Sashe 38
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 4 min read
Wannan ya wuce da wasu wattani Nabila dai ba ta daina d'ora hotonta a status tana habaice-habaice ba. Ni Kuma kamar wadda ta yi wa asiri idan na ga status din nata bana iya d'auke kaina sai na shiga na gani. Tun abinda take yi yana ba ni dariya har ya dawo ba ni mamaki. Ta dage dai wai dole sai ta ba ni haushi tun kafin ta shigo gidan idan da kaddarar kakan kenan domin idan duk jikina kunnene ba zan yarda da maganganunsa ba. Namiji ne akoyaushe yana iya canzawa. Duk wannan bidirin da ake yi Hauwa ba ta sani ba don ban gaya mata komai ba. Da yake ni ba ma'abociyar dora status ba ce don sai nafi wata biyu uku babu komai akan status dina tunda ya haramta mini harkokin social media farkon auranmu na kiyaye tunda ya ce baya son hotona ko guda ya kara fita ina kiyayewa sosai idan har na dora status to hoton yara ne ko addu'a akan wata mas'ala ko kuma tahamidi ka Allah. Yau dai na ce bari na gwada tsokanar Nabila na gani. Hoton ranar auranmu a saudiya na dora wanda aka yi mana ina rungume a jikinsa. Duk muhimman hotonana suna nan a memory na na adana. Guda daya kawai na dora tare da rubuta shukuran ya rabb"
Kafin na kai ga sauka itace kusan ta hud'u daga cikin wad'anda suka duba. Ban yi mamaki ba, na yi murmushi tare da kashe wayar na ajiye cikin zuciyata ina fad'in za mu ga dai zuwan da dawowar."
Na tashi na fita falo da yake yammace yaran duk suna makaranta babu kowa a falon sai tibi tana yi ita kadai. Baba Tabawa tana kicin na leka d'akin yaran na samu Mairo tana shirya musu kayansu da aka goge. Ta juyo da sauri tana fad'in." Hajiya akwai abinda za a yi ne?"
Na girgiza kaina a hankali na ce." E, to idan kin gama a nutse don ba sauri nake yi ba sai ki soya mini wainar fulawa yajin tafarnuwa amma kada ki sanya masa kuli idan za ki ni'ka."
Ta ce." In sha Allahu an gama Hajiya za a yi yadda kika buk'ata." Har na juya zan fita sai na dubeta tare da fad'in." Nafiso ta yi 'kanzo fa wainar Mairo."
Da yar dariya ta ce." Zan yi fiye da yadda kike so in sha Allahu."
Na juya na fita jikina babu wani kuzari na arziki ciki ne da ni, ni na tabbatar da hakan duk da lokacin al'adata bai yi ba balle na gazgata amma ni cikina a sati d'aya ma yake bayyana kansa.
Na leke d'akin Hauwa tana band'aki tana wanka kasancewar itace da girki sultan kuma tunda ban gan shi a wurin Mairo ba nasan yana goye a bayan Baba Tabawa yaron ya shaku da ita sosai.
Na ga hauka a daran ranar dana sanya hotona da maigidan a status wurin Nabila sai da ta jera status sama da arba'in cinkus. Ni kuwa saboda nasan saboda ni ta yi sai na'ki dubawa daga lokacin ma na goge lambarta daga wayata na yi dariyata na koshi ina mamakin al'amarin.
Babu wanda na gayawa ina da juna biyu Hauwa ba ta sani ba haka ma anti Yagana da Sahura ballantana maigidan bai lura ba domin ina ta karfafa jikina. Shi kuma a lokacin abubuwa sun yi masa yawa kwarai yana ta hidimar bude gidajen mai a Legos har guda uku. Da babban kamfanin siminti da za a yi bikin bud'ewa duk a can Legos din. Harkokinsa da yawa sun fi a can, sai ko kano anan Abuja bai fiye yin hada-hadar kasuwanci ba. Nasan dai yana da manyan manyan hotels da gidajen da kwarori suke zaman haya akwai kuma shaguna ana hada-hadar sayar da spire pats. Amma babu lefi gaskiya yana da kadarori masu yawan gaske da arzikin da a kullum yake kara ninkuwa duk inda aka ga haka kuwa tabbas dukiyar tun fil'azal ba a cudanyata da haramun ba.
Yawan fitina da binbini ma duk ya rage saboda yadda na lura idan bai kammala da wannan hurd'odin ba hankalinsa ba zai kwanta ba.