Sashe 21
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 10 min read
To maigidan bai sake shigo mana ba sai da garin Allah ya waye tukkuna ban kai ga fitowa falon ba ya shigo yaran kaf dinsu a tare dashi da yake asabar ce suna gida babu makaranta sai sha biyu na rana suke tafiya tahafiz su tashi shida na yamma.
K'amshinsu ya cika mini d'aki da uban da yaran sun sha gayu.Ido kawai na zuba musu Khalil ya fara gaisheni kafin sauran suma su tsuguna kasa kamar yadda suka ga ya yi "Mama ina kwana." Suka dinga jerowa ina amsawa. Khalil din ya ja baya suma sai suka ja baya suka tsaya kusa da su. Na jima ina nazarin abinda suka yi kafin na furta." Khalil ja su ku tafi wurin Mamanka ku gaisa."
Bai ce mini komai ba sai ya dubi baban nasu da yake tsaye a jikin kofa shi bai shigo ba shi bai fita.
Ganin irin kallon da yake yi masa ya sanya na gane umarninsa yake jira. Na cika da mamaki sosai a raina ina fad'in lallai akwai rikici a kwance idan har bai farga da abinda yake yi cewa kuskure ba ne ya za a yi mace ta haifi d'anta ka d'auke mata shi saboda fin karfi ka kaiwa wata har da ko'karin shiga tsakani akwai matsala idan ni na jure hakan ina da tabbacin za a sha daga da Hauwa.
Kasancewar na lula cikin tunani ya sanya ban fahimci mai yake ce musu ba na dai ji yana magana da yaran kafin su kama hanya su fita. Ya rage daga ni sai a d'akin.
Ya shigo sosai ya tsaya a jikin mudubi. Ganin haka ya sanya ni da sauri na tashi na bar wurin, bandaki na shiga duk kuwa da cewa ba ni da wani uzuri, kawai ba ni son kallonsa ne..
Ban fito ba sai da na d'auki kusan mintina sha biyar tukkuna na fito na samu d'akin babu kowa. Tsaki na ja kawai na wuce na je na zauna zuciyata a cunkushe.
Ban yi tunanin zai dawo da daddare ba tunda sau d'aya yake shigowa wataran ba bayan shigo mana, tunda matsalar nan ta faru ya rikita mana lissafin kwanan turaka domin ko ya shigo baya kwana a gidanmu can wurinta yake tafiya hakan ma yana yi mini ciwo sosai.
Muna zaune a falo gabad'aya har da Hauwa wadda take ta fama garzar yalo da Masaudu ya sayo mata can cikin kasuwa. Kamar koyaushe ya tsaya suna gaisawa da Baba Tabawa kafin ya haura samansa. Hauwa ta tarkata shirginta ta nufi daki ba tare da ta cewa kowa komai ba. Girgiza kaina kawai na yi saboda takaici wannan abin da suke yi ita da shi.
Ina zaune ban motsa ba Baba ta ce." Hajiya ko za a hadawa maigidan abinci ne?" Na ce." Ba na jin yana da bukata baba daga gidan matarsa yake."
Ta yi shiru tana kallon wani waje kafin ta sake dubana tana fad'in." Ko za ki tambaye shi dai."
Na ce." Baba kyale shi don Allah, idan yana da bukata daya shigo zai yi miki magana tunda kun dan jima kuna magana kafin ya haura samansa, kin san ba shi da 'koron baki."
Ta jijjiga kanta ba ta sake cewa komai ba sai ta tsirawa tibi Ido nasan ba ta so hakan ba don babu yadda za ta yi ne.
[Kashe wayata na yi don ba na so na ga kiransa. Bai sake saukowa ba har muka tashi daga zaman falon baba Tabawa dai babu wani karsashi a tattare da ita muka yi sallama.
Sai da garin Allah ya waye tukkuna na kunna wayar haka na kwana babu sukuni.
Ina bandaki ina wanka na ji motsi ban kawo cewa zai biyo ni bandakin ba kawai sai ganinshi na yi ina tsaye tumbur da ni. Hankalina ya tashi ainun wata kunya mashahuriya ta ritsa da ni. Gani na dinga yi kamar ya keta mini alfarma nan da nan na ji idona ya fara kawo ruwa. Duk da ruwan kumfar sabulun da ya yi wa jikina sansani hakan bai hana ni yin gaggawar raromo towel dina da take sakale ba. Na fara kici kicin daure jikina tsananin yadda hannuna yake rawa ya sanya towel din faduwa kasan wurin ruwan da yake zuba ta saman shayar da na kunna ya jike shi.
Raina ya b'aci mutuka haka na sunkuya na dau'ko towel ya yi jagab jikina babu kuzari na kashe shayar kafin na ya'ba towel din a jikina a hakan a jike. Ya tsaya kusa da ni a nutse kawai ya zura mini idanuwansa .
Na daure na furta." Amma dai kasan haramun ne abinda ka aikata ko?"
Ya yi shiru bai tanka mini ba kawai dai ya zura mini idonsa kaf ilahirin jikina rawa yake. Can kasa-kasa na yi tsaki tare da d'an janye jikina. Ya sake biyoni har sai da kirjinmu ya hadu. Hannuna ya kamo kafin ya duba tafin hannun kamar mai neman wani abu. Ya cika ya kamo na hagun shi ma yana dubawa. Cike da mamaki nake dubansa Ina nazarin abinda yake yi. Yadda yake sauke ajiyar zuciya shine abinda ya fara d'aga mini hankali.
Ko'karin sanya ni yake yi a jikinsa ina dojewa, na lura lallen da akayi mini shi yake ta bibiko. Kokawa muka fara yi a toilet din har sai da ya cire mini towel din ya yi jifa dashi can gefe, kuka ne mai karfi ya k'wace mini ganina a haka cikin hasken rana. Ko auratayya zai yi da ni da safe ko da rana yakan sha wuya kafin ya ribace ni na amince domin na tsani ya ga zahiri na a gaske duk da na tabbatar da ce wa babu wata makusa a jikina da za ta janyo mini 'kyama a wurinsa amma haka siddin nake gudun haka.
Saman tumbina da ya dan tasa ya d'ora hannunsa bai ce mini komai ba ya fara wasa da hannunsa a wurin har ya so ya zarce can kasa. Na matse gefe cikin zafin nama kafafuna na wani irin rawa.
Ya sake biyoni a karo na uku. Sai kawai na silale a kasan wurin na zauna tare da takure jikina. Babu wani lamari da zai wanzu a tsakanina da shi a halin yanzu tunda har yanzu ba ni da tsarki kawai dai zai daga mana hankali ne.
Ganin yadda nake kuka tukuru ya sanya ya juya ya fita can kasa na ji shi yana fad'in." Ki fito zan yi magana dake."
Bayan ya fita na yun'kura na tashi tsaye har yanzu kafafuna ba su daina rawa ba, sabon wanka na sake yi. Dana kammala na rasa yadda zan yi na fito tunda towel din da zan d'auro ya jike babu wani a toilet din sai kananu kuma babu wanda zai ratsa ni. Na rasa yadda zan yi haka na jure na bude kofar amma ban fito ba ina hangensa a gefan gadona a zauna yana duba k'aramar wayarsa.
"Ka miko mini towel ko zani ka ji."
Ya dago ya dube ni da sauri amma bai ce komai ba, na sake maimaitawa Ina janye idona daga kansa. A nutse ya ce." Lallai za ki shekara anan a tsaye idan ni zan miko miki towel Amina."
Jin haka ya sanya ban k'ara cewa komai ba. Na yi kundubalar fitowa haka haihuwar uwata. Da kyar da hard'war kafafu na isa wardrobe dina. Ina jinsa yana ce wa." Ni da kayana a ce za a boye mini, to wane lungu da sa'ko ne ba ki kama kaina kin dora a wurin ba, da hannunki fa ki ke miko mini idan kin manta wannan kirjin naki cinyesu ne kawai ban yi na taune ba, kina ba ni ina sha fiye da yadda raina yake so."
Ban ce masa komai ba har na gama kintsa jikina yana ta sakin maganganu masu tsananin nauyi wanda na tabbatar da cewa wasu na aikata da sani na, wasu kuma ban san lokacin da na aikata ba domin kuwa bayan ni da shi sai Ubangiji da ya hallicemu ne kadai ya san irin ta'barewa da haukan da muke yi idan muna auratayya."
Na dube shi bayan na juyo da fuskata, gabad'aya yanayinsa ya canza duk ya shiririce idonsa sun risina sun kankance tare da wani irin yanayi. Yana ta ko'karin dannewa amma abin ya gagara. Koda na zauna a gefansa sai ya janyo ni da k'arfi jikinsa na karkwarwa ya fara fadin." Na zata zan iya dauriya Amina, mai zan samu ne, ina ta shirye-shiryen tafiya legos tunda na lura babu tsarki a tare da ke."
Na cire hannunsa da yake cikin rigita a nutse na furta." Ai ba ni da abinda zan iya baka a halin yanzu."
Ya mayar da hannunsa cikin rigar yana fad'in." Ke ce kuwa ki ke da abubuwan bayarwa my love ."
Na yun'kura na tashi hannun nasa ya sa'bule ya fito daga cikin rigata shi ma ya tashi da sauri na matsa gefe can nesa da shi." Wallahi ba ni da abinda zan baka, ba za ka samu hadin kaina ba muddin ba ka daina had'a ni da iyayena ba, na ga ji da rashin adalcin nan da kake yi mini, ni ba baiwa ba ce, idan kai 'karata shine zai sanya na shiryu to lalacewa zan yi bari ma na gaya maka gaskiya."
Ya zuba mini ido da wani irin b'acin rai a saman fuskarsa ya furta." Haka ki ka ce ko?"
Na ce." 'Kwarai haka na ce, ni da kai, duka babu yaro karami, kamar yadda ba ka so ana tiririn kai ka 'kara wurin magabatanka ni ma haka, ka san halin Baban Saude haka siddin ya zo ya ci wa Hauwa mutunci ai ni ce mai laifi tunda ba ka yarda cikin zubewa ya yi ba, amma ita Hauwa ai taimako ta yi, mai ta yi maka ka saketa kana bin ta da mugun nufi."
Ya jima yana kallona na lura takaici da b'acin rai ne suka taru suka yi masa dabaibayi bai sake ce wa da ni komai ba ya gyad'a kansa kafin ya kama hanya zai fita. Cikin zuciya na ce.'' Shikkenan ka ji idan da dad'i, ita matar da ka ratayawa fulawar soyayya ta iya da kai kawai, Amina karkatacciyar kuka, mu zuba gaba ce dai da k'ullaci ni ma na iya."
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 113
Muka cigaba da tafiya a gidan babu annashuwa da jin dad'in da ma'aurata kan jiyar da junansu. Ya sauko sosai ya yi tubis da shi domin salon horon da na d'auka ba karami ba ne.
Gashi sun yi fad'a da Hauwa ballantana ya tafi wurinta tunda tun dama can ita matar so ba wani kwanciyar aure yake yi da ita ka'in da na'in ba da bakinsa ya gaya mini hakan ba matsa shi na yi ba.Ashe ni da ya mayar towon tushe nice marufar asirinsa domin kuwa tuntuni ni nake iyawa da fitinarsa ko Hauwa ba za ta nuna mini komai ba. Lallai a wannan karon sai na nuna masa kuskuran abinda yake aikatawa a ganina duk hatsaniyar da za mu yi bai kamata ya d'auke mana kwanan aure ya kaiwa wata ba, wannan gadara ce da take hakki da kuma yi wa addini kutse, ba zan iya ba gaskiya idan abinda na yi a yanzu bai sanya ya daidaita nutsuwarsa ba hanya a bud'e take sai ya sake kiran Baban Sauden ya zo. Ni kuma sannan zan sanar da shi irin abinda yake yi mana na take hakki.
Gabad'aya ya nune koyaushe ya shigo gidanmu ba shi da wani kuzari tafiyarsa Legos ta dinga tangal-tangal domin ya turza-turza da ni na'ki amincewa da na bi shi, na gaya masa har abada kafata ta sake taka garin nan, idan lallai sai na yi zaman auran da shi to Ina nan.
Baya tunkarar Hauwa ni yake ta yi wa bibiko. Har yanzu ban san abinda yake tsakaninsu ba. Shi baya shi ba, itama baya ita ba, an rasa wanda zai sassauto a cikinsu. Tana dai gefe tana kallonmu kuma duk abinda yake faruwa bata ta'ba tambayata dalili ba.
Saura kwana daya ya tafi Lagos din ya ritsa ni a d'aki. Da farko rarrashi ya fara yi da ban baki tare da alkawarin ba zai sake kai ni kara ba. Hakan bai sanya ni na sassauto ba domin kuwa a duk lokacin da zan daga kaina na kalleshi wallahi duhunsa nake gani, a ganina zamana a gidansa kamar takura kai ne tunda shi kam ai kansa ya sani.
Bai wani ba ni tausayi ba duk kuwa yadda yake rausayar da kansa da muryarsa hakan bai burge ni ba. Da ya lura duk abinda yake yi ban saduda ba sai fad'a ta inda yake shiga ba tanan yake fita ba. Har da cewa ba zai ka'ra nema ba har ya mutu na je za mu tsaya a gaban Allah ranar lahira.
Ban damu ba Ina zaune ina kallonsa ya kama hanya ya fice cikin b'acin rai.
Tabbas na ji wani iri a jikina a lokacin da yake had'a ni da Allah. To ban san yadda zan yi na kwaci mutuncina a hannun wannan mutumin ba, domin ba ni da k'arfi ta kowane bangare sai ta wannan hanyar itace damata kuma hanyar da za ta sadudur masa da jiki.