← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 35

Sashe 27

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tun daga ranar Yusi bai kara shiga cikin yaran Jamila ba. Ni ma kuma ban 'kara barinsa ya fita ba. Idan garin Allah ya waye muna tare a wurina. Kamalu na taimaka mini, shi kuma yana ta wasansa shi kadai.
Anti Maimuna ta same ni kan cewa hakan da na yi bai dace ba, na takure yara wuri d'aya na hana su sakewa. Na ce mata yadda na yi shine kwanciyar hankalina. Duk da haka ba ta ha'kura ba sai da ta san yadda ta yi ta janye Yusi ya zama d'an dakinta. Ganin kwana biyu Yana zuwa wasa lafiya lau ba a dukansa, sai na kyaleshi, dama kamar yadda ta fad'a babu yadda za a yi yaro ya rayu shi kadai, ko shi Kamalu dana takure a wuri d'aya don ba yadda zai yi ne. Shiyasa lokacin da suka fara zuwa makaranta kamar ya zuba ruwa a kasa ya sha saboda murna.
Na gargad'e shi sosai, akan ya kula. Inda hankalina ya kwanta ma direba ne yake kai su ya kuma dawo dasu, Islamiyya ce kawai suke tafiya da kansu tunda a cikin unguwar take.

Yusi ya riga ya zama d'an d'akin anti Maimuna, don jininsu ya hadu da Salima, itace ta k'ara ri'ke shi, ko makaranta tare suke tafiya, ba ya jiran d'an uwansa, Yana shiryawa yake zuwa wurinsu, sai dai shi Kamalun ya tafi shi kad'ai.
Hakan ya daga hankalin Jamila, macece mai zargi, ta hana mu sakat a gidan, neman rigimar yau daban dana gobe, fadi take na zo na rikita musu gida, ina ko'karin rabawa yaransu zumunci, tunda dalilin sha'kuwar Yusi da yaran anti Maimuna ya haddasa ba'kar gaba da rikici tsakanin yaran nasu. Turzumi da 'yan'uwansa, kaf sun daina shiga wurin Anti Maimuna, wanda dama can nan ne, dandalin wasansu, saboda ita tana da sau'kin hali, kuma tana jurewa hayaniya shiyasa kowane yaro yake da sakewaa wurinta, ba kamar ita jamilar ba.

Ni dai tunda muka yi cacar baki akwanakin baya, ban sake bi ta kantaba, al'amurana sun sha kaina. Yanzu na ajiye d'inkunan jakkunkunan da nake yi, na durfafi manya dinkuna irin na mutan nijar mali, da sengal. Tun lokacin da na je Maiduguri bikin Babandi na yi wa Ya Falmata d'inki, Allah Ya haskaka al'amarina. Jama'a suka dinga kar'bar style a wurinta. Kawai sai ta yi tunanin sayan kayan aiki da irin sutturun da suke tu'amalli, ta kira ni a waya tana sheda mini, za ta turo mini da aikin, idan na kammala sai nasa a mata a mota, ita tana da masu saya a hannu.
Na yi ta godewa Allah, saboda na san wani cigaba ne ya zo mini. Sai dai tunda na fara had'a-hadar ayyuka suka yi mini yawa, ranar girkina na kan sha wahala sosai, kuma wani aikin idan ta turo mini da sauri ake bu'katarsa.
Kamalu makaranta dama shine yake taimaka mini da sanya zufa, jera stones kalmasa da sauransu duk ya iya wannan, Hamusu ko Usaini wani daga ciki ya kai mini tasha a dora a mota.
Yanayin aikina ya fara ta'ba zamantakewata a gidan. Domin ranar girkina zahiri ni ma na sani, ba na gama abincin rana da wuri, Yara suna makara a makaranta, wasu lukutan ma haka suke tafiya ba su ci ba, sai sun dawo tukkuna. da daddare ma sai na kai bayan Isha'i, ban fito daga kicin ba, gajiya ta rafkar da ni, maigidan ya zo da buk'ata na kasa katabus, jikina ya mutu, babu wata kulawa da yake samu.
Anti Maimuna dai tana yi mini kawaici ba ta ta'ba korafi ba. Jamila kuwa mun sha musayar yawu da ita, domin duk lokacin da ban gama abincin rana da wuri ba har yara suka tafi makaranta ta dinga mita kenan, kamar ta zage ni, tana fad'in ai ba neman kudi na zo yi ba, bautar aure na zo yi, akan me zan dinga azabtar dasu. Wasu lukutan shiru nake yi mata, amma idan ta kai ni bango kaca-kaca nake yi mata na ce ba zan yi girkin ba, ta yi duk abinda za ta yi.....✍️
*Gudun aure 1k on talgram via 0542382124....Binta Umar gtbank ko 7084653262 Binta Umar Opey bank. Yan nijar dala dari katin Airtel. Ga masu bin wannan book din ina miko gaisuwata zuwa gareku. Ina daf da kammala free peges tuntuni dai an fara payment labarin nan ba mu fara shi a hakan zan ce muku sharar fage ne. A hanzarta biya domin jin yadda za ta kaya. Na gode muku masu messages fatan alheri tare da yabo bisa wannan littafin Allah Ya saka muku da alheri🤲💝*
*07084653262*

*TALLAH!*
🌲🌳🌿☘️
*DA MAGANI A GONAR YARO!!*
*08089965176*
*07084653262*
*Dayawa akwai matan da suke da matsala ta lalacewar nono yamushewa da kuma fad'uwarsa. Wasu ma 'yan mata ne basu kai ga matakin aure da shayarwa ba amma sai su samu matsalar faduwar nono. To gaskiya akwai magani sai dai kawai idan ba a yi dace ba. Wasu zasuyi ta faman kashe kudi amma buk'ata bata biya ba, wasu kuma zasuyi ta fargaba kada su je garin neman gira a rasa Ido, ma'ana su sayi abinda zai cutar dasu da kudinsu. Kuma yanzu dai tsakani da Allah rijalu sun riga sun gama nuna abinda suka fi karkata a kansa a jikin 'ya mace kirji da kuma baya. Wasu Allah ya hallice su dashi har ya yi musu yawa, wasu kuwa basu dashi kuma mai saurin zubewa ne. To mu dai duk wanda ya san maganinmu ya san ingantacce ne, kuma Yana aiki kwarai da gaske wurin dawo da daraja da martabar nono da izinin Ubangiji. Sahihin magani ne da ya samu sheda da lambar yabo, kuma Islamic ne da akayi masa hadi mai inganci domin gyara jikin mace ba ma iyakacin nono kawai ba. Babu nadama haka zalika babu dana sani da asarar dukiya wurin sayan maganinmu. In sha Allah matsalar ki zata gushe idan kin jarraba amfani dashi. Ba mu tsaya ina nan ba, muna da na gyaran hips sahihi dana k'iba idan kina fama da matsalar rama. Haka zalika muna dana tumbi, da kuma maganin sanyi mai mugun kyawun da yake kassara kowane irin sanyi na fili da boye wanda zaku hadu da maigidanki kuyi amfani tare. Akwai ingantattun supplement wad'anda basu da illa balle su cutar da GARKUWAR jiki. Sai dai su gyara su kuma tayar da komad'a ina nufin inda ya samu nakasu a jikinki. Muna sayar da sabulan gyaran jiki dilka da man gyaran gashi, muna kuma bayar da sari a fad'in najeria da nijar muna tura kayanmu kowane gari da ikon Allah.*
*Muna garin kano duk inda kake za mu aika maka da kayanmu. Domin neman karin bayani sai a yi mana magana ta Whasap ga lambobin da za a same mu a kai.*
*07084653262 ko*
*08089965176*
*SIYAN NAGARI!!!!!!*
*A JARRABA A SAMU BIYAN BUKATA DA YARDAR ALLAH*
[11/26, 10:38 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A*
*TALLAH!*
*Gidan 'kawa ne da kece raini.💯*
🛍️ “Ko ba ki da niyyar siya ba, ki zo ki shiga ki kalla kayayyaki — wallahi sai kin bude ido! Ballantana kuma nasan za ki tashi da kaya saboda kyau da araha.” ✨
🌸✨ “Shigo duniyar da kyau da jin daɗi suka haɗu — daga kyawawan laces na alfarma, Atamfa , abaya masu salo, zuwa kayan ado masu kyalli, kayan girki na zamani da sauran ƙarin abubuwa. A Meerah B Collection , muna adashen kayan kitchen daily 1k to pack 100k items weekly Monthly ✨🌸We are sale kitchen items, electronic, WE ALSO DEAL WITH CONTRIBUTE monthly weekly daily after 10 days for kitchen items or electronic gaba daya wanna package 60k nake had'a sa zaku iya mallaka ta hanyar adashi

https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t https://chat.whatsapp.com/KXsuo5E7syZ879Gcid3wCm?mode=ac_t

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale*
*17*
*Free pege*
Ashe akan ga'ba muka yi wannan sa'insar. Sai maigidan gabad'aya ya d'auki laifi ya d'ora mini, yadda yake yin fad'a shi ya kara tabbatar mini da cewa a kufule yake da ni, dama yana Jin haushina.
"Zaman aure ki ka zo gidana Amina, na gaji da rabon fad'a, kusan koyaushe Jamila sai ta kawo mini korafi akanki, na gaya miki tuntuni matan nam suna zaune lafiya, ban saba da irin wannan tashin hankalin ba, me zai sanya daga zuwanki ki d'aga mana hankali, muddin ba za ki bi umarnina ba, kamar yadda na sanya ki ka ajiye aiki, to d'inkin ma za ki daina yi mini a gida, domin ba zai yiwu ki zo kina neman kudi a gidana ba, kuma kina watsi da umarnina, ni kaina ba na samun kulawa a ranar girkinki, kin fi bawa neman kudi muhimanci, ki gyara muddin kina so ki zauna da ni."
Ban katse shi ba har sai da ya kai 'karshen maganarsa na ce."Ka yi hakuri don Allah, in sha Allahu zan gyara, maganar kuma na zo zan lalata maka gida babu wannan ajandar raina, da zuciya daya na shigo gidanka, sai kaine ma ka 'boye mini wasu abubuwa, amma hakan ba zai sanya na ce ka sake ni ba. Abu na biyu kuma ina kara gaya maka babu wata mace da zan yi wa biyayya, idan lallai sai na bi tsarin da matanka suka ginu akai ne to lallai ba ka shirya zama da ni ba, zan dai yi maka biyayya tunda kai ka ajiye ni. Sannan don Allah ina neman alfarma a wurinka idan zan samu."
Na kai 'karshen maganar ina dubansa. Ya ci kunu sai girgiza kafa yake yi da kyar ya ce."Wace irin alfarma ce?"
"Ina so na nemi mai aiki 'yar matashiya wadda za ta dinga taimaka mini, ka ga Allah Ya sanyawa lamarina albarka, ina so na yi amfani da damar kafin ta kubce mini."

Ya nisa kafin ya ce."Ita Iyami da take zuwa tana yi muku wanke-wanke da shara menene laifinta? Ba fa na son neman fitina Amina, idan ki ka ce zaki d'auki mai aiki ki ke kad'ai zai iya kawo hayaniya a gidan."
Chapter 27 · 0% Book details