← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 35

Sashe 31

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Na san ya ji labarin abinda ya faru, amma bai tare ni da maganar ba, sai ya ja bakinsa ya yi shiru, hakan ya k'ara
sanya ni karatun ta nutsu, tunda bashi ya haife shi ba, ai ba zai damu da abinda akayi masa ba, wata'kila shima ya yarda da zargin da akayi masa tunda shi Kamalu a kuyarsa ta riga ta yi kuka.
Uku ga sallah 'yan gidanmu suka zo kaf dinsu har da yaran Baba Sule. Su Hadiza yanzu an yi hankali an daina giggiwa yadda na lura ma kamar shakka take yi ganin yadda Allah Ya rufa mini asiri. Zuwansu bai daga mini hankali ba tunda muna da abinci wadatacce kajin sallar da muka soya suna da yawa ko rabi ban ci a kasona ba. Ina gama yi musu abinci na d'auko musu naman gabad'aya na ce su juye akan abincin.
Ruwa muke dashi babu lemo nasa aka sayo musu katon biyu. Suka yi facakarsu yadda ransu yake so ban hana su ba. Da za su tafi kowacce na bita da dubu d'aya sannan na bawa Hadiza atamfa turmi biyu iri d'aya dukda tace daga nan gidanta zata wuce na ce don Allah ta koma gidanmu ta kaiwa Ummansu da anti Sakina Ummansu Saminu, na so na dinka musu aiki ya yi mini yawa, na dora musu dubu bibbiyu akai kudin dinki.
Alhamdulillahi shekarar ta zo mini da bud'i da nasara mai yawa. Domin ayyukan da na yi sun tara mini kudi masu nauyin gaske Ya Falmata tana da zuciya mai kyau bata ha'intata ko kad'an, duk wani matakin nasarar da zan taka a rayuwa zata kasance mace ta farko sai ko Sahura data ba ni gudumuwa daban daban. A maza Kam Yaya Aminu shine madubi na.
Sati daya da sallah na shirya fita zuwa gidanmu da gidan Gwaggwo domin tunda na auri Alhaji Muntari bai fi sau uku kacal na shiga cikin garin ba.
Gwaggo ta ji dadin ganina da yaran cikin koshin lafiya. Bakinta ya gaza rufuwa ta dinga murna. Ni ma kuma ban je hannu rabbana ba. Atamfa mai kyau da tsada na saya na dinka mata irin na manya, na hada mata da takalmi da mayafi, sannan na dora mata dubu biyar a kai. Ta dinga godiya har da hawayenta. Hakan ya k'ara karyar mini da guiwa ni ma hawayen suka ciko idona.
Gidanmu kuwa da na je nan naga tsantsar kulawa ban yi mamaki ba saboda na riga na san a yanzu babu abinda ya fi saurin kankaro da mutunci irin kud'i. To Allah Ya hore mini shi a yanzu shiyasa kowa ke ganin girma na. Babanmu ma sam baya ganin aibuna duk sanda za mu had'u ya dinga fad'in auran naki ai Yayi albarka Amina. Ai na gaya miki mutumin kirki ne gashi bai yi miki keta ba ya rike miki yara sannan ya barki kina sana'a. Lallai Ubangiji Allah Ya yi mini sakayya.
***
Na cigaba da rayuwa a gidan Alhaji Muntari da dadi babu dadi ana ta turzawa. Na dai ki yadda na samu ciki domin dabara nake yi a duk lokacin da ya yi auratayya da ni. Muna gamawa zan yi sauri na kada gishiri da ruwan dumi nasha. Kafin gari ya waye duk abinda ya zuba mini ya tsinke ya fito.
Shi dai adduarsa Allah Ya tsananta rabo a tsakaninmu. Ni kuma ina jin na gama haihuwa da kowane namaji wanda Allah Ya ba ni sun isa.

Yara suka koma makaranta. Ayyuka suka yi mini yawa. Sai na fara shawarwari mai zai hana na nemi shago a bakin titi na sanya Hamusu ya binciko mini kwararrun teloli maza na zuba kekuna kawai mu fara gudanar da aikin tare don gaskiya abin ya yi yawa sosai gashi koyaushe suna nake karayi a fad'in najeriya da kewayenta.
Ban yi zaton maigidan zai amince mini da sauri ba, Ina gaya masa ya ce." Ai babu komai ke ma tunaninki ya dawo kan auranki, na yarje miki amma ki kula sosai da yaran da za ki zuba, a samu masu Amana wad'anda suka gwanance da aikin." Na ce." In sha Allahu za a samu." Godiya na yi masa sosai domin da ba na samun goyon bayansa da ban kai matakin da nake a yanzu ba. Amma har yanzu zuciyata ta kasa aminta da haihuwa dashi.

Ina ta shirye-shiryen fadada harkokina, don har mun gama magana da Hamusu ya ce wannan duk ba zai zama matsala ba, zai tsaya mini akan komai. Wani mummunan lamari ya rikito mini wanda lokaci guda hargitsin ya gigita mini rayuwa. Na shiga halin d'imuwa da tashin hankali mai tsananin gaske......✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
[11/28, 9:51 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*TALLAH!*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi
Chapter 31 · 0% Book details