Sashe 1
Gudun Aure Part 5 Complete Hausa Novel · about 8 min read
[12/16, 7:43 PM] bintaumarabbale: 100
Bayan shakara biyu. Hauwa tana da yara biyu Khalil da mai sunana domin tun ranar da ta haihu uban ya yi mata huduba da Amina sai muke kiranta da Minal. Lokacin Hassana da Husaina sun yi wayo sosai suna yawo ko'ina da 'kafafunsu. Na sake samun wani cikin ya samu matsala sakamakon wani mugun zazzabi da na yi mai zafin gaske lokacin duka Bai fi sati shida ba. amma cikin ikon Allah fitar cikin da wata daya na sake samun wani lokacin ina tare dashi a legos. Sai ya ce sai na koma abuja Hauwa ta zo. Dana tambayeshi dalili kawai sai ya ce a gidan Baby Nana ta rasu haka zalika ma a gidan na samu matsalar ciwo mai zafi har cikinsa ya zube hankalinsa bai kwanta ba. Maganar ma sai ta ba ni dariya amma na daure ban yi ba, saboda Ina gudun ya mayar da abin rigima ina dai ta nazari akan tunaninsa kamar akwai rashin tauhidi a ciki, baby Nana ga abinda ya assasa mutuwarta. Ciki kuma da na samu ya zube wannan kuma ni dashi ba zamu taba cewa ga musababi ba, iko ne na Allah, kuma a dai gidan ai na samu cikinsu Hassana da Husaina gashi duka watanmu hud'u da zuwa ya Hauwa za ta d'auki lamarin tunda gaskiya yanzu muna zama na fahimtar juna. Ya ce da kansa zai yi mata bayani dalilinsa. Jin haka ya sanya na ce masa ba azanci ba ne yin hakan, kenan ita ba mutum ba ce, idan har yana zargin gidansa da matsala sai ya canza ba zai yiwu a ce saboda na samu ciki har ya samu matsala ya ce daga gidan ne idan ba rikici da neman tashin hankali ba. Ya ce itama tana samun wani cikin sai ta dawo.
Ganin ya'ki fahimtata ya sanya na k'yaleshi domin kuwa ko bayan hali akwai girma da nauyin shekaru da suka fara turawa, yanzu nan sai ya rikice mana.
Aka yi sa'a, Hauwa ba ta yi gardama ba. kwananmu biyar da dawowa abuja suka juya tare dashi. Dama Khalil tuntuni ya bar hannunta da Minal kawai ta tafi tunda tana shan mama.
***
Baba Tabawa ta cigaba da taimaka mini da ayyukan gidan da dawainiyar yara duk da cewa suma rabi da rabi suke yi suna nan suna can gidan Momi sai dare suke dawowa, wataran ma sukan kwana tunda samun cikin da ya zube na cire su daga mama sun fara cin abinci sosai.
Nakan zauna na yi ta mamakin yadda baiwar Allan nan ta had'a kan yara wanda ta haifa da wanda bata haifa ba ta ri'ke duka. Irin rikon da take yi wa Yusi ko ni uwarsa albarka. Ga Kamalu ma ta kar'be shi, daga hannuna. Duk yadda zuciyata take raya mini mummunan nufi akan abinda take yi ba tsakani da Allah ba ne na'ki aminta, domin babu wata alama ta mugunta da ta ta'ba nunawa akan yaran wanda zan gazgata hasashen zuciyata.
Na kan zauna na yi ta tunani akan hakan wataran har na share hawaye idan zuciyata na kissima mini zarginta. To me ta yi mini idan ba alheri ba, muddin na cika 'yar halak kuwa duk irin abinda zuciyata ke raya mini akanta na yi tsalle na dire na ce ba haka ba ne. Amma wani abin mamaki a wasu lukutan sai na dinga jin mugun haushinta da kishi mai tsanani mussaman idan na tuna yadda maigidan yake bada muhimmanci kwarai da gaske akan abinda ya shafeta.
Ni dalilin alherinta a gare ni nakan kawar da kaina na mayar da komai ba komai ba ne, amma Hauwa kuwa ba ta iyawa sun sha yin fad'a akanta don bata iya jurewa ba. Wasu lukutan ni nake shiga tsakani na nuna masa cewa duk sanda zai yabi matarsa ya daina yi a gabanmu zuciya bata da kashi. Amma ya'ki dainawa. Hauwa ba ta fi ni jin takaicin abinda yake yi ba, kawai ina daurewa ne, kuma ba ta fini kishinsa ba. Idan har muka ce zamu hade mata kai mu biyu abin ba zai yi kyau ba, shiyasa dai nake ta jurewa. Amma na soma yarda da maganar da kullum take gaya mini cewa duk abinda take yi akan yaranmu ba tsakani da Allah ba ne. Shi kansa maigidan ta d'aure shi, kuma baya ta'ba zuwa ya gaya mana ta yi masa lefi duk kuwa da cewar suna samun matsala mussaman ta fannin auratayya ni ina ganewa.
***
Dawowar Salim daga karatu abubuwa suka fara lalacewa. Shine yaronta na biyu bayan Nusaiba itace babba sau daya kacal ta ta'ba shigo wa ta gaishemu. Shekara daya da wani abu yanzu bata sake shigowa ba duk kuwa da cewa tana yawan ziyartar uwar akai-akai, sa'i da lokaci idan ta zo su Yusi sukan shigo da yaronta, amma dai ita kam ba ta da fuska da fara'a, irin na Mamanta.
Kwana biyu da dawowar yaron muna zaune ni da Baba Tabawa a falo muna hira, gefe kuma muna d'an ta'ba kallo a tibi da yake Baba Tabawa ma'abociyar son kallo ce dalilin da ya sanya ma kenan wasan kwaikwayon dadin kowa baya shigeta. Yanzu ma shi tashar arewa24 din suke haskawa. Kamalu ya shigo tsaf dashi cikin Pakistani da yake ire iren kayan da uwar rikon nasu ke sayarwa kenan, duk rabi kayan ma da suke sanyawa irinsu ne da jallabiyoyi wattanin bayane ma na ga ta yi musu sabbin dinkunan shaddodi da yadika. Sune sanye a jikinsa kansa da farar hula mai raga. Tun da ya shigo nake nazartarsa. Yana zama a gefena k'amshin turaransa ya kama mini hanci. Na zuba masa ido Ina kallo ban ce komai ba.
Ya dube ni a nutse kafin ya ce." Mama mun yini lafiya?"
Na amsa da "Lafiya lau ina Momin?''
A takaice ya furta." Na bar ta a gida, lafiyarta lau."
Ya dubi Baba Tabawa da take ta tsokanarsa da yake da sheik take kiransa irin yadda taji maigidan na kiransa. Itama momin hakan take ce masa. Ya yi 'yar dariya yana gaisheta ta amsa tana fad'in." Mai zaka ci anan din duk da nasan dai Momi ba za ta barka malami da yunwa ba."
Ya ta'ba cikinsa yana dariya ya ce." Aikuwa kamar kin sani wallahi tare ma muka ci abincin rana a koshe nake. Amma da daddare dai zan ci kwadon zogale."
Ta ce." Idan wannan ne ai mai sau'ki ne, zan yi maka in sha Allahu."
Ya ce." Na gode Baba."
Daga haka sai ya shiru bai sake magana ba, ya fito da sabuwar wayarsa Samsung da momin nasu ta saya masa ya fara dubawa fuskarsa babu walwala.
Shiru falon ya yi. Daga ni sai shi domin Baba Tabawa ta shiga kicin domin dora sanyayar dare. Kamalu tun yana yaro yake da wani irin hali na bakar zuciya da fushi. Wannan dabi'unsa ne raunanarsu kuwa yana da ala'ka da tafiyarsa karatu da kuma shekarun girma. Amma ba haushe ya ce idan ka jima ba ka ga mutum ba, to duk ranar da kuka hadu ka tambayeshi halinsa. Ni na haifi abina nasan halinsa ciki da waje. Yana da mu'amula ga wanda ya so su yi mu'amular. Amma baya jurar wulakanci a ko'ina ne, akan hakan suka dinga fad'a da Turmizi a can baya.
Duk da har yanzu bai fad'a mini abinda yake damunsa ba, ni da kaina na karanci damuwa mai yawa a tattare da shi. Amma ba zan ce masa uffan ba har sai ya magantu tukkuna."
"Mama ina ta kiran Lambar wayar Baba Hamusu bata shiga tun safe fa." Ya fad'i maganar yayin da yake kallona da wani irin yanayi.
Na ce." Wata'kila network ne, amma Hamusu ai baya kashe wayarsa, ko jiya da yamma mun gaisa."
A sanyaye ya ce." Ina tsammanin hakan."
"Neman me kake yi masa ne?'' Na fad'a idona a tsaye a kansa. Bai dube ni ba ya furta." Ina son zuwa kano din ne na kwana biyu a wurinsa" Na ce." To ka gayawa Baban?" Ina nufin maigidan.
Ya gyada kansa a nutse ya ce." E jiya naso na sanar masa kuma sai na manta, kuma mun yi waya fa, amma dai zan gaya masa ina jin tsoron ya ce a a ne Mama."
"Ka dai gaya masa mu ji mai zai ce, itafa Momin taku?'' ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ce." Mun yi maganar dazu har ta fara had'a mini tsaraba."
Shiru na yi kawai ina kallonsa. Har yanzu yanayinsa bai canza ba. Na ce." Ka ga ka gaya mini dalilin da zai sanya ka zuwa kano ina tsammanin ai baku wani jima da zuwa ba ko ba haka ba ne?"
Shiru ya yi bai ce komai ba sai da na sake maimaita maganarta sannan ya ce." Eh kafin tafiyarku legos ke da Baba muka je wata shida kenan yanzu. Mama ba na tsammanin zan cigaba da zama anan, can wurin Baba Hamusu zan koma?"
"Akan wane dalili?'' Na fad'a ina kallonsa. Wannan maganar za ta iya janyo rikici a gidan, ta kuma janyo mana b'acin rai ni dashi, abinda maigidan ya tsana kenan. Ya dai yarda dai ya sanya akai su su yi kwana biyu gidan Gwaggo kwana biyu gidan Hajja a dawo dasu wajan matarsa. Ni kuma ba ni da damar magana ko da ta maslaha ce sai ya juyata ya yi ta neman rigima yana fad'in don ba shi ya haifesu ba zan nuna masa iyaka, zan nuna masa bai iya ba, duk yadda zan yi masa misali ba zai gane ni ba, karshe ma sai ya ce zai kira Baban Saude dole nake jan bakina na yi shiru na kyaleshi.