← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 43

Sashe 33

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Duk yadda na so ganin na daure zuciyata daga barin jin zafin yadda yake yabon matarsa ta fari data mutu kasawa na yi sai na manta ma da maganar da muke tattaunwaa akai zuciyata ta fara tsalle tana tukuki tsabar zafin kishin da ya taso mini na ce." To ai wannan maganar da kake furtawa kamar gugar zana kake yi mana ni da ita Hauwan kawai ka fito fili ka gaya mini cewa Amina har yanzu ban samu madadin Samira ba, ai ta riga ta mutu kuma duk wanda ya rike ya tafi baya dawowa sai kawai ka ro'ki Allah Ya takaita maka kwana ka je ka risketa."
Ya zuba mini idonsa yana kallona. Na juyar da kaina gefe tare da sake had'e fuskata. Shiru d'akin ya d'auka bai ba ni amsa ba. Na tsame hannuna daga cikin abincin da nake bashi na Yagi tissue paper domin goge hannuna. A hankali ya ce." Ban k'oshi ba."
Zumbura baki na yi na yun'kura na tashi tsaye sai ya riko hannuna tare da janyo ni jikinshi ya mike k'afafunsa na zauna saman cinyarsa. D'auke kaina na yi domin ji na yi ma sam bana son kallonsa saboda takaici wannan a cin fuska ne a takaice."
Ya ce." Amina kalleni."
Kallonsa na yi babu fara'a. Ya rintse idonsa a tsanake ya ce." Kin san jini a jikin d'an adam ko?"
Na yi shiru ban tanka ba. Ya d'an matseni a jikinshi yana sakin ajiyar zuciya cikin kunnena ya furta." A jinin jikinkina kike yawo. Ina can wata uwa duniya kina yi mini gizo Amina ina alkawarin soyayyar da ki ka ce za mu yi idan na dawo gida?"
Da mamaki mai yawa a tare da ni na kura masa Ido. Ya sake matse ni a jikinsa yana me sanya fuskarsa tsakankanin wuyana wurin da yake bala'in so kenan a jikina.
Jikina ya shika k'warai da aniya daga sannan na sallamawa sha'anin rijalu na sake yin lakwas ina ayyanawa a raina ko ni ce na fadi na mutu mutumin nan damuwarsa kalilan za ta kasance babu wani abu na jin dad'in rayuwarsa da zai fasa.
Saukar hannunsa da na ji a kirjina ya sanya ni zabura. Na cire hannun da sauri sai ya had'e yatsunmu wuri d'aya yana bina da wani irin kallo wanda yake ko'karin kassara ni. Nan take tausayin kaina ya rufe ni. Yanzu nan ya gama jadadda irin alhini da kewar tsohuwar matarsa jiya kuma matar da ni da Hauwa muke ganin ya fifitata a kanmu ta fad'i ta mutu yau aka binneta a kabari wai har ya gama alhinin da jimamin yana bijiro da wani shagali da jin dad'in da bai wuce na 'yan sa'anni ba.
Cike da kasala ya sake mayar da hannunsa saman kirjina yana tatta'bawa ban yi nawar sake cire hannunsa ba muka kurawa juna ido da kyar na furta." Ba ka ji wani iri ba?
Lumsassun idanuwansa ya bude a dabarbarce ya ce."Na ji sun 'kara girma ko dan na yi kewarsu ne." Raina ya baci da jin amsar da yake ba ni. Wato ma bai fahimci akan abinda nake magana ba sai kawai na yi yun'kurin sauka daga cinyarsa ya kuwa ri'ke ni da kyau irin rikon da baki isa ki k'wace ba.
Sosai na bude idona a kansa na ce." Gaskiya ni ka ba ni mamaki wallahi mutuwa fa aka yi maka mai zafi har alhinin ya bar gangar jikinka kenan."
Ya gyada kansa yana fad'in." To ai ta riga ta rasu Amina, ni na isa na dawo da ita ne? Mutuwar nan kowa zai mutu to me zai sanya a tauyi rayuwa a bawa gangar jiki da ruhi abinda yake muradi kada ki manta ke fa ki ka yi mini alkawari idan na dawo za mu sha soyayya."
Shiru na yi kawai Ina kallonsa gabad'aya kaina ya kulle mutumin ya gama goge mini duka haddar da na yi a kansa, ai na d'auka na gama karantar halayensa gabad'aya ashe da sauran abinda ban gama sani ba.
Ya d'ora bakinshi saman lebunana ya sumbata kafin ya cire a hankali da wani irin yanayi ya ce." Abin nan yana d'auke hankali Amina zai mantar da ni abubuwa da yawa, bayan kiran sunan Allah a cikin kunci da damuwa sai wannan lamarin domin ni a wurina ma gaba yake da cin abinci, a wannan dare babu abinda zan fasa ai a haka duniyar ta ginu tun kafin mu zo cikinta ake mutuwa ake muka sunnah irin wadda za mu yi yanzu, mu ji dad'i mu gamsu kuma Ubangijin da ya ce mu yi hakan ya ba mu lada
mai yawa."
Na yi kasa da kaina dalili ba ni da wani karsashin da zan kalubanci maganarsa ta kowace siga ya fi ni gaskiya amma ai ana barin halas da kunya wallahi har yanzu matar nan idan ta fado mini a raina sai gabana ya fadi.
Ya cika ni na sauka kasa Yana bude fulas din abinci jikinsa har d'an rawa yake yi ya ce." Abiñci zan baki kici ki koshi kamar yadda ni ma ki ka ciyar da ni daga nan kuma sai mu sake ciyar da juna wani abincin na mussaman ko ba haka ba ne?"
Na ce." Gaskiya ba zan munafurceka ba a yanzu wallahi ba ni da wani karsashin da zan tari wannan lamari daka bijiro da shi. Ka yi hakuri tukkuna dukkunimu hankalinmu ya daidaita sai irin wannan nishadin ya biyo baya."
Ya gyara yanayinsa yana fad'in." Ni ina da karsashina, sannan kuma a cikin nutsuwa da hankalina nake, menene a ciki ne haramun ne, saboda kawai an yi mutuwa sai a ajiye ibadar Allah ba na son jayayya Amina a bukace nake ke daga ganin yanayina ma kin san da hakan to me zai sanya ba za ki sama mini da farinciki ba.
Kuka na fara yi tsakani da Allah ni ban san yadda zan yi na tari abinda yake so ba har na taimaka masa ya nishadantu irin yadda ya saba, har yanzu jikina babu wani kuzari ni gabad'aya ma duniyar ta fice mini daga raina.
Chapter 33 · 0% Book details