← Book details Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 35

Sashe 17

Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

***
Na koma hannun Ummansu Hadiza gabad'aya. Da farko kamar abin arziki sai daga tafiya ta mika tukkuna ta fara nuna fifiko da bambamci a tsakanina da yaranta Hadiza da Fati wadda ta haifeta bayan rasuwar Mamanmu. 'Kiri'kri take nuna komai. Ina kallo zata sayawa yaranta wanduna da 'yan kunnaye da kayan kwalliya ni ba zata saya mini ba. Sai dai na je gidan Gwaggo idan ta lura babu d'an kunne a kunnena sai ta saya mini ko ta cire na kunnanta ta sa mini. Wasu lukutan ma haka zata dafa ruwan zafi ta wankeni da wandon jikina wanda sai ya fi wata d'aya ban cire ba. Gwaggo itace take saya mini wanduna da kayan kwalliya sannan itace take tsefe mini kai ta ba ni kudin kitso na shiga nan makotansu a yi mini.
Da Ummansu Hadiza ta lura da Hakan sai ta hana ni zuwa gidan gabad'aya. Idan mun taso daga makarantar allo Hadiza zata shige ta kwanta ni kuwa zan yi shara da wanke-wanke sannan na je wurin Babamu na kar'bo kudin cefene na je na yi. Tun ban kai shekara goma sha biyu ba na ke yi mana girki. Nasha k'onewa a hannu da k'afa wasu lokotan idan na nuna mata sai ta yi mini banza, sai ta ga dama za ta ce mini sannu. Haka nake warkewa. Kayan makarantarmu na boko ni nake wanke mana. Wani sa'in ma idan Ina wanki Ummansu Hadiza za ta de'bo 'yan k'ananun kayan tagwayen da take goyo Hassana da Usaina ta watso mini tace na wanke musu.
Ba ni da lokacin kaina kullum idan naje makaranta na dinga gyangyad'i kenan, domin wasu lukutan ma da daddare har aikena take yi wurin masu awo da kantina idan tana buk'atar wani abu.

Watarana mun dawo daga makarantar boko ni da Hadiza nuna tafiya sai ga Yaya Aminu akan Kekensa. Na dinga washe baki ya tsaya a gabanmu Yana murmushi. Hadiza ta murguda bakinta ta bar wurin bata gaishe shi ba. Ni kuwa muka gaisa sosai Yana yi mini wasa kamar yadda ya saba a lokacin da yake tambayata me yasa na daina zuwa gidansu ban rufe masa ba na sanar dashi Ummansu Hadiza ce ta hana ni.
Ya rarrasheni sosai yana fad'in ki cigaba da ha'kuri dadin abin ma ke macace aure za a yi miki watarana sai labari. Ya d'auko dari biyu ya ba ni.

Ina shiga gida Ummansu Hadiza ta rufe ni da fada wai na tsaya shiririta bayan na san akwai abinda zan yi. Na ce mata mun gaisa da Yaya Aminu ne shiyasa ban shigo da wuri ba. Hadiza tana daga cikin d'aki na ji tana cewa wannan cangal din ai dan'iska ne, ki cigaba da tsayuwa dashi zai lalata ki.
Raina ya b'aci sosai. amma sai na share ta ban ce komai ba, itama Ummantasu bata kwa'beta ba. Na cire kayan makarantar jikina domin yin abinda yake gabana.
Sa'i da lokaci Yaya Aminu ya kan ba ni dari biyu a duk lokacin da muka had'u. Ni kuma zan kar'ba da murna da farinciki domin wannan dari biyu da yake ba ni tana taimaka mini sosai a makaranta idan ana birek don ma wani sa'in Sahura tana zuwa da abinci sai mu ci tare ina rage yunwa mutuka. Su Hadiza Ummansu tana basu hamsin hamsin kullum. Ni ce dai bata bawa. To ashe tana lure da ni idan an fito birek din ina sayan Aya da gyada. Sai ta je ta gayawa Ummansu ita kuma ta titsiyeni tana tuhumata wai maza nake bi suke ba ni kudi suna tabbatani.
Na dinga kuka ina gaya mata ba haka ba ne. Yaya Aminu ne yake ba ni dari biyu wasu lukutan. Ta dinga fad'in to shi ma ai d'an iskan ne garjejen tuzuru dashi yana zaune shekara arba'in babu aure ai dole sha'awa ta yi masa yawa ya dinga tare yaran mutane Yana tattabe su. Na ce wallahi babu abinda yake yi mini Umma ki aika a kira Sahura ma ki tambayeta ni ba na kula maza.
Hadiza ta dinga fad'in itama Sahurar ai halinku daya haka take kashe kudi a makaranta.

Da Babanmu ya dawo ta gaya masa. Ya yi mini fad'a sosai, amma shi bai zarge ni ba. Sai da Baba Sule ya zo Ummansu Hadiza ta gaya masa. Ya dinga zagina Yana zagin Mamanmu har sai da ya dake ni da igiyar da muke shanya, yana fad'in ba zan gurb'ata musu zuri'a ba.
Ummansu Hadiza kamar wadda ta yi mini farraku da dangin Mamana ko an kai ni garin ba na dogon zango nake Sanya rigima sai na dawo Koda anti Yagana ta yi haihuwar fari ma da muka je da Gwaggo ta ce zata barni a can din na kwana biyu 'yan'uwa su gan ni. Kuka nasa sosai kan cewa ba zan zauna ba, kafata kafarta. Haka Dada za ta yi ta fad'a ta gaji ta ha'kura domin ba na iya sakewa dasu na dai fi son cikin wahalar kamar yadda Dada take fadi a koyaushe.

Sai zuciyata ta sake 'ke'kashewa na ji a raina babu wanda ya isa ya raba ni da alhalin Gwaggwo domin sune suka tallafi Mamana a lokacin da bata da kowa yanzu kuma suna tallafata. Duk da basu had'a ji'bi da Mamanmu ba 'kawance ne kawai da zaman gari d'aya ya had'a su da Dada amma kusan koyaushe na dubi gwaggo sai na ga kamar dangin Mamana nake tare dasu gabad'aya. kuma ina zuwa gidanta Muna gaisawa sa'i da lokaci amma ban ta'ba bari Hadiza ta farga da hakan ba.

Sahura k'awata ce sosai a bayan gidanmu gidansu yake. Ajinmu daya da ita a boko da allo haka zalika ma makarantar dare ajinmu daya da ita. Gidansu babane Babansu Yana da rufin asiri daidai gwargwado. Ya rasu ya dan bar musu d'an abin hannu kuma yana da akid'ar boko sannan akwai had'in kai a gidan zumunci bai lalace ba. Nan nake zuwa na huta a wasu lukutan na yi ta kuka tana tausata ina gaya mata ina so ko diploma ma ne na yi domin na samu aikin da zan dogara da kaina. Ita kuma ta yi mini alkawari za ta gayawa Baban yayansu a yi mana kokari a tare idan jarrabawarmu ta fito.

Muka ta so a gidanmu 'yan mata mu hud'u. Hadiza ce babbar cikinmu sai ni, sai Fati wadda aka haifeta bayan rasuwar Mamanmu, sai kuma tagwayen da ta yi. Daga su ba ta sake haihuwa ba. Sai da Babanmu ya auro Ummansu Saminu mai suna Sakina. Tana zuwa ta fara da maza ta gwaye Hassan din ya rasu kwana biyu da haihuwarsu.

Tsabar yadda nake wahala a gidanmu ya sanya na tsunbure jikina ya tsuke. Shekaruna suka 'buya. Sai ya zamana har su Hassana sun fi ni kyawun gani da 'kira ta 'yan matanci. Dama ba a zancen Hadiza da Fati tunda a lokacin Uwarsu a tsaye take a kansu da kayan ado da kwaliyya. Gasu da jiki ruguzaza irin nata. Babban burinta a lokacin miji ya fito ta yi musu aure gabad'aya. Ba ta damu ni da halin da nake ciki ba. Duk sai da suka riga ni fara al'ada. Na dinga nuku-nuku ranar da na fara na b'uya ina kuka. Da 'kyar na gyara kaina. Na bi duk matakan da ake koya mana a makarantar dare. Sai dai wandunana biyu ne kacal gashi ba ni da audiga ina dai ganin su Hadiza da ita suna amfani ni kuma sai na yagi dankwalina na kasa shi biyu nake kunzugu dashi. Su yi tayi mini dariya Usaina ce ma daga cikinsu ta mu ta zo daya itace a 'boye take d'auko mini audigar a cikintata ta kawo mini.

Anti Sakina wato Ummansu Saminu itace daidai da Ummansu Hadiza domin dama ita a shirye ta shigo gidanmu. Kuma tunda ta ga ta fara da maza a gidan ta gyara zamanta. Itama Ummansu Hadizan tunda ta lura da cewa 'yar bana bakwai ce ta shafawa kanta lafiya. A wasu lukutan tana yi magana idan ta ga son zuciyar da ake yi a gidan. Ta dinga fad'a tana cewa su yaranki shafaffu ne da mai ne da ba za su yi aiki ba. Wannan ba gata ki ke nuna musu ba Murja aure za ki yi musu ba kuma ki san inda zaki kai su ba. Ita wannan din ki kewa gata. Wahala dai mai shigewa ce, kuma shi da ba a yi masa mugunta domin ba kasan ranar da zai yi maka ba.
Makamantan maganganun take yi mata a duk lokacin da ta su ta had'o su a gidan. Ni dai ba na cewa komai sai dai na yi musu shiru su yi su gama. Na dai ajiye a raina cewa watarana sai labari.

Daf da za mu yi saukar al'kur'ani a makarantar allonmu wani Alhaji Halilu mai kudi da mata biyu ya fito fagatatan Yana son auran Hadiza wata uku kacal yake so a sanya a d'aura auran Babanmu ya ce bai shirya ba domin bai ajiye komai ba. Mutumin ya ce gidansa akwai duk abinda ake buk'ata ba sai an wahalar da kai ba. Babanmu ya ce za a yi bincike tukkuna ya jira shi. Baba Sule ya yi tsalle ya shiga sha'anin bai bari an tsananta bincike ba ya ce tunda yarinyar tana so a maganata ta 'kare. Kuma dai yanzu a sha'anin aure kawai a binciki aljihun mutum, idan zai iya ri'ke iyali ai an yi barka. Balle ya ji labarin mutumin da rufin asirinsa harkar motoci yake yi. Babanmu Ya ja bakinsa ya yi shiru bai sake magana ba. Baba Sule shi ya yi ruwa da tsaki ya kar'bi kudin auran dubu dari masu danko irin na da.
Chapter 17 · 0% Book details