Sashe 30
Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta fara gaya masa abinda ya kawota. Ya dube ni tare da cewa." Amina ba karya Jamila ta yi ba doyar nan bata suyuwa karni take yi yau ni kaina ban iya ci ba wallahi, bayan kunyar da ki ka ba ni a cikin abokai, ashe dama ba ke ki ke yin aikin nan ba?"
Shiru na yi masa ban tanka ba. Ya dubeta tare da cewa" Tafi wurinki zan yi maganin abin." Ta juya ta tafi ba ta sake cewa komai ba.
Yana shigowa falon na sake daure fuskata. Yaran suka tashi suka bar wurin.
Bai ce mini komai ba, ya wuce cikin kuryar d'aki. Minti biyu na ji yana fad'in." Ina ki ka ajiye mini dabinon nan dana shigo dashi kwanaki?"
A cunkushe na ce." Ka duba cikin doruwa."
Gabana ya buga da karfin gaske tuna abinda na ajiye a dorowar. Da sauri na tashi na shiga d'akin na same shi a tsaye hannunsa rike da kwalin maganin, daya hannun kuma robobin dabinon ne.
Jikina ya yi mugun sanyi. Kai a kasa na nufe shi.
Ya dubeni ya jijjiga kansa. Cikin mamaki da al'ajabi ya ce." Maganin hana d'aukar ciki a gidana Amina, Ashe ha'intata ki ke yi dama, ina ta wahalar banza wuri zuba kwaya-kwayena ke kuma ki sha magani su tsinke su bi rariya, dama da wannan nufin ki ka shigo mini Amina? me ya sa ki ka yarda da haihuwa da tsohon mijinki wanda bashi da ko kwabo sai ni da Allah Ya rufawa asiri ki ke gudun had'a zuri'a da ni bayan tun kafin mu yi aure na gaya miki ni mutum ne mai burin tara zuri'a."
Cikin sanyin jiki na ce." Wallahi ba haka ba ne, na yi hakan ne domin ni da kai mu huta, mu mori amarcinmu, amma mai zai sanya na guji haihuwa da kai bayan kana da nasaba, kuma Allah Ya rufa maka asiri, idan na yi haka ai na yi butulci ga Allah, don Allah ka yi hakuri."
Babu sassauci a tare dashi Ya ce." Watanki takawas a gidan nan Amina don Allah ki gaya mini amarcin da ki ka bari na ci dake, tun baki fi sati biyu ba a gidan nan ki ka daina ba ni kulawa, bayan kin san ni din namaji ne mai buk'ata, kin fi bawa neman kudinki muhimmanci, a gaskiya wannan lamarin ba zai tsaya iyakacin ni dake ba, dole waliyinki Sule ya ji abinda yake faruwa domin akwai cutarwa a ciki."
Jin haka ya sa na fashe da kuka ina fad'in." Don Allah kada ka fitar da maganar nan wallahi zan gyara, magani kuma daga yau na daina amfani dashi, ka yi hakuri ba zan sake ba."
Kuka nake tukuru, harda face majina. Sai jikinsa ya mutu, ya riko ni muka zauna kan gado yana cewa." Tunda wannan shine karo na farko na yi hakuri, kuma kin yi alkawarin ba za ki sake ba, amma ina so yau ki ba ni kulawa ta mussaman domin a mutukar buk'ace nake dake."
Da sauri na ce." In sha Allahu na yi alkawari ba zan sake shan magani ba, kuma san dinga baka kulawa." Ya girgiza kansa yana bina da wani shu'umin kallo.
Saurin fahimtarsa da rashin riko ya sanya nake jin zan iya cigaba da rayuwa da shi duk da cewar har yanzu zuciyata bata gama aminta dashi ba.
Dinkin da na yi wa Salimat ya d'agawa Jamila hankali, ta fito tana ta zage zage da neman fitina, tana kiranmu da munafukai ni da Anti Maimuna. Babu wadda ta kulata a cikinmu. Hakan ya k'ara yi mata ciwo, da maigidan ya dawo ta gaya masa. Ya shigo yana tambayata na ce masa hakane na yi wa Salimat da Yusura d'inki iri daya.
Ya yi shiru na minti biyu kafin ya ce." Kema Amina ba ki so zaman lafiya, mai zai sanya ita jamilar ki kasa yi mata kawaici, itama ai sai kisa yaronta daya zata ji dadi."
Saboda ba na so maganar ta yi tsayi na ce." Allah Ya kaimu wata shekarar sai ayi, amma ka gaya mata d'azu da ta fito tana zaginmu ba tsoronta ba ne ya sanya na yi shiru, saboda muna watan Azimi ne, wallahi ta kara zagin iyayena sai na yi mata duka."
Yana dariya yake cewa." Ke yanzu kina ganin Jamila zata daku a hannunki?"
Na ce." Abu ne mai sau'ki." Sai ya tashi ya fita yana dariya tare da cewa." Amina rigima kenan."
Washe garin sallah Yusura ta tafi gidansu don tun kafin sallar take ce mini a can za ta yi. Kamalu har ya yi naci da magiya ya gaji, so yake na bar su su je gidan Gwaggwo su yi sallar a can na ce a a dalili ba na son abinda zai sake danganta shi da unguwar muddin ba da ni ba, balle har su hadu da Saminu. Haka nan ya ha'kura, gashi ba wani shiri yake yi da yaran gidan ba, sai ya sake takura sosai, shi Yusi Yana can wurin Salimat a can ma yake wanka kaf kayan sallarsa suna wurinta. Anti Maimuna ce ta tursasani barinsa ya bi yaran gidan zuwa gidan kakarsu uwar mijinmu Hajiya dogara. Ba yadda na iya da ita, saboda zahiri Ina ganin kimarta ganin yadda take mu'amulantata a gidan. Kamalu ya dinga murna da tsalle, Yusi yana kyalkyala masa dariya. Da zasu tafi sosai na yi masa fada akan ya kiyaye ya kula banda rawar kai, kuma babu ruwansa da Turzumi tunda ba shiri suke yi ba. Ya yi mini alkawarin zai kula.
Sai dai kuma sai da na yi dakacen barinsa zuwa gidan Hajiya Dogara dalilin satar da tace ya yi mata.
Suka dawo gidan kowa ransa babu dadi, domin tun a can Turmuzi ya Tara 'yan unguwa suka ture shi suna yi masa ihun b'arawo.
Yadda ya shigo a firgice shine abinda ya tabbatar mini da cewa babu lafiya. Yana zama ya fashe da kuka! Hawaye masu tsananin gudu suka dinga tsere a kumatunsa.
Ina ji yo hayaniyar yaran gidan daga waje muryar Jamila tana ta tashi. Salimat da Yusi suka shigo. Ta zauna a sanyaye tana cewa." Wallahi bai d'aukarwa Hajiya Dogara kudi ba, ni na rasa ma a inda ta ji cewa Yana sata. Abinda ma tunda muka je gidan bai zauna ba Yana kofar gidan a zaune, sai da zamu ci abinci ne na ce a kirawo shi, wai amma tana bud'e jakarta ta duba ta ga babu dubu daya sai tace shine ya d'aukar mata. Sai da zamu tawo tukkuna tana daga kasan tabarma ta ga kudinta ashe anan ta ajiye.
Amma sai ta yi shiru ba tace komai ba, kuma tana ji fa Turmuzi ya Tara Yara suna yi masa ihu amma bata hana shi ba, kuma bata gaya masa cewa taga kudin ba."
Murmushin takaici kawai na yi na ce." Salimat tashi ki je kawai Allah Ya kyauta."
Ta tashi jikinta duk a sanyaye ta fita.
Yusi ya dube ni, murya na rawa ya ce." Mama me yasa kowa ya tsani Yayana ne?" Sai ya fashe da kuka ya kwanta kasan kafet yana rerashi."
Na dubi Kamalun da lokaci guda ya firgice. Na ce ka gaya mini gaskiya ka d'auki kudin Hajiya dogara ko baka d'auka ba?"
Ya sa hannu ya goge hawayen da yake zuba a fuskarsa. Ya ce." Wallahi ban d'auka ba Mama sharri ta yi mini."
Na girgiza a kai, a raunane na ce." To shikkenan ni ma na aminta baka d'auka ba, yadda yanayinka ya nuna, ka share hawayenka ka ji ko."
Ya sauke ajiyar zuciya tare da sanya duka hannuwansa biyu Yana goge fuskata.
Koda maigidan ya dawo ban ce masa komai ba. ba wai don abin bai yi mini ciwo ba, sai don kimanta mahaifiyarsa. Amma zahiri da wata ce ta yi mini haka inaga sai na daureta. Kuma maganar ban san abinda zata haifar ba tunda Ina kan dokin zuciya, kuma uwa ta zarta komai. Ina fata hakan dai ya zama na farko domin idan ta sake faruwa ba na tsammanin zan yarda.