Sashe 22
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da zai tafi ko sallama bai yi mana ba, sai da ya kwana uku ma da tafiya tukkuna muka samu labari a bakin Masa'udu cewa ya tafi ban ji komai a jikina ba, dalili na riga nasan irin rabuwar da muka yi ta rashin arziki ba zata bari ya shigo ya yi mana sallama ba.
***
To kwanaki suka cigaba da tafiya har aka fara lissafin watanni da tafiyarsa bai kira waya ba haka zalika mu ma ba mu kira ba. Sai na so tsokanar Hauwa tukkuna zan ce mata ta kira shi a waya ta ji yana lafiya. A lokacin zan ga b'acin ranta ta dinga fad'in mijinki dai Amina, ki daina danganta ni da wannan rikitaccen tsohon. Na yi ta dariya idan tana hayaniya a raina nakan ce jinin jikinku kuma yana yawo a junanku tunda duk rintsi a ba za a canzawa towo suna ba.
Babu wata ala'ka da ta sake had'a mu da Momi, tun bayan rigimar Hauwa da Nabila kanwar ta itama ta kama kanta, farko farkon zaman takan shigo mana amma tun sanda Hauwa ta yi mata cin mutunci ba ta sake shigo mana ba yanzu kusan watanni biyar kenan. Sai dai duk ranar juma'a takan turo mana yara su gaishe mu wasu lukutan har da abin arzikinta. Duk sanda ta aiko mana da abu sai dai ni nayi d'auka amma Hauwa ko kallo abin bai isheta ba. Kiyayyar da take nunawa matar tana bala'in ba ni tsoro. Kyautar Momi mafiakasari perfumes ne masu dadin kamshi wasu lukutan ni nake amfani da su, ko kuma na yi kyautarsu. Ni dai har yanzu ban kulleceta ainun ba domin sai nake ganin kamar ba ni da wata hujjar da zan tsananta gaba da kiyayya a kanta tunda a zahiri ko mun ki ko mun so matar mutum ce har da rabin mutum. Ko ga yanayin yabo da k'aunar da mutane ke yi mata ya ci a ce sha'aninta ya daina daga mana hankali ko sanya mana zazzafan kishi. Makasudi dai mijinta shine yake ta yun'kurin dole sai ya 'batata a wurinmu ya dasa mana kiyayyarta dangane da abinda yake yi a kanta ba kowace macace za ta jure ba.
Kadaran kadahan nake jin ta a zuciyata. Kuma ba na jin haushinta ainun sai dai irin kishin nan da ba za a rasa ba. A ko'ina zan fad'a alheri ta yi mini don yara sun shiga tsakaninmu hakan ba zai sanya ni na mance ba. Na dai nesanta yarana da ita shikkenan sai a zauna lafiya.
Sosai Nusaiba da Salim suka d'auki gaba matsananciya da mu. Adam ne kawai yake iya daurewa idan tsautsayi ya sanya mun had'u ya gaishe ni, amma tun ranar da su Yusi suka bar garin gabad'aya ya gaina shigowa gidanmu. Salim da 'yar uwarsa Nusaiba kam abin na su ya yi nisa idan za mu had'u sau goma cikinsu babu wanda zai dubi inda nake balle na sanya a raina cewa za a gaishe ni.
Yusi bai ta'ba gaya mini ce wa Adam ya ziyarce shi har sau biyu ba duk kuwa da cewa yakan kira ni a waya sa'i da lokaci mussaman a ranakun da ba su da makaranta tunda tuntuni sun cigaba da d'ora karatunsa a bayaro wasu lukutan ba su da isheshen lokaci mussaman Kamalu da ya ri'ke b'angare biyu. Karatu yake yi sosai irin na da'awa sosai yake bin Malam sunna domin samun ilimi kwanaki satinsa guda a bauchi wurin Sheikh Guruntum. sai bayan da ya dawo tukkuna yake gaya mini da na tambaye shi dalili ya ce mini yana zuwa neman sani ne. Yanzu dai yana tare da Shaikh Abdullahi gadon-k'aya yana daya daga cikin yaransa da suke take masa baya.
To a bakin Hamusu nake samun labarin zuwan Adam din don har yake gaya mini irin kayan da Momi din ta aikowa da Gwaggo ta hanyar Adam din.
Na yi mamaki sosai kuma jikina ya kara yin sanyi da lamarinta a yi alheri da kyauta hannun hagu bai sani ba. Duk yadda na nuna mata rashin 'kara da kawaici akan yaran nan k'okarinta zumuncin nan da take ta nanata mini ya cigaba da tabbatuwa.
Ubangiji Allah Ya ba mu ikon yin abu dominsa.
Haka dai rayuwar ta cigaba da tafiya a hangunce ta fannin maigidan namu kam yadda ba mu neme shi ba shima bai neme mu ba. Tun abin baya damuna har ya fara damuna mussaman da bikin Fadila babbar diyar anti Yagana ya tashi. An yi bikin Yusura sati uku da suka gabata lokacin muna tsaka da rikici dalilin da ya sanya ma kenan ban tambayeshi ba domin kuwa nasan zai huce fushinsa akan hakan ya samu damar gasa mini maganar da ransa yake so kuma ya hana ni zuwa, saboda kada dukan ya zama biyu ya sanya na k'yale shi.
Hajja da kanta ta kira ni a waya game da zuwa bikin Fadila da suke shirye-shiryen tafiya ita da Gwaggo tare da yaran wato su Kamalu ai anti Yagana mutuniyarta ce don haka ban yi mamakin nuna za'kuwarta akan sha'aninta ba. Rasa abinda zan ce mata na yi na kama inda-inda da kyar dai na ce mata ni ma ina nan ina shiri amma wata'kila za su riga ni yin gaba. Ba ta fahimci cewa da matsala ba muka yi sallama na ajiye waya cikin zullumi da tunanin yadda zan sanar da shi tafiya maiduri ya bar ni kai tsaye. Da kunya kusan wata hud'u da tafiyarsa ban kira shi ba bayan kuma nasan da tsananin fushina ya tafi yanzu kuma na kira shi nace masa me?"
Haka kwana biyun nan na kasance cikin yanayi na tunani har sai da Hauwa ta fahimta ta tambayeni na gaya mata halin da ake ciki. A lokacin itama jikinta mutuwa ya yi ta dinga fad'in lallai a wannan ga'bar baki da bakin magana Amina. Bikin Fadila kuma ai ke ce kirjin biki, idan ba ki halarta ba akwai matsala gaskiya.
To katsam ina cikin wannan halin ya zo ba tare da tsammanin zuwan nasa ba, tunda ka'ida wata shida muke yi a can legos din mu dawo, wai Ashe Momi ce babu lafiya hawan jini da sugar har sai da ta kwanta a asibiti tsayin kwanaki goma ba mu sani ba.
A bakin Masa'udu muke jin wannan labarin domin kuwa shi din ma ya tabbatar mana da zuwansa kamar yadda ya tabbatar mana da tafiyarsa. Bai shigo mana a ranar ba sai washe gari da rana wajan daya da minti biyar lokacin ma daka gani daga massalaci ya fito.
Muna falo gabad'aya muka yi masa barka da zuwa ya amsa kadaran kadahan babu fushi haka zalika babu cikakkiyar walwala. Ya tsaya suna magana da Baba Tabawa kamar yadda suka saba har yana ba ta labarin rashin lafiyar Momi din da yadda ta ji jiki. Sosai ta dinga jajantawa tana k'ara tabbatar masa da cewa gabad'ayanmu ba mu sani ba. Wannan karon Hauwa ba ta tashi ba ban sani ba ko nauyin da jikinta ya yi mata ne oho, tunda cikinta a cikin wata na takwas yake ya fito sosai idan ta jibge a wuri d'aya da kyar take tashi. Ya kama hanyar samansa babu wadda ya sake kalla a cikinmu. Amma yanayinsa kadai ya tabbatar mini da cewa lalurar da matarsa take ciki ta dame shi saboda ga yanayin yadda yake bawa Baba Tabawa labarin ciwon tabbas ya ci jikinta da k'arfi.
Bayan shud'ewarsa daga wurin da kamar minti goma na tashi na bi bayansa zuciya cike da zullumi da fargaba.
A kwance na same shi kawai ya tsirawa rufin d'akin ido. Gabad'aya sai gwiwa ta yi sanyi (wai shin me cece ma duniyar nan ne) tausayinsa ya d'an kamani, amma bari tasirin hakan ya raunarta da ni ba. Har yanzu da sauran takaicinsa a cikin zuciyata.
A nutse na zauna gefan k'afafunsa. Ya dube ni bai ce komai ba sai ya janye idanuwansa. Na sauke ajiyar zuciya a hankali na ce." Wallahi ba mu san ta yi ciwo ba, ashe har kwanciya ta yi a asibiti babu labari ai da mun shiga mun dubata."
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Sai na janye idona daga kansa na yi kasa da kaina ina dan wasa da yatsun hannuna. Shiru d'akin ya yi na minti kusan goma kafin na sake dubansa yanzu idonsa a lumshe yake kamar mai shirin bacci ganin haka sai na tashi da niyyar fita. Ba tare da ya bud'e idon ba ya ce." Koma ki zauna ina son magana dake."
Na zauna din kamar yadda ya buk'ata. Ya tashi zaune tare da sauke k'afafunsa kasa. Ya dube ni a nutse kafin ya furta." Akwai matan da annabin rahama ya fad'a cewa ya gan su a can karkashin wutar jahanama, kuma suffofinsu sukan bayyana tun a duniya. Akwai kuma matan da tun a duniya za a dinga yi musu ishara da nuni da cewar aljannar Firdausi madawamiya ce a gare su. Sune muminai wad'anda ayyukan alherinsu yake bayyana ga ko'ina."
D'akin ya yi tsit bayan ya gama maganarsa. Na dube shi tare da furta." Ni ina a wane babi kenan, ai ba kai kake bada aljanna ba."
"Tabbas ba ni nake bada ita ba, amma tana k'asan kafafuna haka annabin rahama ya fad'a."
Sai da na d'aure sosai kafin na furta." Ayyukana ba su kai ka daga mini kafa ba kenan?"
Ya gyada kansa yana ce wa." Gaskiya ba su kai ba har yanzu. Momi ce ko yau ta fad'i ta mutu wallahi na yafe mata ki shaida aljanna da izinin Allah zata tabbata a kanta."
Na yi shiru zuciyata tana hantsilawa saboda tsabar bala'in b'acin rai. Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un na cigaba da nanatawa ban sake mayar masa da martani ba, kuma ban tashi daga wurin ba na ji gyaran muryarsa yana cewa." Kwanaki mun yi waya da Hajja take sanar da ni za su tafi maiduguri da yaran zuwa hidimar bikin 'yar Yagana hakane ko."
Ban dube shi na ce." Hakane yau saura kwana tara, jiya dai Hajja take ce mini ranar alhamis za su tafi."