda ya san lallai da wahala ya yiwu ba.
Jin an kira shi a waya ya sanya na tashi na fita daga d'akin ba tare da na sake cewa komai ba, matsalarsu ce can ta family iyakacina shawara, kuma ni ban tura Hauwa cewa ta yi abinda take yi ba, akan kanta take yi saboda wata manufa tata da kuma masifar kishi, duk wanda zai zarge ni da hannu akai ya d'auki hakkina. Ba zan sake cewa masa komai ba.
Chapter 13 · 0% Book details