← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 35

Sashe 4

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*3*
Na bude d'akin na fito ina kuka sosai na ce." Haba baba Sule wannan wace irin magana ce. Idan ba ku taimaka mini wurin kula da yaran nan ba ai ba za ku dinga furta munana kalamai a kan su ba. Wallahi ko kai ka ji abinda suka aikata sai ka yi musu hukuncu, a gaskiya maganganun nan da kake fad'a akan yaronan Kamalu sun yi tsauri da yawa."

Sai ya harzu'ka yana ce wa." Rashin kunya za ki yi mini don ubanki, ni za ki nunawa ban san abinda nake yi ba, an fad'a din Kamalu takad'iri ne ba ya ji, ko za ki musanta mini ne? yaron da kullum cikin d'auko miki magana yake, kaf zuri'armu babu fitinanne a can dangin ubansa ya samo wannan bakin halin. Akan ya je yana d'auko abin mutane ai gwara ya d'auki buhun ya tafi ya yi jari bola, ai sana'a ce, yara nawa ne suke yi, ko za ki gaya mini naki yaron ya fi na kowa, akan hakan ki ka zage karfi akansa kina dukansa, Murja ta yi mini bayanin komai, to wallahi idan ba ki yi wasa ba da kaina zan d'aukesu na mayar da su can wurin kakarsu su je su 'karata."

Cikin kuka mai cin rai na ce." To baba Sule duk mai ya kawo wannan maganganun? Wahalar nan wai wanene yake yi mini ita ne? yaran nan fa kwanciya kawai suke yi su tashi a gidan nan, duk d'awainiyarsu ni ce, na d'auka ai sai ana wahala da mutum tukkuna za a nuna gazawa akansa. A tsaye nake akansu ba zan iya bari su yi wannan sana'ar ba gaskiya magana kenan, Allah ma sai ya tuhume ni, tunda ya taimaka mini da yadda zany..... Ban yi tsammani ba na ji ya tsinka mini mari a fusace yana ce wa." Za ki nuna mini ba ni na haife ki ba kenan, tunda har zan iya fad'in Magana ki mayar mini da raddi, don ubanki ni ba kanin babanki ba ne, Ina ce ni ne na bada auranki ga uban yaran. Wato Ke har abada bakinki ba zai mutu ba ko?"
Ummansu Saminu ta ce." Ni abin ne ya ba ni mamaki Sule ashe duk zaman da muke yi a gidan nan, Amina ta na yi mana kallon sakarkaru wad'anda ba su iya tarbiya ba. Wato yanzu na gane nufin ki kina so ki janye yaronki a ganinki kamar ana so a lalata shi ko?"
Na ce." Ba haka nake nufi ba. Ni dai na ce ban yadda yarona ya yi jari bola ba, karatu nake so ya yi."
Baba Sule ya ce." To ke ma don ubanki gidan za ki bari aure za ki yi, ai ba a ce don ubansu ya mutu ki sarayar da k'uruciyarki ba. Tun wuri ki fito da miji ki yi aure." Ban ce masa komai ba na bar wurin zuciyata a cunkushe da tunani da fargabar mummunan kalubalen da yake fuskantoni.

Wannan ya wuce da kwana biyu wani abu bai sake faruwa ba. Kamalu ya ji fad'a da dukan da na yi masa. Ya rage wasu abubuwan mussaman da ya ga Baba Sule ya mare ni, sai ya dinga kuka a lokacin yana ba ni ha'kuri da al'kawarin ba zai sake ba.

***
Ranar juma'a da wuri suka yi wanka suka shirya tsaf cikin kaya iri d'aya hula da takalmi ma duk iri d'aya. Yusi ya kalle ni a sanyaye ya ce." Mama me yasa ba za ki je ba, don Allah ki shirya mu tafi tare."
Na ce." Yusi ba na jin dadi, zan bari zuwa wani satin idan muna raye sai mu je tare, idan kun je ku gaishe mini da Gwaggwo da kyau." Na kalli Kamalu dake tsaye a jikin bango sai 'bata rai yake yi, na ce." Kai na gane abinda ya sa duk lokacin da za ku je gidan Gwaggwo kake jin haushin saboda tana yi maka fad'a ko?"
Ya yi shiru bai ce mini komai ba. Na girgiza kaina tare da furta. " Ka d'auko ledar can shinkafa ce rabin kwano da taliya guda uku a ciki, ka kai mata, ungo wannan dubu biyu ce sai ka bata. " Ya kar'ba ya sanya a aljihu. Ya kama hanyar fita yana fad'in." Dallah malami taho mu tafi."
Da sauri na ce." Wallahi tallahi ka ci zalinsa a hanya sai ranka ya 'baci, muddin ka ta'ba mini yaro kasan karon mu da kai." Ya zum'buri baki ya fita."
Na kalli Yusi da yake ta walwala duk ranar da za su je wurin kakar tasu yana kasancewa cikin farinciki da nishadi. Sai na ji kwalla ta ciko mini a Ido. Yanayin sanyi da d'abi'a' sak mahaifinsa, mutum ne mai walwala da sanyi hali, baka ta'ba ganin fushinsa. Yusi kamar Yaya Aminu ya yi kaki ya tofar kamarsu d'aya.
Kamalu kuma wasu suna cewa da ni yake kama.
Na d'auki naira hamsin a cikin jakata nasa masa a aljihu ina fad'in." Idan ka ga wani abu a hanya ka saya. Ka yi kyau sosai
d'an saurayina."
Sai ya fashe da dariya yana cewa." Mama ki saya mini gilashi sannan ba ki fesa mini turare ba."
Da sauri na bude 'yar sif dina na d'auko turare ina fad'in." Kash an yi tuya an manta da albasa yarona d'an gayu ne."
Na fesa masa turare ko'ina a jikinsa. Na ce." Ku gaisa mini da ita da kyau."
Yasa takalminsa Yana cewa.'' To zan fad'a mata Mama zan ce sai wani satin za ki zo." Ya kama hanyar fita da sauri.
Na janye idona, a sanyaye na zame na kwanta kawai sai wasu hawaye masu d'umi suka fara sulmiyowa suna bin kumatuna. Ban yi yun'kurin gogewa ba tunda ni kad'ai ce a d'akin. Kukan kuma shi zan yi na samu sassaucin cunkusar da zuciyata ta yi. Abu biyu ne suka tarar mini. Duk lokacin da zan yi al'ada na kan kasance cikin k'unci da 'bacin rai. Sai kuma matsaltsalun da nake fuskanta. Matsalar Kamalu itace ta fi damuna a halin yanzu ba ni da wanda zai taya ni a gidan. Duk wanda zai bud'e baki sai ya ce masa fitinanne. Na san illar baki domin ana cewa har ya fi maita. So nake yi ni da yara mu yi nesa daga gidan da unguwar gabad'aya domin mu canza wata rayuwar, amma yin hakan ma kalubale ne mai zaman kansa.

Na 'kudindine a cikin mayafi na ci kukana na k'oshi. Cikin zuciyata na dinga nanàta addu'ar nan (Rabbi Inni Lima Anzalta Ilayya Min Kairin Fa'kir) ina ta kiran Innalillahi wa'ina ilaihi raji'un! Har Allah ya sassauta mini k'uncin da nake ji a raina. Na tashi na juye ruwan wankan dana d'ora.

A gurguje na yi wanka na shirya jikina tsaf. Lokacin na dan ji sassauci ciwon marar da ya matsanta mini kasancewar abin ya fara zuba. Na shirya na fito duk suna cikin d'aki. Na kulle 'kofata. Sannan na tsaya kowacce daga bakin kofarta na yi mata sallama.
Har na kai bakin kofar fita Ummansu Hadiza ta kira ni.
Na shiga na sameta tana d'aura dakakken yajin da take sayarwa na daddawa dana barkono. Ta ce." Ina ta zuci-zucin yi miki magana gashi kuma kin shirya za ki fita, Ina za ki je ne? Na ga an yi hutun makaranta ko kayan d'inki za ki sayo?"
Na ce." A 'a ba kasuwa zan je ba, gidan Sahura zan je."
Sai ta ce." Ayyo, to dama babanku ne ya ce na fad'a mini za ki yi ba'ko yau, Alhaji Mutari ne ya ce yana sonki da aure."

Cikin fad'uwar gaba da tsananin tashin hankali na ce." Wanene kuma Alhaji Mutari Umma sai kuma akace masa ni aure zan yi, ko ni kad'ai ce bazawara?"
Ta zuba mini ido na minti biyu kafin ta ce." Matsalarki kenan Amina rashin tauna magana, ni sa'arki ce da za ki ba ni amsa cikin gatsali."
Na sassauta fuskata na ce." Umma zancen ne na ji shi kamar saukar aradu wallahi, ki yi hakuri don Allah."
Ta ce." Alhaji Mutari Ubangidan Babanki Sule shine ya nuna masa hotonki, shi kuma ya yi Allaragaf dake."
Na ce." To ba za ta yiwu ba, Umma ba aure zan yi ba, tarbiyar yarana ce a gabana a yanzu, kuma ko zan yi aure ni zan duba mijin da zan aura wanda ya cancanta babu ruwana da dukiya nagarta nake nema kamar dai Yaya Aminu, in sha Allahu zan samu."

Ta ce." To, ni dai na isar da sa'kona Amina, amma ki yi nazari sosai akan maganar kafin ki yanke hukunci."
Na yun'kura na tashi ina cewa." To zan yi, in sha Allahu Umma sai na dawo."
Ta ce." Ki gaishe da Sahura da yaranta." Na kama hanya na fita ba tare da na sake cewa komai ba tsabar tashin hankalin da nake ciki.

Cikin zullumi da tunani mai zurfi na isa gidan Sahura. Na same ta tana shirin fita. Ganina a hargitse ya d'aga mata hankali.
Na nemi wuri na zauna kawai sai na rushe da kuka!
Ta kid'ime ainun! Ta rirri'ke ni tana fad'in." Sis menene don girman Allah ki yi shiru kada ki jazawa kanki lalura, ba fa ke kad'ai ba ce, kuna nan da yawa iyayen marayu, kuma ki godewa Allah da ya ba ki sana'ar da za ki yi d'awainiya da yaranki, wallahi akwai wad'anda aka mutu aka bar musu marayun ba su da yadda za su yi, wasu ma sai sun yi bara da ro'ko suke samun abinda za su ci, ni kaina da nake da mijin kullum cikin fafutuka nake, kin san komai ba sai na fad'a miki ba, Abbansu Yasir bashi da tartibiyar sana'a, kasuwa yake shiga Yana tare mutane idan an yi katari sai ya kai su shagon da suke nema, da haka fa yake samun abinda zai kawo gida, ki yi hakuri ki godewa Allah, ki kuma cigaba da yi wa Mijinki addu'a, Allah Ya gafarta masa."
Chapter 4 · 0% Book details