← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 35

Sashe 11

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"A 'kafa ku ka je tsinto lemon har na'ibawa kuma ku ka dawo a kafa?"
Ya daga mini kai alamun 'E' hawaye na zuba a kumatunsa. Na girgiza kaina jiki a mace na ce." To koma ka kwanta."
Ya kwanta ya takure wuri d'aya Yana goge hawayen da suke karakaina a fuskarsa
A hankali na fita daga cikin net din na jingina jikin bango(garu) ina nazarin abinda muka tattauna.
Ba a shaidar d'an yau, Amma duk da haka zuciyata tana tabbatar mini da cewa Saminu Yana taka muhimiyar rawa wurin gur'bata mini tarbiyar yaro. Ya girmeshi ya fi shi wayo. Kuma muddin za su kwana a gida su wayi rabuwarsu za ta yi wahala. Duk lokacin da zan zauna da Kamalu na yi masa fada da nasiha yakan nuna nadamarsa ya yi ta kuka Yana ba ni ha'kuri akan ba zai sake ba. Amma ba a yin sati zai koma ya cigaba da d'auko mini magana. Babu yadda za a yi na fito na fadi wannan maganar a cikin gidan a yarda dalili kowa yana ganin fitinar Kamalu ta fi tsananta bayan ba haka ba ne. Ita Ummansu Saminu ta san yaronta ba ya ji, amma kullum cikin kare shi take ko abu suka aikata a tsakaninsu za ta cire shi tace ai lokacin da abin ya faru baya nan. Babban tashin hankali ne zai afku idan na fito na fadi cewa Saminu ne ya tura Kamalu yin 'kwace.
Hawaye masu masifar zafi suka fara gararanba a kumatuna. Dole dai abinda ba na so shi zai faru. AURE Ina ganin shine zai nesanta ni da zaman gidanmu ko yarana za su samu ingantaciyar tarbiya. Ba na jin son mutumin a cikin zuciyata ko kad'an. A duniyar nan ma ba na jin akwai wani d'a namiji da zan so fiye da Yaya Aminu, zan aure shi ne domin katange kaina daga zargi da kuma tseratar da yarana daga rushewar tarbiya. Ina hasashen samun nutsuwa daga gare shi dalilin yadda ya nuna damuwa da kulawa da ni da yarana.
Da kyar na runtsa saboda tunanin rayuwar da take fuskantoni. Ina idar da sallah na hau kan keke domin rage din'kunan da suke hannuna.
Sai da na hada set uku tukkuna na sauka daga keken domin karyawa. Lokacin yaran sun tafi makaranta allo.
Na karya a gurguje na yi wanka na nufi makarantar tasu. Bayan mun gaisa da malamin na fad'a masa abinda yake tafe da ni. Ina so a yi mini saukar al'kur'ani domin warwarewar matsalata.
Dubu goma ya kar'ba a hannuna a matsayin sadaka za a dafa shinkafa da wake ga Wand'anda suka yi karatun.
Cike da kwarin guiwa na dawo gida, a raina ina fad'in babu abinda ya gagari Allah komai da lokacinsa.
Sai bayan na koma gida tukkuna na kunna wayata.
Minti biyar a tsakani kira ya shigo. Sabuwar number ce. Ban yi mamaki ba tunda dama ya ce zai kira ni. Na daga a nutse da sallama ya amsa da sauri yana cewa." Ba kya kunna wayarki da wuri ne, ko ba ki da chaji ne?"
Na ce." Ina da caji ba na kunnawa da wuri ne saboda wasu dalilai."
Ya sauke ajiyar zuciya tare da furta." A a ranki ya dade ki dinga kunnawa da wuri domin kada wasu alheran su wuce ki, ba ki ji yadda na d'okantu da jin muryarki ba."
Murmushi na yi na ce." Alhaji kenan, ina kwana ya iyali?"
"Lafiya lau, iyali kuma duk suna nan lafiya, suna gaisheki da kyau, ina fatan yarana na wurinki suna cikin koshin lafiya?"
Na ce." Suna lafiya, sun tafi makaranta."
"To Allah Ya yi musu albarka, yanzu a Ina maganarmu ta kwana, ni dai da gaske nake, Amina ni ba yaro ba ne, ina da mata biyu Uwargidana tana da Yara biyar mata hud'u namiji daya. Ta biyun kuma tana da Yara hud'u duk maza, ke idan kin zo nawa za ki yi mini, domin har ga Allah ina so na hada garke da yawa, tunda Allah ya huwace mini."
Jin maganarsa ta karshe sai jikina ya yi sanyi, domin har ga Allah ba ni da burin daga mun yi aure na haihu sai zama ya yi zama tukkuna na lura da kamun ludayinsa da iyalinsa. Shi kuma har ya fara maganar haihuwa.
Ya yi gyaran murya yana cewa." Na ji kin yi shiru Amina, kada ki ce mini ba ki amince ba "
Ajiyar zuciya na sauke na ce." Ba wai ban amince ba ne, ka d'an sake ba ni lokaci Alhaji zan je Maiduguri a can dangin Mamana suke zan yi shawara da Yayata, in sha Allahu zan kira ka na fad'a maka abinda na yanke."
A sanyaye ya ce." Shikkenan, yaushe za ki tafi Maidugurin ne, sai na zo na kai ki."
Dariya na yi na ce." Ka yi hakuri tare da Babanmu zamu tafi jibi in sha Allah."
Ya nisa kafin ya ce." Da kin bari mu tafi tare sai dangi su gan ni, mu gaisa da juna."
"Ka yi hakuri dai Alhaji a hankali za ku gaisa."
Ya numfasa tare da cewa." To babu damuwa, amma zan iya bada kud'in mota ko?"
Na ce." Ai ina da kudin mota ranka ya dad'e."

"Ki ajiye na ki za su yi miki amfani ta wani gefan, ki turo mini acct d'inki zan sa miki kudin mota kin ji ko?" Cike da bada umarni ya kai karshen maganar. Na ce." To na gode sosai, Allah Ya kara budi, wannan lambar tawa Opey bank dina ne, idan ka cire ziron farko."
Ya ce." To za ki ji ni, in sha Allahu rabbi."
Yana kashe wayar ni ma na kashe na ajiye a hankali na lumshe idona ina ta so na tursasa zuciyata ta fara ganin haskensa......✍️
1k on talgram via 0542382124...Binta Umar gtbank..
*07084653262*
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/17, 9:51 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

*TALLAH!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
Chapter 11 · 0% Book details