Sashe 36
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 9 min read
Ranar lahadi Hauwa ta sauka bayan la'asar. Na yi farinciki sosai da ganinta domin ko waya ba ta gaya mini ba sai kawai ganin Masa'udu muka yi da akwati lokacin ni da Mairo muna falo a zaune muna kallo baba Tabawa na kicin domin shirin dora sanwar dare yaran kuma na tahafiz. Masa'udu ya dire akwati bayan ya gaishe ni yana fad'in." Hajiya k'arama ce ta dawo." Ya juya ya fita da sauri ya sake shigo da wata akwatin k'arama.
Na dinga dariya ina fad'in." Hauwa wace irin bazata ce wannan?"
Ta nemi kujera ta zauna tana ce wa." Dama ai na gaya miki cikin satin nan."
Na gyada kaina ina cewa." To me yasa ba ki yi mini waya ba."
Murmushi kawai ta yi tana duban Mairo na ce." mai aikin Momi ce ba ki gane ta ba itace uwar dakinsu Khalil."
Mairo na dariya ta furta." A a Hajiya ina ni uban masu gida ne fa kuma uban d'akina.
Ta d'an risina tana gaishe da Hauwa cike da ko'karin bata girma.
Itama ta amsa da sakewa da murmushi a saman fuskarta. Baba Tabawa ta fito daga kicin bayanta goye da Sultan yana dan kusurkusur. Ganin mu tare da Hauwa a zaune sai ta d'an yi saroro kafin kuma ta saki fuskarta da azama ta k'araso tana ce wa." Hajiya Hauwa sannu da zuwa."
Ta amsa da "Yawwa Baba Tabawa ina yininmu ya kokari?"
Baba Tabawa ta amsa da "Lafiya lau alhmdullhi ya aka baro su inna Uwani."
Ta ce." Duk suna nan lafiya suna gaisheku."
Baba Tabawa ta kwanto yaron tana fad'in." Kar'be shi ya ji duminki."
Ba tace komai ba ta sanya hannu ta kar'bi yaron ta rugume shi a kirjinta. Baba Tabawa da sauri ta juya ta nufi dakinta minti uku ta dawo da madararsa a dame a cikin fida ta mika mata lokacin ya sanya yatsunsa a baki yana tsotsa.
Ta kar'ba a dan sanyaye kafin ta yun'kura ta tashi da yaron ta nufi dakinta. Na dubi Mairo da ta kurawa tibi ido, tun zuwanta na fahimci ma'abociyar son kallo ce kuma American film duk da ba jin abinda suke fad'a take yi ba amma tana ganewa har idan na tambayeta tana fahimta kuwa tiryan tiryan ta ba ni labari. Na ce." Mairo shigar mata da akwatin nan dakinta. Ta tashi da sauri ta yi yadda na umarcta. Bayan ta fito sai na tashi na shiga d'akin na sameta zaune a gefan gado rungume da yaron ta gama bashi madarar ya koma bacci idonta ya nuna alamun kuka. Ta zuba mini ido har na zo na zauna kusa da ita bata janye idonta daga kaina ba.
A nutse na ce" Ya yi bacci kenan?" Ta gyad'a kanta tana fad'in." Amina sai dai Allah Ya sakawa yaron nan amma na zalince shi, zai rayu ba tare da ya d'and'ana nonon uwarsa ba, kin san dama ba ni da wani wadataccen ruwan nono wallahi ya fi sati biyu da d'aukewa. Dole a cigaba da ciyar da shi da madara kafin ya kai matakin cin abinci, idan na dube shi sai kunyarsa ta kama ni, ina fargabar ya girma a tashi maganar nan da duk abinda ya faru Ina ganin zai yi mini wani irin kallo wata'kila ba zai yi imanina ba kamar sauran."
Da sauri na ce." Haba dai ki daina fad'in haka Hauwa, dama haka Allah Ya shirya kuma ai d'a bai isa ya biya iyayensa hakkin dawaniya ba, ki daina fad'in bai zai yi imaninki ba, ai tunda ki ka sha wannan gwagwarmayar kafin zuwansa duniya wata'kila ma shine wanda za a huta dashi. Ke dai kawai ki cigaba da yi musu addu'a sannan kuma ki kiyaye faruwar makamanciyar wannan matsalar anan gaba.
A Dan sanyaye ta ce." In sha Allahu rabbi babu abinda zai sake faruwa Amina, zan kiyaye sosai ba ni kuma da bakin da zan yi miki godiya."
A nutse na dafa kafadarta na ce." Har abada babu godiya a tsakaninmu Hauwa duk abinda na yi miki kamar kaina na yi wa."
Na d'an jima a d'akin muna tattauna batutuwa mabambamta kafin na fito lokacin yaran sun dawo daga makaranta ina jin karadinsu a dakinsu. Kai tsaye can na nufa na same su tare da Mairo kamar koyaushe tana kiciniyar basu kayan da za su sanya bayan sun cire unform din. Na ce." Khalil Mama ta dawo tana d'aki maza ku je ku gaisa."
Hassana ta buga tsalle tana fad'in." Don Allah da gaske ne, dama Babanmu ya ce za ta dawo tana Makka haka ya ce mana ko Usai."
Ta yi maganar tana duban abokiyar tagwaitakartata. Na yi tsam Ina nazarin murnar da suka yi a zaman da suke yi momin bata rasu ba kenan ubansu ya ce musu tana makka jira suke yi ta dawo shiyasa kenan na ga sun saki jikinsu a kwanakin nan ba kamar sanda suka dawo gidan ba.
Khalil din dai bai ce komai ba tunda ya fi su wayo shi din ma ba gama sanin mutuwa ya yi ba amma ga dukkanin alamu bai yarda da maganar da baban nasu ya yi ba, don ban ga alamun murna a fuskarsa ba.
Ya fita daga d'akin yana gyara maballin rigar jikinshi. Bayansa na bi kai tsaye naga ya nufi d'akin uwar. Na sauke ajiyar zuciya cikin raina na furta Allah Ya sassauta mana bak'idaya.
Tare suka fito da Mairo wai sai sun tafi can gidan Momin tunda ta dawo. Na dube ta ina tambayar kukan mai Minal take yi ta gaya mini yadda suka yi a d'aki bayan fitata. Hassana ta yi hanyar fita tana janyo hannun Minal din suka fadi a bakin kofa domin ita Minal jikin ne amma babu kwari. Tsawar dana bugawa yarinyar ta yi daidai da shigowarsa. Ya gan su a bakin kofa durshen Minal na ihu!
Ya cicibeta ta tashi ya rike hannunta yana tambayata. Usai da take tsaye kusa da Mairo itace ta bashi amsa cikin yanayin maganarta tunda har yanzu hausar ba ta zauna a bakinta daidai ba tana gwaranci Hassana ta fi ta iya magana.
Ya 'bata fuska yana dan hararata ya ce." Ke kuma maimakon ki rarrasheta sai tsawa Amina, yaushe za su sake dake kina yi musu irin wannan hantarar."
Na ce." Yaushe na hantaresu?"
Ya ce." Karya na yi kenan, abinda gashi idanuna ya nuna mini."
Na yi shiru ban sake magana ba.
Fitowar Hauwa daga d'akin kafad'arta sa'be da Sultan ta d'auke hankalinmu. Khalil ya biyo bayanta da fida a hannunsa.
Da mamaki yake kallonta amma bai ce komai ba. Ga dukkanin alamu dawowarta shi din ma ta yi masa bazata.
Ta mikawa Mairo yaron tana fad'in." Ki goya shi yamma ta yi. Da sauri kuwa ta kar'be shi da towel din ta fara ko'karin sa'ba shi a baya.
Ta hillaci yaran suka shige d'aki tana fad'in." Za ta basu tatsuniyar bari wa biba, da ta duduwa mai kan 'bari. Jin haka ya sanya Usai sakin dariya tana tsalle suka bi ta a baya har da Khalil din. Amma ban da Minal domin ita kam tana ta k'ananun kuka. Ciccibarta ya yi ya daukota a hannu ya zo ya dire mana ita a gabanmu yana fad'in." Wacece uwarta a cikinku?"
Babu wadda ta bashi amsa. Ya dubi Hauwa yana fad'in." Wannan idan ba ki sani ba bari na gaya mini rigimammiya ce da kafiya da taurin kai. Momi Allah Ya gafarta mata itace kawai take iyawa da ita a duk lokacin da ta fara irin wannan koke-koken. Ba ki san wannan ba tunda ba ta rayu a hannunki ba. Abinda nake so na gaya miki akanta shine kada ki ce za ki dakar mini yarinya domin ba mu yi mata rainon duka ba. Minal idan ba a ta'ba ta ba tana da hakuri kwarai da saurin sabo, muddin kuwa ta fara wannan kukan nata babu shakka akwai dalili. Za mu samu matsala gagarima na ji labarin wataran kin kai hannunki jikinta. Kin saba dukan Khalil ki kwana kalau ban da wannan idan ki ka yi ranki zai 'baci mutuka."
Ta yi kasa'ke tana kallonsa har ya gama kafin ta ce." To yanzu ni ai ban san abinda aka yi mata ba. Idan har yaro ba zai yi kuskure a hukunta shi ba ai an d'auki ga'barar lalatashi ko ba haka ba ne Amina."
Na ce." Hakane kuwa, ina ga kamar wannan ba soyayya ba ce Allah Ya ja zamaninka."
Ya gyad'a kansa yana cewa." Ai na fad'a muku abinda yake raina ban munafurceku ba, ba ni son a ci zalin yarana amana ce a hannunku."
Shiru muka yi muna ta kallonsa har ya gama maganarsa ba mu ce komai ba. Sai ya sunkuya ya sunkuci yarinyar ya sanyata a k'ugunsa kamar wata 'yar yaye sai sakin ajiyar zuciya take yi.
Hauwa ta ce." Wai don Allah me aka yi mata ne?"
Na gaya mata duk yadda aka yi. Sai ta duba shi yana nufi hanyar samansa ta ce." Kenan ba ta san ni na haifeta ba ko?"
Ya juyo yana cewa." Ko ta sani to ta manta yanzu tunda babu sha'kuwa idan kin manta ai ni manta kyarar da hantarar da ki ka dinga yi musu ba a duk lokacin da suka kawo muku ziyara. Lefin wata ya shafe su, me yasa za su tuna dake."
Ta gyad'a kanta ba sake cewa da shi komai ba. Muna kallonsa har ya haura saman da yarinyar a 'kugunsa.
Ta zauna saman kujera kusa da ni jikinta duk a sanyaye..
Na ce." Kada ki wani damu neman na yi yake yi duk abinda zai yi ki kyale shi kada ki biye masa idan ya ga baki damu ba zai bari."
Ta dube ni da dan murmushi tana fad'in." Ina ganin fa don yarinyar nan takwararki ce yake fifitata a cikin yaransa. Ni dai fahimtar da na yi kenan Amina."
Na zuba mata Ido Ina nazarin maganarta ni duk irin abinda yake yi akan yaransa ban ta'ba tunanin yana fifita Minal saboda tana da sunana ba. Na fi tunanin soyayya ce kawai irin ta iyaye ai dole a cikin yara wani ya fi shiga cikin rai idan nuna fifiko da k'auna ne ai Khalil zai nunawa ko mai sunan Amininsa Amadu(Sultan) sai na gaza ce mata komai na dinga kallonta. Murmushi ta yi irin na saman leben nan tana fadin." Kin cancanci irin wannan soyayyar Amina domin ke din mutum ce har da rabi kuma da gaskiyarsa kina da hakuri da kawaici saurin sabo, Amma duk ranar da aka ta'bo ki to za a sha daga. Mafiakasari kuma haka duk mai d'auke da suna Amina yake.
Dariya maganarta ta ba ni na ce." Lallai Hauwa abinda na za ki fada kenan to na gode shine abinda zan ce."
Ta tashi tana fad'in." Bari na bi bayansa saman."
Ban ce mata komai na bita da kallo mai tafe da murmushi.
Lokacin sallar magriba ne ya tashe ni daga falon zuciyata cike da nazarin maganar Hauwa akan Minal.