Sashe 2
Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Yanzu ina Kamalun yake?"
"Ya d'auki kudi a jakarki ya tafi sayo kunu da awara."
Na kalli agogon da yake bangon d'akin, takwas saura mini goma. Na ce." To tunda an yi hutun boko sai ku yi shirin allo idan kun karya ba zan iya cecekuce da rabon fad'a ba."
Ya ce." To Mama." Kamalu ya shigo da jug din kunu da awara a bakar leda Yana cewa." Mama na d'auki dari biyar a jakarki na sayo awara ta d'ari uku kunun dari biyu, yanzu darin sukari za ki bayar."
Na ce." Kamalu kai kullum burinka ka janyo mini magana ko? kullum sai na zaunar da kai na yi maka fad'a, amma magana tana shiga ta kunnan dama ta fita ta kunnan hagu ko? Ba za ka ri'ke maraicinka ba Kamalu abinda kake yi fa shi d'an'uwanka zai kwaikwaya, ba za ka barni na ji da abu daya ba sai ka jefa mini damuwa da zullumi a cikin raina ko Kamalu."
Ya zauna jiki a sanyaye ya ce." Mama don Allah ki yi hakuri kin ji, ba zan kara ba."
Na ce." Haka kullum kake fad'i Kamalu amma kana fita zaka sanya kafa ka shure maganata, me yasa kake dukan yaran mutane kana d'auko mini magana, bakin jama'a a kanka, kowa Kamalu kowa Kamalu, so kake yi baki ya kamaka ko?"
"Mama ki yi hakuri ba zan sake ba."
Girgiza kaina kawai na yi cikin zuciyata nake masa addu'ar shirya. Na ce." Ka je ka zuba mini ruwa a buta zan wanke bakina."
Da sauri ya tashi ya d'auki buta ya fita. Sai gashi ya dawo yana cewa."Mama sun d'auke gugansu. Na tambayi Ummansu Saminu ta ba mu aro wai ba zata bayar ba tunda kina sana'a ki saya mana."
Kaina ne ya d'aure da jin maganar. Na ce." Umman Saminu ce din ta fadi haka?"
Ya ce." E, wallahi." Ban yarda ba sai na tashi na fita da kaina na tsaya a bakin kofar dakinta na ce.''Umma ina kwana?" Tana rabawa Yara karin kummalo ta amsa a dakile.
Na ce." Guga za ki d'an ban aro zan ja ruwa."
"Amina ki sayi guganki don Allah, kullum sai kin ara, bayan Allah ya hore miki, kada ki ce za ki yi gadara domin ba babanku ne ya saya ba, kowa da kud'inta ta saya. Yawan jan ruwan da Kamalu yake yi miki, duk gugana ya fatattake."
Kafin na ce wani abu. Ummansu Hadiza ta le'ko tana cewa." Kin ga zo ki d'auki nawa ki yi abinda za ki yi gugan me da har za ki tsaya ana yi miki gori akansa."
Hakan sai ya fusata Ummansu Saminu. Kamar dama kiris take jira, ta fito tsakar gidan tana cewa." Aikin banza da wofi. Murja sai yanzu ne za ki nuna mata k'auna waye bai san irin jifan da ki ke yi mata ba. Ba zan bayar da gugan ba, tunda ba ubanta ne ya saya ba.''
Ni dai ban ce komai ba na je na d'auki gugan na wuce bakin rijiya ina jin su suna ta masayar yawu. Na kud'ire a raina idan na fita kasuwa sayo kayan d'inki zan tsaya na siyo gugana da duk abinda na san za a yi mini gori akansa.
Babanmu ya fito daga d'akinsa da shirin fita hannunsa da hulunun mutane da yawa. Ya tsaya yana tambayar ba'asin hayaniyar da suke yi. Babu wadda ta ba shi amsa a cikinsu. Kamalu ya ce." Saboda gugan jan ruwa ne, Ummansu Saminu ta c... Na daka masa tsawa sai ya yi shiru yana kallona. Na ce." Wuce ka je ka d'auko mini d'an bokitin nan.''
Ya bar wurin da sauri. Na dan risina a lokacin da ya kusa karasowa bakin rijiyar da niyyar fita. Na ce." Baba ina kwana"
Ya amsa ya dan tsaya yana kallona kafin ya ce." Ko zan sami dari biyar a wurinki Amina yau haka na wayi gari babu ko kwabo, wad'annan matan kuma suna nema su tona mini asiri da sanyi safiyar nan."
Na ce." Ina da ita Baba." Sai ya ce." To ki aiko Kamalu ya kawo mini, zan aike shi ya sayo mini shayi."
Na ce." Baba don Allah ka rage cin borodin nan kwanan nan fa ka tashi daga lalura basir ne da kai mai muni."
Ya ce." Ai kad'an nake ci, kuma shayin tsura nake sha ba madara.
Na ce." Dukda haka dai Baba, hanyar lafiya a bita da shekara."
"Amina abinda ya tashi basir din nan fa zama ne, da kuma cin rogo da gyad'a dana dimanta amma zan kiyaye dai."
Ya kama hanya ya fita yana gyara tarin hulun nan da suke hannunsa. Sai da na cika butocina da babban bokitina mai murfi sannan na mi'ka mata guganta.
Muna karyawa na ce." Wallahi Kamalu duk lokacin da ake hatsaniya a gidan nan na ji ka kara sanya bakinka sai na sanya an zane mini kai, kaine mai bakin magana ko?"
Shiru ya yi. Na k'araci yi masa fada bai ce uffan ba.
Na kunna kurfoti na d'ora musu ruwan wanka suka yi suka tafi makaranta.
Na had'a wankinmu da ya taru, na sanya sabulu a ciki na daure. Sannan na juye ruwan dana dora na je na yi wanka a gurguje na shirya da zan fita na yi musu sallama. Kafin na wuce kasuwar sai da na tsaya a shagon Babanmu na bashi dubu daya kamar yadda na yi masa alkawari kafin ya fita.
Da ya tambayeni Ina zan je na ce." Kasuwa zan je na sayo kayan d'inki.
To da yake motar sabon gari bata wahala ina fita titi na samu. Sai dai gosolw da ya ri'ke mu a hanya daidai sabon titi gidan 'kankara.
Na rasa cunkuson menene direban da yake jan mu ya ce.'' Rasuwa akayi nan cikin Sani mainagge shine Alhaji Tajo ya zo gaisuwa wad'annan zungura-zunguran motacinsa ne da jama'arsa."
Na ce.'' Na d'auka ai dan kasuwa ne ba 'dan siyasa ba ne."
Ya ce." E, d'an kasuwa ne sosai, ai ba sai lallai d'an siyasa za a yi wa wannan cunkoson ba. Shi ma babban mutum ne a garin nan."
Na girgiza kaina. Ban yi mamaki ba tunda sananne ne. Akwai d'aruruwan mutane dake 'kar'kashinsa. Bayan haka ma har kalandarsa na ta'ba kafewa a d'akina a lokacin da Abbansu Yusi ya yi aiki a kamfaninsa na sarrafa robobi. Kafin ya sanya soke sunansa daga jerin ma'aikatansa...
✍️
*Garkuwar mata Bintuumarabbale*
*08089965176*
*07084653262*
[11/11, 7:38 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*Marubuciyar*
*Yar bangar siyasa*
*Ba'aboren namiji*
*Madadi*
*Ga irinta nan*
*Goje*
*Babban yaro*
*Sadauki Omar*
*Nida Yaya sadam*
*Da sauransu..!*
*@Arewa Books*
*Bintuumarabbale*
*2*
Matar da take zaune a kusa da ni ta ce." Kai gaskiya ban yarda ba domin kuwa wannan bawan Allan ya ma fi wani dan siyasar. Yadda yake taimakon jama'a shi zai nuna maka cewa adali ne yana kuma da tausayi, tabbas da zai fito takara ina ganin zai iya lashewa muddin jama'a sun san ciwon kan su to shi zasu dangwalwa kuri'arsu. Ni dai ko yanzu ya fito takara shi zan za'ba."
Cike da karsashinta tare da kwarin guiwa ta dire maganarta. Yadda ta ha'kik'ance take bayar da sheda akansa shi yake nuni da cewa lallai akwai abinda ya ta'ba yi mata a rayuwa ko wani da ya danganceta.
Tunanina ya katse a lokacin da na ji direban namu shi ma yana ce wa." Gaskiya ni ma 'kuri'ata tasa ce, domin yayyuna biyu a kafamninsa suke aiki, sun yi gida, sun yi aure kuma suna ri'ke da iyalinsa. Ko yau zai sallameka daga aiki zai baka kudin da za su isheka jari domin yin wata sana'ar, ai mutumin kirki ne mai dattako wallahi."
Na ce" Ban tari numfashinka ba, irin wad'annan mutanan fa suna zama da mutum ne idan sun ga zasu amfanu. Babu yadda za a yi ku ce lallai ya cika cif kowane d'an adam za ku same shi da da aikata wasu kusakuran. Ni dai wallahi duk inda za a je ba zan bayar da sheda a kansa ba. Domin ni ma mijina ya yi aiki a kamfaninsa na robobi kafin rasuwarsa, kuma daidai gwargwado ya yi masa bauta. Amma tashi d'aya ya sallame shi bai duba uzuri da lalurarsa ba. Kuma bai bashi komai ba."
Matar da take kusa da ni ta kalleni tana fad'in." Anya kuwa, gaskiya ban yarda da maganarki ba, mutumin nan adali ne, sai dai idan mak'arkashiya aka yi wa mijinki a kamfanin, amma zahiri daidai gwargwado yana yi wa ma'aikatasa hidima."
Na ce." To ko annabawan Allah suna kuskure ballanatana mutum, ba wai na ce dole ku yarda ba ne, ni ma kuma babu lallai na aminta da hasashenku akansa ba domin lokacin da aka bawa maigidana takardar sallama mun shiga tashin hankali sosai, shiyasa duk lokacin da na ji sunansa sai gabana ya yanke ya fad'i wallahi."
Direban ya dinga dariya yana ce wa." Lallai hajiya kenan ko da zai fito takara ba za ki zabe shi ba?"
Kai tsaye na ce." Babu lallai gaskiya."