← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 35

Sashe 13

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gyatsine baki ta yi ta kawar da kanta ba ta ce mini komai. Na yi dariya tare da mayar da hankali kan Ya Falmata dake cewa." Tunda kin zo kuma kin tabbatar mini dake tela ce, akwai atamfofina biyu da zaki dinka mini, sai dai fa kin san din'kunan mu sun sha bam-bam da irin naku."
Ba tare da damuwa ba na ce." Nuna mini irin wanda ki ke so a waya, anti Allah ya yi mini fikira fa."
Anti Yagana ta yi dariya tana fad'in." Lallai ni ma na yarda sai dai akwai saurin kuka."
Ya Falmata tana dariya ta fito da wayarta ta fara nuna mini irinsu. Ban ta'ba yi ba don gaskiya zasu ja kayan d'inki da yawa a can idan na ce su biya ayi musu babu wadda za ta iya fitar da kudi kusan dubu ashirin da wani abu. K'arkari dubu uku dubu hud'u. Sai ta yi wuta tukkuna suke iya biyan dubu biyar ayi musu d'inki.

Na ce." Anti an yi an gama in sha Allahu muddin akwai kayan d'inki ai abu ne mai sau'ki a wurina."
Ta ce." Duk abinda ake buk'ata yanzu zan aika kasuwa a sayo." Na ce." To shikkenan ni kuma in sha Allahu rabbi kafin dare na kammala miki. Cikin farinciki ta ce." Zan yi magana da Maman Sabir yanzu ma'kociyata ce tana da keken d'inki sai ki shiga gidanta a nutse ki yi."
Na ce." To shikkenan antina....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/18, 6:12 PM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*M.W.A.*

TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay

*@Arewa books*
*Bintuumarabbale.*
*Free pege*
*9*
A ranar yini na yi akan keke don duk wanda ya zo sai ya tambaye ni. Ango Babandi ya biyo ni har gidan muka sha hira irin ta zumunci. Shi din ba sa'ana ba ne, amma akwai sha'kuwa mai 'karfi a tsakaninmu kasancewar tun ina k'arama idan an kawo ni garin dashi muke wasa. Shine babban jika na d'a namiji a gidansu Mamanmu. Babansu shine babba a gidan, sai Baban Saude shine na biyu.
Na saki jiki sosai ina tsokanarsa amaryarsa tafi shi kyau shi ba'ki ne kamar shuni ita kuma kamar ka matsa jini ya fito. Ya dinga dariya yana fad'in ." Ai ganganci ne na auri bak'ar mace, ba zamu haifo yara bakake ba gwara a surka."
Na ce." Ai yanzu an fi yayin bakar mace, mazan ma duk sun gane, abinda wasu farin nasu na mai ne, ko da yake dai ita wannan amaryar taka ma tana yi mini yanayi da bafulatana."

Ya ce." Fulani ne usul gabansu da bayansu. hausarta ma bata fita sosai." Na ce." Ai na ga alama, Babandi Allah Ya sanya alheri. Shekara mai zuwa mu dawo suna."
Ya amsa da "Amin Yana gyara tsayuwarsa ya ce." Ke wai yaushe za ki yi aure ne, na san dai ba kya rasa mane ma."
Hankalina yana kan abinda nake yi na ce ." Duk ranar da Allah Ya nufa zan yi, Babandi aure da haihuwa da mutuwa duk na Allah ne, amma ina mamaki naga ana titsiye mace wai ana tambayarta yaushe za ta yi aure, abin yana daure mini kai wallahi."
Ya ce." Hakane gaskiya, amma fa sai kin sanya abin a ranki tukkuna. Allah Ya ce ka taimaki kanka ni ma zan taimake ka, Amina tunda mijinki ya mutu na ga take takenki ba kya son ayi miki maganar aure ."
Dariya na yi na ce." To ai auran ne ya zama abinda ya zama Babandi, da wahala yanzu na samu mai sona tsakani da Allah kamar Yaya Aminu. Wallahi gabad'aya mazan basa burge ni balle na ji sha'awar auran, ko ka ga na yi to Allah ne ya kaddara."
Ya dube ni a tsanake ya ce." Mu cire maganar wasa anan Amina, wanda ya mutu fa ya riga ya mutu, kada ki tauyi rayuwarki da k'uruciyarki, ki ce za ki zauna haka, ko bayan haka ma kina da sha'awa irin wadda Allah Ya 'kaddarawa bayinsa, aure shi zai katange ki daga fad'awa wani halin."

Na numfasa tare da ce wa." Babandi ban san me yasa rashin aurena yake damun mutane ba wallahi. Sai na ga 'yan mata suna zaune a gaban iyayensu ba a matsa musu ba sai zawarawa. Duk wanda zai dube ka sai ya yi maka wata fahimta. Babandi ka ganni nan wallahi babu wanda yake yi mini wahala ni nake yi kayata. Kuma ina kula da kaina sosai bana taba barin wata kofa da zata janyo mini 'bacin suna. Sana'ata kawai na sanya a gaba, a yanzu burina yarana su yi wayo Allah Ya taimake ni su tsaya da kafafunsu, su samu ilimi da tarbiya. Sai na ji dadin auran."

Ya harareni Yana furta." A lokacin kin tsufa kenan, kina maganar shekara ashirin fa anan gaba Amina. Lokacin kin yi hamsin, wane namiji ne zai yi kwad'ayin auran tsohuwa."
Na fashe da dariya ina cewa." Shikkenan ka ga sai na k'arasa rayuwata a haka, dama ba na so na yi aure ranar lahira na tashi a matar wani, nafi so na tashi a matar uban yarana."
Ya ce." Wannan ba hujja ba ce Malama sai kin yi aure fa, idan ba ki da tsayayya a cikin abokaina akwai wanda yake son kari, idan ma ba za ki auri mai mata ba akwai samari. Tunda Allah Ya sa kina da jiki mai kyau na san da gudu za a aureki."

Na ce." A a ba sai ka kawo mini kowa ba. Na kusa in sha Allahu. Akwai wani mutumin Ubangidan Baba Sule a kasuwa, akan maganarsa muke ina fata zaka tayani da addu'a Allah Ya sa alheri ne. Wata'kila ma ina komawa gida da 'yan kwanaki ku ji labarin d'aurin aure."
Cike da farinciki ya ce." To Alhamdullahi, ina
taya ki murna da fatan alheri, Allah Ya sa idan kin shiga kin shiga kenan, Allah Ya kad'e fitina."
A takaice na amsa da Amin." Maganarsa da muka yi yanzu ita ta tuna mini da wayata dake kashe. Jiya da daddare bayan mun gama waya dashi na kasheta ba don komai ba sai don gudun kada ya kira ni ina cikin jama'a, na lura kuma shi yana son yawan waya kamar matashin saurayin da yake da sabuwar budurwa. Ni Kuma sabgogina sun isheni zaman yin wayar nan ba ni dashi, don sai na ga kamar batawa kai lokaci ne.

Sai da na koma gidan anti Yagana tukkuna na kunna wayar bayan na gabatar da sallar isha'i. Jikina ya yi tubus gajiya ta dirar mini, ta zaman mota da zaman keke. Bacci ya fara surata, Yusi Yana can cikin yaran anti. Da yake Yana da saurin sabo ya sake dasu duk inda zasuje sai su ja shi. Anti Yagana ta shigo tana fad'in." Ga abinci nan na tawo mana dashi, idan za ki ci sai ki fito ki d'iba."
Na ce." To shikkenan anti Gajiya ce ta addabeni wallahi." Tana ko'karin fita daga d'akin take cewa." Ai dole, zaman mota da zaman d'inkin nan da ki ka yini kina yi. Ki sha Panadol mana."
Ido a lumshe na ce." Anti ba na so na sabawa kaina da shaye shayen maganin nan, gari Ya na wayewa zan warware."

Ta fita daga d'akin ba ta ce komai ba.
Ina jin kiran waya na san wanda nake tsammani ne. A nutse na daure na daga wayar da sallama a bakina.
Ya sauke ajiyar zuciya Yana cewa." Wato saboda kin lura na kamu da sonki shine za ki yi mini jan aji ko Amina, da alheri fa na zo gare ki, ba zan cutar dake ba."

A sanyaye na ce." Ba haka ba ne wallahi, yau na yi ina wani uzuri ne, shaf na manta ban kunna wayar ba sai yanzu, amma ka yi hakuri, kuma ai ka bari mu gaisa ko."
Ya sake sauke ajiyar zuciya a karo na biyu Ya furta." Dukda haka dai ba ki damu dani ba Amina, ai jiya kafin mu yi sallama kin yi mini alkawari za ki kunna wayarki, sannan Zaki sanar da ni shawarar da ki ka yanke akan sha'aninmu. Amma gari Yana wayewa na ji waya a kashe, yini na yi cikin zullumi wallahi."

Yadda yake tausasa murya da lallashi. Sai Yaya Aminu ya fado mini a raina. Kwalla ta taru a idona. Shi ma haka yake yi mini wasu lokutan ma ni na ce da laifi amma sai ya mayar dashi kansa yayi ta rarrashina. Nasa yatsa na goge kwallar da ta fara zuba. A sanyaye na ce." Ai na
bada ha'kuri Alhajina, a yi mini afuwa ba zan sake ba."
Ya ce." Na yi miki afuwa, amma ki dinga kira na kina jin lafiyata Hakan shi zai tabbatar mini da cewa kin damu da ni."

Murmushi na yi na ce. " In sha Allahu rabbi zan yi Hakan, sannan albishirin da zan yi maka shine na amince da auranka. Daga zarar na dawo sai mu tsayar da magana."

Cikin wani irin yanayi na farinciki da karsashi yake furta." Alhamdullahi. Allahamdullahi, na gode Allah Amina, ni ma albishirin da zan yi miki shine idan an daura auranmu zamuje saudia mu yi godiya ga Allah."

Cikin jin dadi na ce " Aikuwa na gode sosai da wannan karamcin, Allah Ya kara suttura, Ya kuma raya zuri'a." Ya amsa da "Amin cikin walwala da farinciki, yadda yake nunawa shi yake sake tabbatar mini da cewa 'Sona yake yi bilhaki da gaskiya' Ba auran dandano zan yi da ni ba. Zuciyata ta kara aminta da auransa na san a hankali idan da kyautatawa soyayyarsa zata shiga cikin zuciyata. Muka yi sallama cikin mutumci da kulawa.
Chapter 13 · 0% Book details