← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 43

Sashe 16

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 3 min read

"Ita din mutuniyar arziki ce kenan?" Ya fad'a da izgili." Na yi shiru ban bashi amsa ba domin yadda ya fadi maganar ya nuna mini cewar a fusace yake.
Jan tsakinsa na ji kafin ya datse kiran. Na cire wayar daga kunnena raina a kuntacce na tashi na shiga bandaki domin gyara jikina.
Da kyar na iya cin abinci duk kuwa da dokin sakawarar da na yi amma takaici bai barni na ci da yawa ba. Hauwa kam ko dand'ane ba ta ce ba a daran sai da Baba Tabawa ta yi mata fatan wake da manja da kifi ga uban attaruwun da ta ce a zabga mata saboda yanayin bakinta.
Sai bayan goma na dare tukkuna muka yi sallama kowa ya shiga domin ya kwanta.
Lokacin kiran Hajja ya shigo wayata can saman dirowa romat na d'auka na rage murya domin koda na shiga d'akin kallo na kunna domin idanuwana gabad'aya a soye suke da zallan b'acin rai da damuwa
Na shiga zullumi da nazari sosai a lokacin da na ga kiran Hajja domin sai nake tunanin ko ya sanar mata da wata magana ne. Yanayin yadda muka gaisa da wasa da dariya ya sanya na dan ji sanyi a raina sosai ta yi mini tambayoyi masu cike da hikima irin ta manya ni na na bata amsa cikin hikima ban yarda na sanar da ita akwai matsala ba tunda bai gaya mata ba, to fadarta daga bangarena takan iya janyo mini matsala babba.
Ta ce." Ga Yusi dai muna tare dashi anan falo duk ba mu kwanta ba, Kamulu kuma ya ce mini zai shiga cikin gari can gaba da gidanku rijiyar zaki ya ce mini idan ban manta ba an gayyace shi bude wata sabuwar makarantar islamiyya ya ce mini zai kwana a gidan Gwaggo da safe sai ya wuce can din."
Murmushi na yi a tsanake na ce." To shikkenan Hajja, Allah dai Ya saka da alheri na gode sosai, Allah Ya kara lafiya da nisan kwana."
Ta amsa da Amin Ya Allah. Kafin ta bawa yaron wayar na ji maganarsa yana fad'in." Mama barkanmu da dare.
Na ce." Barkanmu dai Yusi ya kuke?" Ya amsa da "Alhamdulillahi Mama." Shiru ya biyo bayan maganarsa. Gabad'aya tunda abin nan ya faru yaron baya sakewa da ni. Kamalu ne ma ya kira ni a waya shi ma sau daya sai ka ce wad'anda aka yi wa wata huduba akaina. Kai na girgiza a hankali na ce." To tunda ba ka da abin cewa sai an jima ko.".
Yana 'yar dariya ya ce." Mama kenan, na yi shiru ne ai Ina sauraranki ko da abinda za ki ce mini."
Na ce." Da yake ni ce sarkin korafi ko?"
Shiru ya yi bai ce komai ba, amma ina jin sautin murmushinsa. Na ce." Malam kashe waya ka bawa mai ita."
Da sauri ya amsa da "To mama." Amma ban ji ya kashe din ba, nasan jira yake yi ni na fara kashe tawa.
Murmushi kawai na yi na ajiye wayar a gefena tare da sauke ajiyar zuciya.
Chapter 16 · 0% Book details