Sashe 21
Gudun Aure Book 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Saukar hannu na ji a kumatuna. Da sauri na bud'e idona, sai na ga Yusi a gurfane a gabana Yana kuka harda shashsheka. Gefe kuma Kamalu ne ra'kube a jikin kusurwa sai ajiyar zuciya yake saukewa.
Ganin haka ya sanya na yi namijin ko'karin daidaita kaina. Na tashi na dan gyara abinda ya samu a d'akin. Na gyara musu shimfida kafin na kira Usaini na bashi kudi ya sayo mana abinci, don ba zan iya yin komai ba saboda gajiya da fargaba.
Suna cin abincin na ce dasu su kwanta sai da safe kuma.
Suka shiga net din a tare Ina kallon yadda Yusi yake ta rirri'ke dan'uwan nasa da har yanzu yake a tsorace Yana ganin zan shammace shi ne kamar yadda na saba na zane shi.
Kiran anti Yagana ya shigo wayata dake cikin jaka. Na d'aga da sauke ajiyar zuciya. Tambayar da nake hasashe ita ta jefo mini.
Na ce." Ai an gama komai sun ba mu yaran. Amma sai da aka yi dauki ba dad'i sosai da jama'ar unguwar.
Ta ce." Ubangiji Allah Ya kiyaye faruwar hakan anan gaba, ki yi ta addu'a watarana sai labari."
Na ce." In sha Allahu rabbi anti, sai da safe."
Muka yi sallama na ajiye wayar na fita na d'auro alwala domin ban yi magariba da isha'i ba. Da kyar na iya tsakurar abinci, hakan ma don dai kada na kwanta ban ci ba, na cutu, shiyasa na ci kad'an, na zame na kwanta a kan daddumar ina lumshe ido. Bacci ya fara fizgata kira ya shigo wayata a karo na biyu, ban kawo kowa ba sai Alhaji Muntari, shine ya kan kira ni a irin wannan lokacin, sai na kan rasa azancin hakan, mutumin da yake da iyali ai a irin wannan yanayin ya kamata ace yana tare da wadda ta yi girki.
Ban saki jikina ba sosai, dalilin damuwar da nake ciki, da kuma fargabar kada hakan ya haddasa masa rikici a cikin gida domin na san ba kowace mace ba ce za ta iya daurewa da hakan, na dinga yin hamma ina amsa masa magana a kasalance. Hakan ya sanya shi yi mini sallama yana fad'in da safe zai sake kirana mu k'arasa tattuna maganar tunda na dawo a satin yake so a yi komai a gama.
Na ajiye wayar. Idona a lumshe na cigaba da nazarin yadda abubuwan za su kasance anan gaba, ko na'ki ko na so, dole na auri Alhaji Muntari domin katange kaina da mummunar kaddarar da take shirin rufto mini. A zahiri na furta 'Allah Ka takaita mini wahala'
Ban yi wani baccin kirki ba dalilin tunanin da ya'ki barina, akan kunne da idona asubahi ta yi. Na yi sallah, yaran ma na tashe su kamar koyaushe suka daura alwala suka fita. Ban koma bacci ba domin na san akwai wad'anda za su dako mini sakammako abinda ban k'arasa ba, na kammala. Duk wadda ta zo kar'bar dinkinta ba na yarda na bata sai ta cake mini kudina tukkuna. Domin zurga-zurgar nan, da wannan matsaltsalun kudin hannuna duk sun kare, don dai ma Alhaji Muntari ya taimaka mini da wasu.
Yusi ne ya shigo shi kadai jikinsa sanyi kalau saikace wanda ya tashi daga ciwo fatar samar idonsa duk ta tasa, tamkar shi ya aikata lefin duk ya shiga damuwa. Na kalleshi a nutse na ce ." Ina Kamalun yake?"
"Yana can massalaci a kwance Yana bacci, wai kafarsa ce take ciwo. Mama kin ga har ta kumbura."
Na ce." Je ka taso shi, ka ce ya zo in ji ni."
Ya kalle ni. "Mama tsoro yake ji kada ki dake shi, shiyasa ya kwanta a can.
Na ce."Ai da zan dake shi da tuni na dake shi Yusi, addu'a na ke yi masa, Allah Ya shirye shi." Ya saki ajiyar zuciya Yana fad'in." Bari na je na kirawo shi."
Ya fita da sauri.
Minti uku da fitarsa Hamusu Ya shigo. Muka gaisa ya ce." Tun jiya na so na shigo mu tattauna Allah bai nufa ba, da yake ban dawo da wuri ba, Gwaggwo duk ta sheda mini abinda ya faru, anti Amina jama'ar gari suna ta zaginmu akan mun sakar miki wahala, don Allah wannan karon kada ki ce a a, ki ba mu yaran nan, su koma hannunmu da zama, komai Yana da lokaci, kuma in sha Allahu yaran nan, sai duniya ta amfana dasu."
A nutse na ce." Ban ki maganarka ba Hamusu, kuma ban ce kun gaza mini ba, ni dai har duniya ta nade babu kalmar zagi ko 'batanci akanku, duniya ban ga abinda za ku yi mini ba Hamusu, domin Iya k'auna kun nuna mini. Ba wai ba na son ba ku yaran nan ba ne, ina tausayawa Gwaggo da shekarun tsufa suka cimmata. Ta rainin yaranta cikin nutsuwa da kwanciya hankali, ba zai yiwu ace kuma yanzu da take buk'atar kulawa a kai mata wahala ba. Ku barni da yaran in sha Allahu babu abinda zai gagare ni."
Ya ce." Ai kin san na kusa aure, zaman da yaran za su yi a hannun Gwaggo na hucin gadi ne, daga zarar na yi aure da 'yan watanni sai su koma hannuna da zama, in sha Allahu zan ri'ke su da kyau, haka nan yarinyar da zan aura na sanar da ita duk abinda yake faruwa kuma ta ce ta amince za ta ri'ke su."
Na dube shi cikin nazari. Wato wasu lukutan maza suna da gajeran tunani. Ta ya za a yi amarya daga aure ta fara jigila da yaran ma da bana mijinta ba. Akwai matsala babba wadda shi ba zai fahimta ba a yanzu sai zama ya yi zama tukkuna. Yanzu yarinyar zata furta karya domin tabbatuwar auran, idan ta ga ta shiga daga ciki sai ta canza alkibula.
"Hamusu wannan karon ma dai Ina ba ku hakuri, kuma ma dai har gida zan zo wurin Gwaggwo mu tattauna, aure zan yi nan da sati biyu in sha Allahu, kuma wanda zan aura ya amince mini, zai kula mini da yaran nan, ba ni na nuna ina son hakan ba, shi da bakinsa ya furta, ka ga kuwa bai kamata mu watsa masa kasa a Ido ba, sannan ina so da ni da yaran gabad'aya mu yi nesa da unguwar nan, Kamalu ya canza abokai, muna cigaba da addu'a sai ka ya dabi'un nasa sun canza gabad'aya.
A sanyaye ya ce.' Anti Amina surutun mutane shi yake damuna wallahi, Baba Sule sai ka ce babu dangatanka duk inda ya zauna sai ya zagi Gwaggo, ya aibata mu, kuma kin ga ba lefinmu ba ne, duk talaucincmu ba zamu kasa ri'ke yaran nan ba."
Cikin takaici da b'acin rai na ce." Ka yi hakuri Hamusu, don Allah kada ka sanya damuwar Baba Sule a ranka, ni kaina bai barni ba, kuma Allah da zuciya yake amfani, kai dai ka cigaba da yi musu addu'a. Komai zai zama tarihi."
Ya ce." In sha Allahu rabbi anti."
Yaran suka shigo d'akin. Gabad'aya muka dube su. Da gaske dai d'ingisa k'afar yake gefanta ya kumbura kadan. Ya zube a bakin k'ofa, murya na rawa yake gaishe da kanin Uban.
Bai amsa ba hankalinsa yana kan kafarsa ya ce." Garin tura kurar ruwan ka ji ciwo, domin an ce kaine jami'i wurin d'aukar kurar ko?
Ya girgiza kansa yana fad'in." Ba ni ba ne, Shamsu ne ya tura kurar ni kuma na d'auki jarakuna biyu, muka nufi kasuwa, sai Saminu da ya cire wili da taya ya sayar."
Ya girgiza kansa tare da furta." Allah Ya shirye ku. Ya dube ni kaina a kasa domin duk sanda na kalli yaron Ina ji kamar na fasa ihu.
Ya ce." Bari na je na kira Abdullahi mai chamis ya zo ya duba shi.
Na ce." Anya Hamusu kafar nan, ba targad'e ba ne, dukansa fa suka yi 'yan sandan."
Ya ce." Ai dole su dake shi tunda ya yi yun'kurin guduwa, idan suka riga suka kamaka, kawai ka mika wuya.
Sai ya fashe da kuka Yana cewa." Ban yi yun'kurin guduwa ba, wani daga cikinsu ne ya rike ni ya dinga dukana da takalmin kafarsa."
Babu wanda ya tanka masa a cikinmu.
Hamusu ya tashi ya fita. Ni kuma na cigaba da abinda nake yi. Sai kawai na tsinkayi muryarsa yana cewa." Mama ina kwana?"
Na dube shi a nutse na amsa.
Ya yi shiru fuskarsa duk hawaye a bushe. Ya furta." Don Allah ki yi hakuri kin ji."
Na ce." Ai na ha'kura tuntuni."
Sai ya rarrafo kusa da ni, yana fad'in." Ki dake ni, idan hakan zai sanya ki daina damuwa a kaina, jiya na ga ba ki yi bacci ba, kina kuka."
Na ce." Yaushe ka ga ina kuka Kamalu? Idan ka ce ban yi bacci ba wannan na yarda, amma ban yi kuka ba."
Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya.
Na ce." Na yafe maka, Kai ma ka yi mini alkawari ba za ka sake ba."
Da sauri Ya ce.'' Wallahi ba zan sake yi ba, kuma ba zan kara kula Saminu ba."
Na ce." Allah Ya kyauta, Kai be Yusi d'auko kofi a kwando ka je ka sayo kunu, ina da sugar, sai ka wuce gidan awara."
Da sauri ya yi abinda na umarce shi, ya kar'bi kudin ya kama hanya ya fita da saurin gaske.....✍️
*GARKUWAR MATA*
*BINTA UMAR ABBALE*
[11/23, 10:21 AM] Aunty B: *GUDUN AURE!*
*NA*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*TALLAH!*
'Yan uwa
Barkanku da zuwa FAMAS SCENTS OF LEGENDS,
duniyar turarukan wuta masu kamshi na musamman mai samar da nutsuwa da kwanciyar hankali.
Mun tanadar muku da turarukan wuta masu dadin kamshi kamar su
Sandal flakes
Hawee
Gabgab
Halut
Dorot
Coconut chips
Dufr(farce)
Black khumra
Brown khumra
White khumra
Oil perfumes da
Body sprays
Dan turara gidajenku,tufafinku da jikinku.
Ga duk mai buqata zai iya tuntuban mu ta lamba kamar haka
Call/WhatsApp
07037489958
Location:Gonan Ganye,zaria
Kaduna state
Nationwide Delivery
*DATA Mai karfi da quality 💯*
TEEMAH DATA SERVICES MTN
1GB @550
2GB @950
3GB @1450
4GB @1550
5GB @1700
CHECK CODE *323*4#
VALIDITY 30DAYS
CHAT@08112392177
CALL @08037026306
8037026306 fatima musa ibrahim opay