← Book details Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 43

Sashe 29

Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 4 min read

"Ai Amina mutuwa wa'azi ci ga duk wanda Allah Ya sa zai hankalta, duk d'aukaka da sharafin mutum a duniya ba iya tsallaketa. Mu 'yan adam ai muna da mantuwa shiyasa muke ganin kamar ba za ta zo kanmu ba, a yadda dai kike ba ni labarin irin abinda Hauwa take yi wa matar nan wallahi ita ya fi kamata mutuwar ta dake ta, ta kuma ji tsoron Allah har ta mutu bata nemi afuwarta ba Allah baya yafe hakkin wani akan wani har sai wanda aka zalinta ya ce ya ya yafe, aikin banza ai kishi ba hauka ba ne, ni kaina Hauwa ta ba ni mamaki kuma na raina wayo da iliminta domin jalihi ne kadai ba zai fahimci cewa ba hassada take yi wa baiwar Allah nan ba."
Shiru na yi Ina ta auna maganganun da take yi. Ni kaina na kan zauna na yi ta nazari akan mai yasa Hauwa ta zafafawa matar nan da yawa. Kishi ne ko hassada mai yasa komai sai ta mayar da shi rigima da sa'insa lefi ni aka yi wa amma ban yi irin abubuwan da take yi ba, tabbas dole a dora ayar tambaya a kanta koda kuwa ba hakan ba ne a zuciyarta ni kaina ba zan fita daga zargi ba tunda yan uwanta da yawa suna ganin cutar da ita muke yi ta hanyar hade mata kai da yi mata tawaye tare da fito da kishi muraran. Idan zan kwana ina rantsuwa da Allah kan cewa ba ni yi mata hassada da b'akinciki babu wanda zai yarda.
Haka na kwana cikin zullumi da nazari na tashi da ciwon kai irin na gefe damuwa da tunani da rashin bacci. Misalin tara saura Baban Saude ya kira ni yana tabbatar mini da cewa suna kan hanya suna da d'an yawa.
Na kira Babanmu ya ce mini shi ma sun taso su uku har da Ummansu Hadiza.
Wanka na yi na kintsa na fita falo cikin hijabi har kasa na samu Baba Tabawa itama cikin hijabin da carbi ta kammala abin kari da d'an dama. Da asuba na ce ta yi abinci da yawa saboda bakin da suke tafe. Muka gaisa tare da sake yi wa juna gaisuwa. Masa'udu tare da
Sale suka shigo da akwati kafin shigowar Hajjan Kamalu ne ya fara shigowa tukkuna suka shigo Hajja da Gwaggo da Hamusu a biye a bayansu.
Bakin kofar na isa da sauri ina yi musu barka da zuwa. Na kar'bi jakar dake hannun Hajja ina fad'in." Gwaggo sannunku da hanya Hajja kun yi sauri sosai fa kamar a hanya kuka kwana.
Suka zauna a kujera tana fad'in." Da asuba muka taso ai, kuma dai Garba ya kure gudu sosai shiyasa Allah Ya kawo mu."
Na nutsu sosai muka gaisa a tsanake Hamusu dake can saman kujera mai cin mutum d'aya ya gaishe ni na amsa tare da tambayar iyalinsa da yaronshi Arif da bai wuce shekara biyu ya ce mini duk suna lafiya. Baba Tabawa bayan sun gaisa da yi wa juna ta'aziyya na ce ta kawo musu abin kari.
Na dubi Kamalu dake gefe a tsaye jikin labule ya sake girma da fad'i sosai suffa ta mazantaka ta bayyana a tattare dashi har da gemu ya fara ajiyewa. Yatsansa makale da carbi mai lamba yana ta rarraba Ido a kanmu yanayinsa gabad'aya kamar mai nazarin wani abu damuwa da tashin hankali sun gama bayyana a tattare dashi. Ganin mun had'a Ido dashi ya sanya ni janye nawa idon. Ina jin wani abu na taso mini da tashin hankali. Ya gurfana a gabana cikin kula da ladabi ya furta."Mama ina kwana ya muka ji da hakurin wannan rashi."
Na amsa da "Alhamdulillahi mun gode Allah."
Ya furta." Allah Ya jikan Momi Ya gafarta mata."
Gabad'aya muka amsa a falon.
Na dubi Hajja tare da fad'in." Yusi bai samu zuwa ba ne?'
A tsanake ta ce." A a ai tare duk muke tafe tun a waje ya ce Garba ya ajiye shi yana can tare da Adamu."
Na gyada kaina ba tare da na sake cewa komai ba. Baba Tabawa ta kawo tire uku masu girma cike da abin kari na taimaka mata wurin zubawa kowa Hajja ta ce ." Hajiya Saratu tana tafe in sha Allahu mun yi waya da Alhaji Haruna shi da d'an uwansa Alhaji Dahiru sun ce za su yi kokarin samun jana'iza." 'Yan uwan mahaifin maigidan ne Wanda a yanzu su kadai ne suka rage musu a family din. Na gyada kaina a sanyaye na ce." Allah Ya kawo su lafiya.
Chapter 29 · 0% Book details