← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 43

Sashe 11

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na ce." Hauwa babu lafiya 'bari zan yi wallahi yanzu haka maganar nan da nake yi miki jini ne yake zuba asibiti zan je. Ta yun'kura ta tashi da gaggawa tana fad'in." Bari na sa hijab muje Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un!
Da sauri na fita daga d'akin jin yadda wani abu mai nauyi ya fado cikin pant dina. D'akina ana shiga da gaggawa na zarce toilet na yi sauri na tsuguna abun ya fado kafin wani mashahurin jini ya biyo baya da tsananin ciwon k'wankwaso da gwiwa. Bangon bandakin na dafe tare da rintse idona da k'arfi na kira sunan Allah Ina jin shigowar Hauwa d'akin da yake ban rufe kofar toilet din sosai ba kawai sai ta shigo ta kamani itama sunan Allah kawai take kira tana fad'in." Shikkenan gashinan ma ya fita cikin sau'ki sannu bari yanzu na tura Masa'udu ya je pharmacy ya sayo miki wasu magunguña ba sai mun je asibiti ba in sha Allahu, Allah Ya takaita miki wahala duk abinda ya yi saura zai fito cikin salama idan an yi amfani da maganin."
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 106
Ban damu da jin abinda ta ce ba tunda na san aikinta ne. Ita da Baba Tabawa suka gyara toilet din tsaf. Baba Tabawa dai sai jajantawa take yi har da 'yar k'wallarta tana fad'in." Namiji ne gashinan har Ubangiji ya fara yi masa hallita. Hauwa da suke aikin tare uffan ba ta ce mata ba ta yi mata shiru kawai. Ina zaune a gefan gadon Baban ta zo ta fita da wata leda a hannunta tana fad'in. "In banda abinki Hauwa ya za a yi ya jefa d'an mutum a masai ina gaya miki gashinan Ubangiji ya fara fitar masa da hallitarsa.
Ido na bi ta da shi Hauwa ta fito daga toilet din tana fad'in." Magana ai ta mutu Baba ki je ki kai a bunne shi tunda haka aka koya miki a makarantar islamiyarku ta mutanan da."
Na dube ta a tsanake na ce." Abinda ya fita za a binne?"
Ta gyada kanta tana fad'in." Haka ta ce, shine ta tattare ta zuba a leda wai ita dai ba da hannunta za a zuba d'an mutum a masai ba."
Murmushi kawai na yi na ce." Hauwa kin san mutanan da camfi, wasu fa har yanzu suna wanke mahaifa tsaf su shiryata da likkafani su bunne. Ko musulunci an ce bata da wani amfani
Ta ja tsaki tare da furta." Mu a asibiti ma wallahi tattarasu muke yi a buhu a kai bola. Bata da wani amfani face zaman da ta yi da d'anka a ciki."

Shiru ya biyo bayan maganarta kafin ta numfasa a hankali ta ce." Wallahi Amina sai na ji Ina ma ace ni ce na samu wannan matsalar kin san Allah ba na k'aunar cikin nan da yake jikina."
Na dube ta domin ni lamarinta ma yanzu ya daina ba ni mamaki, yadda ta tsananta kiyayyarta akan mijinta kamar ba jininta ba shine abinda yake masifar daure mini.
Ni zullumi da tunanina ma yadda zan sanar da mai cikin ya zube ya amince kai tsaye ba tare da ya juya lamarin ba shine kawai abinda ya fi damuwa ita kuwa na fahimci yanzu gabad'aya ta daina tsoronsa balle ta daga masa kafa.

Sai da na ci abinci tukkuna ta gwada mini duk yadda zan sa magunguñan da ta bayar a rubutuce aka sayo mini sannan na kwanta ita kuma ta tashi ta fita. Bacci ne mai nauyin gaske ya d'auke ni wanda cikinsa na kasance cikin hargitsin mafarkai marasa ma'ana.
Shigowar kira a wayata dake gefena shi ya tashe ni cikin firgici na tashi zaune wanda ya yi daidai da tsinkewar jini da k'arfinsa wanda nake da tabbacin ya huda zanin jikina kuma babu makawa sai ya shafi mashinfidin da yake kan gadona.
Wayar na d'auka na duba Hamusu ne da sauri nasa a kunnena. Jin shi cikin nutsuwa ya sanya hankali ya dan kwanta kad'an na amshi gaisuwar da yake miki kafin na tambaye shi su Kamalu da fara'a mai yawa a tare da shi ya ce mini gamu a ciki tasha a tare dama kiran da na yi miki kenan yanzu za mu wuce gida."
Na sauke ajiyar zuciya tare da furta." Alhamdulillahi, ka gaishe mini da Gwaggo idan an jima da daddare na d'an samu nutsuwa a lokacin zan kira ka sai mu kàrasa tattauna yadda za a yi."
Ya ce." To shikkenan anti sai na jiki in sha Allahu."
Kashe wayar na yi na ajiye saman bedlamp kafin na zuro kafafuna kasa a hankali. Baba Tabawa ta turo d'akin ta shigo. Sai na sauke ajiyar zuciya domin na ji dadin shigowartata.
Ta nufo ni tana fad'in." Sannu ai na shigo ya kai sau biyar ba ki tashi ba ga la'asar ta yi babu kyau bacci a irin wannan lokacin.
Na ce." Tunda nasha magunguñan jikina ya mutu amma dai ciwon marar da sauki alhmdullhi sai jinin da yake zuba shine abinda ya d'an ba ni tsoro.
Ta ce." Ai wannan dole ne sai a hankali zai dinga janyewa." Ban ce komai ba na tashi a hankali na nufi bandaki ina fad'in." Baba ki dan fito mini da wasu kayan tare da audiga sai ki miko mini."
Ta amsa cikin kulawa. Wanka na yi da ruwan d'umi na gasa jikina sosai na shirya a toilet din na fito. Lokacin har ta cire zanin gadon da ya baci ta shimfida mini wani tare da sanya turaran wuta. Ina fitowa ta shiga bandakin da bedsheet din a hannunta.
Bata fito ba sai da ta wanke zanin gadon tare da kayan da na cire ta fito dasu a boket ta fita can haraba domin shanyawa.
Sai bayan sallar magriba Hauwa ta sake shigowa ta duba ni, mun kai kimanin minti talatin a tare muna tattaunawa kafin ta fita.
A lokacin na samu sararin kiran Hamusu a waya gaishe ni ya sake yi kafin cikin inda-inda ya ce dama yanzu nake cewa bari na kira ki a waya gani nan tare da Gwaggo ma."
Na ce." Allah sarki ba ni ita to."
Tana kar'bar wayar cikin kulawa na gaisheta tare da tambayar yanayin jikinta ta amsa itama da kulawa.
Sai da na d'an nisa tukkuna na fara yi mata bayanin duk abinda yake faruwa. Bata katse ni ba har sai da na kammala maganata kafin daga bisani ta ce." Hamusu duk ya yi mini bayani Amina kuma ai maigidan naki ma bai jima da tafiya ba mun jima muna tattauna magana akan lamarin rayuwar nan hakuri ake yi da d'a da dukiya duka babu wanda ya san mai amfanarsu sai Allah."

Kaina ya yi masifar daurewa jin abinda take ce wa, gabad'aya tunanina sai ya tsaya cak! ya aka yi ya san abinda na shirya ko dai Hamusu ne ya gaya masa. Ita kuma Gwaggo mai take nufi da wannan maganar wato ita ba ta kishin nata kenan, tun asali ban santa da son abin duniya ba balle na ce ya rud'eta da kudinsa.
Na ji maganar Hamusu yana cewa anti abinda ya faru shine d'azu bayan na sauko yaran nan a tasha sai na zarce dasu kasuwa domin saya musu kaya da abubuwan buk'ata kamar yadda ki ka bada umarni. A hanyarmu ta dawowa wallahi Sukairaju ya d'auko Yallabai a mota zuwa airport ya hange mu don shi bai ma gan mu ba shi Sukairajun ne ya gaya masa shine fa ya sanya shi ya biyo bayanmu har gidan Gwaggo. Babu yadda zan yi anti dole ta sanya na gaya masa komai a gabansa Gwaggwo ta yi fad'a sosai domin kin san ni da ke ba mu gaya mata matakin da muka dauka ba, anan ta sake tabbatar masa da cewa ita ta bashi yaran tun lokacin kwanciyata a asibiti kuma kyautar tana nan ba ta janye ba.
Wannan dalilin ya sanya shi d'aukarsu amma ya ce zai a jiye su a gidan Hajja tunda ba kya son zamansu a abujan. Kyauta kuma ya kar'ba har abada."
Wani irin takaici marasa misaltuwa ya lullubeni. Mutumin nan ya zame mini bala'i ta kowace siga dole sai ya tan'kwarani. Ban san lokacin da wasu lafiyayyun hawaye masu zafi suka fara silalowa kumatuna ba. Kashe wayar kawai na yi na ajiye ina jan hanci zuciyata kamar ta buga. can kamar saukar tsawa na ji saurin muryarsa a falo. Gabana ya fadi sosai domin kuwa wannan sautin ba na sa ba ne aro shi ya yi. Asali muryarsa sanyi ne da ita ko fad'a yake yi asalin muryarsa ba zata gigitaka ba sai dai zafin ba'kaken maganganunsa.
Ban yi yun'kurin fita falon fa saboda bala'in haushinsa da nake ji a raina nasan dai dole zai shigo d'akin ya same ni. Baba Tabawa ta a shigo a gaggauce tana fad'in." Idan za ki iya fitowa falon ki fito Amina, mijinku ya shigo yanzu amma abin babu dad'i tsakaninsa da Hauwa."
Na ce." Ka kyale shi kawa Baba, fitowata ba zata amfanar da komai b.... Ban kai ga rufe bakina ba na ji kukanta da maganganunta 'kasa-''kasa
Baba Tabawa ta ce." Marinta yake yi fa." Na diro daga gadon da gaggawa "Duka!" Na furta da mamaki mai yawa, ai ba halinsa ba ne. Bar shi da ba'kar gaba da bakaken maganganu amma baya dukan mace. Bai ta'ba kai hannunsa jikina ba.
Daidai lokacin da ya ke ce wa." Ke kadai ki ka zo, kuma ke kadai za ki fi ce mini daga gida. Yara kuma ita na yi niyyar bawa Maryam zan bawa, ban yarda da tarbiyarku ba."
Tana kuka ta ce." Ai gado muka yi da ni da kai. Tunda abinda ya yi Hauwa shi ya yi Tajo. Hajja ta saki nono ta bawa Uwani ni dai duka babu na za'ba, Allah Ya saka mini."
Ya sake kai mata mari ta goce tana fadin." Ni ma rabon shan wahala ne ya sanya ni auranka, kuma in sha Allahu mun rabu kenan har abada, kuma sani cewa wannan masifar daka 'kunsa mini sai ya shiga masai."
Chapter 11 · 0% Book details