← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 43

Sashe 35

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gida ya watse kowa ya tafi don a washe garin ranar su Hajja suka tafi har da yaran gabad'aya sai ya zamana gidan daga ni sai Baba Tabawa da Sultan (Baba Amadu) shine muke kiransa da sunan. A daran ya shigo mini da yaran gabad'ayansu Khalil twins Minal sai suka zama baki. Suka rakube a kujera sun kasa sakin jiki kamar ba gidan ubansu ba, abin ya ta'ba mini zuciyata kwarai da gaske sai da na shiga d'akin na ci kukana na koshi.
Na fito na tarar da Baba Tabawa tana ta hidima dasu kayansu tsaf an shigo dashi ta gyara musu d'aki tunda akwai d'akina a falon na mu. Na tambayi Khalil Baban nasu ya ce mini yana saman bai sauko ba. Kai tsaye can na nufa na same shi cikin jallabiya Bai jima da yin wanka ba. Kusa dashi na zauna da yake hankalina ba a jikina yake sosai ba ban fahimci dawa yake waya ba sai dai katse kiran da ya yi yana fad'in zai sake kira zuwa an jima shine abinda ya d'an ja hankalina domin sau tari yakan yi wayoyi muhimmai a gabana na sirri wanda ya kamata ya boye mini ma a gabana yi yake yi. Na tsargu sosai da abinda ya yi a yanzu na dinga kallonsa domin karantar yanayinsa babu yabo babu fallasa a tare da shi.
Na ce." Mai zai hana Mairo mai'aikin nan da take hidima da yaran nan ta dawo nan . Naga sun saba da ita sosai za ta taimakawa Baba Tabawa kada abin ya yi mata yawa."
Ya gyad'a kansa yana fadin." Yadda ki ka ce a yi hakan za a yi, na kuwa ji dadin shawararki." Na ce." Sai magana ta biyu yaushe Hauwa za ta dawo?"
A tak'aice ya ce." Wannan kuma ita za ki tambayata hajiya."
Na yi shiru Ina kallonsa da mamaki a tare da ni na ce." Ai ka ce ka yafe mata ya kamata ku tattauna a tsakaninku ko?"
Ya gyad'a kansa yana fad'in." Na yafe mata mana, amma tsakani da Allah ni zan dinga binbininta, kofa a bud'e take haka zalika ma dakinta yana nan ta dawo duk lokacin da ta shirya bai dame ni ba."
Na ce." Wannan ba magana ba ce Allah Ya taimaka, wata'kila ai bata ga fuska a wurinka ba."
Ya 'bata rai yana fad'in." Ki kyale ni da wannan maganar Amina kada ki bata mini rai ko abin ya shafe ki ne?"
Na yi shiru ina kallonsa kawai kaina na sarawa. Zan kira Hauwan na ji ta bakinta.
Ya ce." Ya kike ganin za a yi da yaran nan Salim da Adamu. Za ku ri'ke su tsakani da Allah ko kuwa na bari dangin Mamansu su d'auka tunda ita Nusaiba tana d'akin mijinta."
Da tsananin takaici da b'acin rai na furta." Wace irin magana ce wannan don girman Allah, ka dinga tauna harshe kafin ka gaya mini magana, ni fa mutum ce mai zuciya a kirji, kada na gaya maka ba'kar magana ka ji haushi."
Ya yi murmushi irin na saman lebe kafin ya ce." To ai na zuba Ido ne naga za ki yi mini magana akansu na ji baki ce komai ba bayan kin san amana suke a hannuna, me yasa zan kawo muku su ba tare da na nemi amincewarku ba, kin yi magana akan mai dauwaniya da yaranku sannan kin yi magana akan Hauwa shiyasa na ce to bari na tunasar da ke"
Na danne abinda nake ji na ce." Amma dai kasan idan ka kawo su gidan nan zan kula da su ko? Ni ma ai ta ri'ke mini nawa, kai ko bata yi mini alheri ba, ro'kon maraya sai wanda Allah Ya so wallahi su zo su zauna zan yi iyakacin bakin kokarina."
Ya sauke ajiyar zuciya Yana fad'in." Alhamdulillahi, ita Hauwan fa, tunda ai bakinku daya kina magana da yawunta." Ban biye masa ba tunda na fahimci neman magana yake yi na ce." In sha Allahu rabbi babu matsala itama."
Sai ya saki fuskarsa yana fad'in." To na gode sosai, mu taru cikin ladan da ni daku gabad'aya mu tashi a gefan manzon rahama, domin fadinsa ne duk wanda ya rike maraya ya kula dashi sosai to a ranar 'kiyama za su tashi tare.
[12/21, 7:01 PM] bintaumarabbale: 120
Na so na share sha'aninsa da Hauwa amma na kasa hakurin tsame kaina. Kad'aici ne ya yi mini yawa da tunani da zullumi. Ban gazgata maganar nan da ake ta yawaita fad'a ba wato kishiya abokiyar zama ce sai yanzu. Ko babu komai bibibiyu tana da dadi idan baba Tabawa ta shiga kicin babu motsin yaran suna makaranta ita kuma mairon taje garinsu tun bayan rasuwar Hajiya Maryam din bata dawo ba amma dai ni da kaina na yi waya da ita tace mini in sha Allahu tana kan hanya. Gani ni ba ma'abociyar kallon ba wasu lukutan nakan kira Sahura a waya mu yi hira ko anti Yagana amma dai duk da haka mutum ai rahama ne. Wani sa'in na kan bita kicin din na sanya mata hannu mu yi aikin tare muna hira irin ta yau da gobe hum rayuwa kenan.

Ajiyar zuciya na sauke na d'auki wayata dake ajiye a kusa da ni na lalubi lambarta. Bugu d'aya ta yi ta d'aga gaisawa muka yi cikin kulawa kafin na daure na yi mata tambayar da take damuna a kasan raina.
Irin murmushin nan na takaici ta yi. Duk da ba ni ganinta nasan a cikin kunci da takaici take. a dusashe babu wani kuzari ta ce." Amina ban ga fuska ba har yanzu, na yi lefi na kar'bi laifina kuma na bawa duk wanda ya cancanta hakuri amma mutumin nan na kira shi yafi sau ashirin bai daga mini waya ba. Yanzu da za ki duba duka wayoyinsa za ki ga text messages dina na ban ha'kuri da kar'bar kuskure amma bai ce komai ba. Ya zan yi, ina so kafin ace na dawo mun d'an sasanta junanmu duka sai mu yafi juna tunda shi ma yana da lefi har ta'aziyar matarsa na yi masa amma hakan duk bai sanya ya saurareni ba."
Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Ke ma dai da wata magana kike Hauwa, ai tunda iyaye sun shiga ciki kuma da bakinsa ya ce ya mayar dake tuntuni tun kafin ma ki haihu a ganina kawai ki dawo ki rungumi jaririn yaron nan da bai fi kwanaki talatin a duniya ba. Idan har sai kin tsaya kin ji ta bakinsa ko sai ya kula ki wallahi yana gane hakan zai fara gwara kanki a garu tunda dama shi kin san rarrashi da kwantar dakai baya yi masa. A shawarce kawai ki dawo idan ya so koma me zai faru a tsakaninku ki kawar da kanki har ya gama kullacinki ya sauko nasan dai zai yi ta takalarki zuwa yanzu ai ya ci ace kin gama gane halayensa."
A sanyaye ta furta." Shawarar da muka yanke kenan ni da Inna, in sha Allahu cikin satin nan zan dawo, Amina na gode sosai da kulawa."
Cikin jin dad'i na ce babu komai Hauwa Allah Ya kiyaye faruwar hakan anan gaba. Ta amsa da Amin." Kafin mu yi sallama.
Ban gaya masa yadda muka yi da ita ba kawai na ja bakina na yi shiru sai dai Ina ta zuba Ido naga dawowar su Salim gidan kamar yadda ya gaya mini amma yau kusan kwanaki goma kenan da maganar ba su dawo ba.
Da daddare bayan ya gama cin abinci a tsanake na fara tambayarsa. Sai da ya kashingida tukkuna ya ba ni amsa da ce wa. Sun sake yanke shawara da 'yan uwan Momi din akan cewa Nabila za ta dawo gidan ta zauna domin ta cigaba da kula da su tunda dama bata da aure sannan kusan ta fi kowa Ido da shakuwa da Momin, ta san abubuwa da yawa da suka shafeta mussaman harkokinta na yau da gobe, muhimi dai manyan kadarorinta an kasafcesu kamar yadda addiini ya tana da an raba gado nasa wanda ya gada a matsayin mijinta ya barwa yaran gabakiya dukiyarsu tana hannunsa gabad'aya shagunanta na nan ne aka cigaba da hada-hada kamar yadda yaran suka bukaci da a yi musu hakan. Dalilin dawowar Nabila gidan kenan domin ta taimakawa yaran wurin kula da harkokin kasuwancin tunda suna so su dora daga inda Maman nasu ta tsaya ne."
Zuciyata daya na ji dad'in hakan a raina, domin a ganina dawowar Nabila kusa da su za su ji dad'i koyaushe idan sun juya za su ganta a makwafin mahafiyarsu tunda jini ai ya fi karfin wasa. Ko nan din suka dawo ba za su sake sosai ba tunda ga abubuwan da suka faru a baya amma idan suna ganinta a koyaushe a gidan za su ji dad'i.
Addu'a sosai na yi wa yaran tare da yi musu fatan alheri akan abinda suka niyyata Ubangiji Allah Ya yi mana jagoranci bakidaya ita kuma Allah Ya yi mata gafara.
Chapter 35 · 0% Book details