← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 35

Sashe 20

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Muka dinga fa'di tashi da zurga-zurga makaranta tare da Sahura, kuma kamar yadda Yayansu ya yi alkawari bai bambamta ni da ita ba, duk abin buk'ata da ya danganci karatunmu tare zai saya mana Wanda ita a d'akinta ta kammala. Ni kuma har lokacin ba ni da wani tsayayye. Ina dai ta addu'a da neman yadda asirina zai rufu domin a lokacin na mayar da hankali sosai wurin neman aiki, da kuma fitar da style na din'kunan mata. Sosai nake neman kud'i a gidan. Hakan ya janyo mini kwarjini da mutunci a wurin matan Babanmu Mussaman Ummansu Hadiza da ta watsar da makamanta a kaina ta fara jana a jiki tana nuna mini k'auna. Hadiza da a can take ganin tafi karfin ma ta kula ni idan ta zo gidan sai ya zamana tana shakkata don ganin irin sutturar da nake sanyawa tana nema tafi karfinta ita da take da miji. Babanmu kuwa yadda nake taimaka masa shiyasa koyaushe cikin sanya mini albarka yake. Anti Sakina itace muke sama-sama Hakan ya samo asali ne dalilin 'kin auran 'kaninta da na yi saboda binciken da na yi akansa aka tabbatar mini da cewa ba shi da wata cikakkiyar sana'a sai maning, sannan uwa uba yana shaye-shaye, kullum yana shagonsa a kwance da waya a hannu wasu ma suna zargin yana harkar yahoo (damfara) ita kuma ta kawo mini shine a ganinta ta rufa mini asiri ganin yadda duk na tsofe a gida, an aurar da 'yan uwana, 'yan matan unguwarmu a yanzu duk babu sa'ata. Shine ta yi mini wannan gwanintar. Tabbarar mini da munanan halayensa ya sanya na ce ban amince ba. Babanmu ya goya mini baya, shine dalilin da ya sanya take jin haushina har tana fad'in dama can na yi masa girma tunda na girmeshi kawai dai ta tausaya mini ne shiyasa tace masa ya aureni . Maganarta ta ba ni dariya sosai a lokacin sai na shareta ban tanka mata ba, muka cigaba da zama a haka ina ko'karin kaucewa duk abinda zai janyo mini samun matsala da su a gidan, amma ba na yarda su zo mini da son zuciyarsu....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/22, 10:12 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Na yi nisa a arewa idan ba kya son jira ki yi maza ki garzaya can Kisha karatu!*
*Domin biyan kudin karatu a talgram kuwa 1k ne ga hanyar biya 0542382124...Binta Umar gtbank mutanan nijar dala dari ne katin airtel sai ku kankare hoton a turo mini sheda ta wannan lambobin*
*Whasap kawai*
*08089965176*
*07084653262*
Astagfirullah jiya na yi mistake typing error inda zan rubuta Alhaji Halilu wato mijin da Hadiza ta aura sai na rubutu akasin hakan. Wad'anda suke bibiyar littafin nasan za su gani bisa kuskure ne, ina neman afuwa.
*Free peges*
*13*
Watarana katsam Yaya Aminu ya zo yana gaya mini ya sama mini offer ta aikin koyarwa. Saboda murna kamar na rungumeshi na rasa ina zan tsoma kaina. Na dinga yi masa godiya wanda har na gaza ha'kuri na tambaye shi yadda aka yi ya sama mini aikin da har na fitar da raina da samuwarsa. Nan yake gaya mini wani abokinsa ne da suka yi harkar siyasa. To shine mutumin da suka wahaltawa da ya samu kujera ya raba musu offer biyar domin su taimaki makusantansu. Cikin ikon Allah ya kaiwa kanwarsa daya ya rabar da sauran. Tunda lokacin shi yana aiki a karkashin kamfanin Alhaji Tajo. 'Kanwar tashi sai ta rasu, shine ya nema mini alfarmar maye gurbinta da ni. To komai dai rabo ne, kuma na tabbata addu'ar da nake yi ita Allah Ya kar'ba ya kawo mini aiki cikin sau'ki da rangwame. A daidai lokacin ne itama Sahura ta samu aikin rabon magani 'kauyika amma mijinta Idiris ana ta turzawwa dashi ya 'ki amincewa bayan kuma ba haka akayi dashi ba kafin auran.
Cikin hukuncin Allah na fara zuwa aiki da zuciya daya. Sai dai yadda 'yan gidanmu suke ko'karin juya mini manufa shi ya fi damuna. Mutanan unguwarmu ma suna ganin kamar yanzu na yi karfin da babu wanda ya isa ya gaya mini na ji, tunda babu uwata a gidan matan Babana ban d'auke su a bakin komai ba. Wasu ma suna fad'in duk an yi wa 'yan'uwana aure ni kuma na tsaya za'be sai mai kudi. Kowa dai da irin kallon da yake yi mini akwai masu cewa ma zaman kaina nake yi, na fi karfin Babanmu tunda ina bashi kudi na toshe masa baki. Wannan maganar kuma daga bakin Ummansu Hadiza ta fita, domin itace mai yawan fad'in haka har jama'ar unguwa suka d'auka.

To da yake komai ya yi farko yana da k'arshe. Idan kaddara ta gifta babu yadda bawa zai yi dole ya kar'beta hannu biyu, ya kuma roki Allah Ya sa alheri ne faruwar Hakan.
Budurwar da Yaya Aminu yake nema da aure har an kai kudi da sa ranar d'aurin aure rana tsaka ta bijire tace ta fasa. Kuma kada ku d'auka lafiyayayyace kamar kowa. Bai yi gigin haka ba saboda shima ya san ga yadda Allah ya yi shi, sai ya nemi daidai dashi don har ya fi ta lafiya ma tunda shi yana yawo da 'kafafunsa, sa'banin ita da kafafun suke a nanna'de a keke take yawo. Sai dai kyakykyawar gaske ce fara tas da ita. A haka suka kulla soyayya har suka kai matakin aure rana tsaka wani gurgu d'an wani attajiri ya ganta a wani taro da suka yi irin nasu. Ya ce Yana sonta. Ganin daga gidan da ya fito ya sanya iyayenta da ita kanta suka dawowa da Yaya Aminu kudinsa wai ya nemi wata.
A lokacin ya shiga rud'u sosài, domin ya d'okanta da auran da ya shafe shekaru sama da arba'in a kasa bai yi ba, har furfura ta fara feso masa, kuma a hakan ma bashi gwaggo ta fara Haifa ba, ta yi haife-haife kafin zuwansa yaran suna rasuwa. Sai da shekarun girma suka cimmata ta haife shi, Allah Ya raya shi tare da d'an'uwansa Hamusu da tazarar da take tsakaninsu take da yawa. Wannan dalilin ya sanya hankalinsa ya tashi. Ita kanta Gwaggo ta shiga damuwa. A lokacin ne ya zo har kofar gidanmu ya aiko nazo.
Na fita na same shi muka gaisa ba yadda yake duk ya yi rama. Ya fara tambayata ko Ina da tsayayyen wanda zan aura. Na ce masa babu. Sai ya bijiro mini da bukatarsa akan na share masa hawaye, idan kuma da takura ko ba na sonsa kada na cutar da kaina na gaya masa sai ya ha'kura.
Na ce wallahi ko ka fi haka nakasa da talauci zan aureka Yaya Aminu, kuma da zuciya daya, na amince Ubangiji Allah Ya tabbatar mana da alheri.

Ba'a ja dogon lokaci ba iyaye suka shiga lamarin. Ummansu Hadiza ta dinga fad'in dama tuntuni na fahimci soyayya kuke yi, tun kina yarinya. To tunda shi ki ka gani, ai ba mu da abinda za mu ce akan haka. Anti Sakina kuwa dariya take yi tana fad'in. Ai ta gwammace ta auri nakasashe an kawo mata mai lafiya da aikin yi ta ce ba ta so. To za mu ga zuwan da dawowar ai. Duk maganganunsu akan lamarin bai dame ni ba. Kawai dai ni na tsananta da addu'a Allah Ya sanya mana alheri da albarka a cikin auranmu.
Danganin Mamanmu ba su k'yamaci lamarin ba sanin wacece Gwaggo ya sanya suka nuna faricikinsu da hakan. Kuma suka yi mini shatara ta arziki a lokacin auran duk abinda ake Yayi da buk'ata sai da suka saya mini aka shirya mini dakunana biyu wanda Yaya Aminu ya kama hayar gidan a can sharad'a wajejen kamfanin da yake aiki ya yi hakan ne domin ya samu sau'kin zuwa neman abincinsa.
Zaman lafiya muka gudanar a zaman auranmu, tunda aka yi babu wanda ya ta'ba jin kanmu, Muna ta rufawa juna asiri, duk wanda zai zo gidana sai ya yi sha'awa domin ba na yin girki lami sai da nama ko kifi, kuma idan mutan zai tafi na bashi kudin mota. Na ri'ke aikina da sana'ata hannu bibbiyu, muka dinga cud'a rayuwar har na yi haihuwar fari, wata matsala ba ta faru. Irin sa'banin nan na zama ba mu taba samu ba, tunda kowa yana ko'karin kiyayewa da kyautata mu'amula da abokin zamansa.

WANNAN SHINE ABINDA YA FARU GA RAYUWATA TA BAYA.
Chapter 20 · 0% Book details